Jihadul-Islami Ta Jaddada Aniyarta Ta Ci Gaba Da Gwagwarmaya Har Sai Falasdinawa Sun Samu ‘Yancinsu
Published: 8th, October 2025 GMT
Dakarun bangaren sojin kungiyar Jihadul Islama ta Falasdinu Sarayal-Quds ta bayyana cewa: Fursunonin mamaya ba za su ga hasken rana ba har sai an sharuddan Falasdinawa
Dakarun bangaren sojin kungiyar Jihadul Islama ta Falasdinu, sun jaddada cewa: Fursunonin mamayar Isra’ila ba za su ga hasken rana ba, sai dai ta hanyar tattaunawa da musayar ra’ayi da yahudawan sahayoniyya da suka kuduri aniyar kawo karshen yakin Gaza.
A cikin wata sanarwa da dakarun Sarayal-Quds suka fitar, sun jaddada cewa su da dukkanin bangarorin gwagwarmaya ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen samar da hanyar kawo karshen yakin Gaza da kuma wahalhalun da Falasdinawan suke ciki.
Har ila yau, sun tabbatar da cewa: “Makaman ‘yan gwagwarmaya makamai ne da aka samar da su don ‘yantar da kasa da kuma yakar makiya, kuma ba za a karbe su ba har sai an cimma wadannan manufofi guda biyu.”
Dangane da farmakin ‘yan mamaya da ake kira “Gideon 2”, sanarwar ta jaddada cewa sakamakon wannan farmaki “zai fi zama abin takaici, wajen shan kashi, da kwasar kaskancin makiya ‘yan shayoniyya.”
Sanarwar ta ce Sarayal-Quds da sauran kungiyoyin gwagwarmaya, ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen lalubo hanyar kawo karshen wannan yaki da kuma wahalhalun da al’ummar Zirin Gaza suke ciki ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Falasdinawa 12 Ne Suka Yi Shahada A Harin Wuce Gona Da Irin Sojojin Mamayar Isra’ila A Gaza A Yau Laraba October 8, 2025 Hamas ta bayyana muhimman bukatunta a tattaunawar tsagaita wuta a Gaza October 8, 2025 Iran ta yi gargadi game da katsalandan na EU akan tsibiran tekun Fasha October 8, 2025 Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare Gaza duk da tattauwanar da ake a Masar October 8, 2025 Gaza : Spain na son gurfanar da Isra’ila gaban ICC kan cin zarafin masu fafutukar kai agaji October 8, 2025 Faransa : Ana ci gaba da kira ga Macron ya yi murabus October 8, 2025 Dubban Mutanen Moroko Sun Yi Zanga-zangar Nuna Goyon Bayan Falasdinawa October 7, 2025 Kamfanin Jirgin Sama Na “Oman Air” Ya Maye Gurbin Isra’ila Da Falasdinu A Cikin Taswirarsa October 7, 2025 MDD Ta Yi Maraba Da Hukunta Mai Laifi Na Farko A Yankin Darfur Da Kotun Duniya Ta Yi October 7, 2025 Golpayagni: Jagoran Juyi Ne Ke Rike Da Tutar Gwagwarmayar Fada Da Azzalumai A Duniya October 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Cibiyar Lafiya Ta Nasser Ta Ce: Yaran Gaza 5,500 Suna Bukatar Agajin Gaggawa A Kasashen Waje
Cibiyar kula da lafiya ta Nasser Medical Complex da ke Gaza ya bayyana cewa: Yara 5,500 ne ke bukatar agajin gaggawa a kasashen waje
Daraktan cibiyar kula da lafiya ta Al-Shifa da ke Gaza ya ce: Babu wani agajin jinya da ya shiga zirin Gaza duk da cewa an shafe sa’o’i 72 tsagaita bude wuta.
Ya kara da cewa: Mutane 170,000 marasa lafiya da kuma wadanda suka jikkata na bukatar tafiya cikin gaggawa zuwa wajen Gaza domin neman magani.
Al-Nasser Medical Complex ya kuma ce: Yara 5,500 na bukatar magani a wajen Gaza. Daraktan asibitin yara na Nasser Medical Complex, Dr. Ahmed Al-Farra, ya bayyana cewa, akwai yara 5,500 a zirin Gaza da ke bukatar agajin gaggawa a wajen yankin saboda tsananin karancin magunguna da kuma ci gaba da tabarbarewar yanayin kiwon lafiya.
A nata bangaren, Nour Al-Saqa, mai kula da harkokin yada labarai na kungiyar likitocin da ke yankin zirin Gaza, ta ce sama da mutane 170,000 da suka jikkata a zirin Gaza na bukatar kulawar gaggawa.
Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta fara aiki tun ranar Juma’a. A matakin farko, yarjejeniyar ta tanadi shigar da kusan tireloli 600 na kayan agajin gaggawa a kowace rana. Sai dai wasu kananan motoci ne kawai aka ba su izinin shiga, kuma har yanzu ba a kai agajin jinya a zirin Gaza ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Amurka Ya Yi Barazanar Aikewa Ukraine Makamai Masu Linzami Kirar Tomahawk October 13, 2025 Trump, da Al’Sisi za su jagoranci taron zaman lafiya kan Gaza October 12, 2025 ‘Yan Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar October 12, 2025 Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice October 12, 2025 Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi na hannu a yakin Ukraine October 12, 2025 Arachi: HKI Ba Abar Amincewa Ba Ce, Falasdinawa Su Yi Hattara October 12, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon October 12, 2025 An Gudanar Da Taron ‘Farkawar Musulmi’ A Nan Tahren Inda Aka Tattauna Batun Falasdinu October 12, 2025 Amurka Da Masar Ne Zasu Jagoranci Taron Rattaba Hannu Tsakanin HKI Da Falasdin A Sharm Sheikh October 12, 2025 China Ta Sha Alwashin Maida Martani Kan Harajin Trump A Kanta Na 100% October 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci