Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Gayyaci Jakadun Kasashen Turai Don Gargadarsu
Published: 8th, October 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta gayyaci jakadun kasashen Turai zuwa ma’aikatar
Bayan katsalandan din da ke kunshe cikin sanarwar hadin gwiwa da ministocin harkokin wajen kasashen Larabawan yankin Tekun Farisa (GCC) da kungiyar tarayyar Turai suka yi, ma’aikatar harkokin wajen Iran ta gayyaci jakadu da shugabannin tawagogin kasashen kungiyar ta Tarayyar Turai tare da mika musu takardar nuna rashin amincewa mai kakkausar murya kan goyon bayan da’awar karya mara tushe.
Bayanin baya-bayan nan da kungiyar hadin kan kasashen Larabawan yankin Tekun Pasha da kungiyar tarayyar Turai suka fitar sun jaddada da’awar cewa tsibiran uku ba mallakin Iran ba ne, wanda ya hada da zarge-zarge marasa tushe dangane da tsibiran guda uku da kuma shirin makamashin nukiliyar Iran, lamarin da ya haifar da rashin gamsuwa ga ma’aikatar harkokin wajen Iran.
Majalisar hadin gwiwar kasashen Larabawan yankin Tekun Pasha (Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain, Kuwait, Oman, Qatar) da kungiyar Tarayyar Turai sun fitar da sanarwa a ranar Litinin a taronsu na 29, inda suka jaddada bukatar dakatar da shirin Iran na samar da makamai masu linzami da kuma hada kai da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Bayyana Aniyarta Ta Rashin Daina Samar Da Magunguna Ta Hanyar Fasahar Makamashin Nukiliya October 8, 2025 Jihadul-Islami Ta Jaddada Aniyarta Ta Ci Gaba Da Gwagwarmaya Har Sai Falasdinawa Sun Samu ‘Yancinsu October 8, 2025 Falasdinawa 12 Ne Suka Yi Shahada A Harin Wuce Gona Da Irin Sojojin Mamayar Isra’ila A Gaza A Yau Laraba October 8, 2025 Hamas ta bayyana muhimman bukatunta a tattaunawar tsagaita wuta a Gaza October 8, 2025 Iran ta yi gargadi game da katsalandan na EU akan tsibiran tekun Fasha October 8, 2025 Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare Gaza duk da tattauwanar da ake a Masar October 8, 2025 Gaza : Spain na son gurfanar da Isra’ila gaban ICC kan cin zarafin masu fafutukar kai agaji October 8, 2025 Faransa : Ana ci gaba da kira ga Macron ya yi murabus October 8, 2025 Dubban Mutanen Moroko Sun Yi Zanga-zangar Nuna Goyon Bayan Falasdinawa October 7, 2025 Kamfanin Jirgin Sama Na “Oman Air” Ya Maye Gurbin Isra’ila Da Falasdinu A Cikin Taswirarsa October 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: aikatar harkokin wajen da kungiyar kungiyar ta
এছাড়াও পড়ুন:
Tashar Talabijin ta Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew
Tashar Talabijin ta Press TV ta Iran ta kaddamar da sabon sashenta na harshen Hebrew don isa ga masu sauraro na Yaren Hebrew na duniya.
Yanzu ana iya samun wannan sashen ta hanyar asusun X (@PresstvHebrew) da kuma tashar Telegram (@PresstvHebrew), kuma Za a kaddamar da cikakken shafin Intanet na tashar nan ba da jimawa ba.
Sashen na Hebrew zai rika bayar da labarai, binciken kwakwaf, da sharhi kan abubuwan da suke faruwa a yankin da ma duniya baki daya.
A cewar Ahmad Norouzi, darektan sashen watsa labarai a bangaren harsunan ketare na Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRIB), ya bayyana cewa babban aikin tashar shi ne fallasa gaskiyar duk abinda jami’an Isra’ila ke neman boyewa, gami da takunkumin da aka sanya wa kafofin watsa labarai na yaren Hebrew a Isra’ila a lokacin rikice-rikicen baya-bayan nan.
Kaddamar da wannan tashar ya biyo bayan wani kuduri da Majalisar Koli ta Juyin Juya Halin a banagren Al’adu a Iran ta yi kwanan nan, wanda ya dora wa hukumar gidan talabijin da radiyo ta Iran (IRIB) alhakin kafa sashen sadarwa na talabijin na yaren Ibrananci ta duniya.
Tashar Talabijin ta Press TV ta bayyana cewa wannan shiri yana da nufin dakile farfagandar gwamnatin Sahayoniya da kafofin watsa labarai masu alaka da ita, don karfafa diflomasiyyar kafofin watsa labarai na Iran, da kuma gabatar da abubuwan da suka faru a yankin da kuma ra’ayin mutanen Iran.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru Mafaka Ta Wucin Gagi November 25, 2025 China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Velayati: Alakar Iran da Iraki tana da karfi November 25, 2025 Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin November 25, 2025 An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin November 25, 2025 Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar November 25, 2025 Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci