Babban mai shiga tsakanin na Hamas ya isa Masar domin tattaunawa da Isra’ila
Published: 6th, October 2025 GMT
Babban mai shiga tsakani na kungiyar gwagwarmayar falasdinawa ta Hamas Khalil Al-Hayya ya isa Masar, inda ya jagoranci tawagar da ake sa ran za ta fara tattaunawa wacce ba ta kai tsaye ba da Isra’ila, a cewar kungiyar.
Hamas ta ce za a fara tattaunawar ce kan “hanyoyin tsagaita bude wuta, da janye sojojin mamaya, da musayar fursunoni.
yau Litinin ne aka tsara tawagar Isra’ila za ta isa wurin, kamar yadda ofishin Benjamin Netanyahu ya bayyana, a wani bangare na tattaunawar.
Su ma wakilan Amurka, Masar da kuma Qatar zasu halarci tattaunawar a matsayinsu na masu shiga tsakani.
A cewar majiyoyin diflomasiyya, tattaunawar tsakanin Isra’ila da Falasdinawa za ta gudana ne a birnin Sharm el-Sheikh.
Ana sa ran tattaunawar za ta mai da hankali kan lokaci da cikakkun bayanai don ba da damar sakin ‘yan Isra’ila da aka yi garkuwa da su.
Tattaunawar za ta gudana ne tsakanin Isra’ila a bangare guda da kuma ‘yan Hamas a daya bangaren amma ba keke-da-keke ba, kuma za’a nisanta kafafen yada labarai daga tattaunawar.
Hamas dai ta dage kan bukatar dakatar da dukkan ayyukan soji da kuma na Isra’ila.
Bayanai sun ce sojojin Isra’ila sun ci gaba da kai hare-hare a birnin Gaza har zuwa jajibirin tattaunawar, inda suka kashe gomman mutane kamar yadda hukumar tsaron farar hula ta yankin ta sanar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran na goyan bayan duk wani shiri da zai samar da ‘yanci ga al’ummar Falasdinu October 6, 2025 Rahoto: A cikin shekaru biyu Isra’ila ta jefa tan 200,000 na bama-bamai a Gaza October 6, 2025 Gidauniyar Mandela ta yi tir da Isra’ila kan dakile ayyukan jin kai zuwa Gaza October 6, 2025 Afirka Ta Kudu Ta Aike Da Tawagar Bincken Musabbabin Mutuwar Jakadanta A Birnin Paris October 5, 2025 Iran: Kungiyar Kwallon Raga Ta Mata Ta Ci Kofin Asiya October 5, 2025 HKI Ta Kwace Kudin Gwamnatin Faladinu Dala Miliyan 7.5 Ta Rabawa Wasu Iyalan Yahudawa 41 October 5, 2025 Sojojin Sudan Sun Zargi Rundunar “RSF” Da Kai Hari Akan Cibiyoyin Fararen Hula October 5, 2025 Yan Sanda Sun Kama Masu Zanga- zangar Nuna Goyon Bayan Falasdinu A London October 5, 2025 Dakarun Sojin kasar Yamen Sun Harba Makamai Masu Linzami A HKI October 5, 2025 Masar Ta Zargi Habasha Da karya Dokokin Kasa Da Kasa Kan Rikicin Madatsar Ruwan Kogin Nilu October 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya
Daga Bello Wakili
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya karɓi labarin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi cikin alhini da jimami.
Fitaccen malamin da ke Bauchi ya rasu ne a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2026, yana da shekaru 101.
Shugaban Ƙasan ya yi jimamin rasuwar jagoran Darikar Tijjaniyya, yana bayyana shi a matsayin ginshiƙin ɗabi’a wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa da wa’azi.
Shugaba Tinubu ya ce rashinsa babban rashi ne ba ga iyalansa da dimbin mabiyansa kaɗai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya.
Shugaban Ƙasa ya tuna da albarka da goyon bayan da ya samu daga marigayi Sheikh Dahiru Bauchi a lokacin yakin zaɓen 2023.
“Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba, mai cike da natsuwa da hikima. A matsayinaa na mai wa’azi kuma masani kan tafsirin Alƙur’ani Mai Girma, yana da’awar zaman lafiya da tsoron Allah. Rasuwarsa ta bar babban gibi,” in ji Shugaban Ƙasa.
Shugaba Tinubu ya yi ta’aziyya ga mabiyan Shehun a ci da wajen ƙasa bisa wannan babban rashi.
Haka kuma ya ja hankalinsu da su girmama sunansa ta hanyar bin koyarwarsa ta zaman lafiya, ƙarfafa dangantakarsu da Allah, da kuma kasancewa masu taushin zuciya ga jama’a.