Aminiya:
2025-10-13@18:09:06 GMT

NAJERIYA A YAU: ‘Halin Kunci Ya Sa Muke Zama A Baca A Abuja’

Published: 6th, October 2025 GMT

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Halin matsin tattalin arziki ya tilasta da yawa daga cikin mutane zama a bacoci a garin Abuja da wasu biranen Najeriya.

 

Mutane a birane kamar Abuja da Legas Da Fatakwal na cikin halin matsi sakamakon rashin ingattaccen muhalli.

Ko wannen irin rayuwa irin wadannan mutanen ke yi?

NAJERIYA A YAU: Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Takarar Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan DAGA LARABA: Tasirin Bambance-bambance Tsakanin ‘Yan Najeriya Shekara 65 Da Samun ‘Yancin Kai

Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai a yau da ake bikin ranar muhalli ta duniya.

Domin sauke shirin, latsa nan

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: manyan gidaje a abuja

এছাড়াও পড়ুন:

Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe

A cewarta, shirin ya taimaka wajen noman shinkafa da ta kai kimanin tan 99,452, wacce kuma kudinta ya kai kimanin Naira biliyan 13.527 tare kuma da noman rogo da ya kai kimanin tan 87,237, wanda kudinsa ya kai Naira biliyan 3.925, musamman domin a kara samar da wadataccen abinci da kuma kara bunkasa fannin tattalin arzikin jihar.

 

Sai dai, ta bayyana cewa; har yanzu a jihar ba a samar da wani cikakken tsari a hukumance ba, a kan tsarin na shirin na CAF wanda hakan ke haifar wa da shirin koma baya a jihar.

 

Ta yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki a fannin bunkasa aikin noma, domin samun riba a jihar da su bayar da hadin kai wajen shiga cikin tsarin na CAF, musamman a bangaren noman shinkafa da rogo da sauran amfanin gona.

 

Kazalika, ta bukaci mahukunta a jihar da su samar da tsari a hukumance, musamman na dogon zango domin ci gaba da samar da wadataccen abinci a fadin jihar baki-daya.

 

Shi ma a nasa bangaren, jami’in shirin na jihar; Dakta Emmanuel Igbaukum ya bayyana cewa, masu ruwa da tsaki a jihar, sun nuna sha’awarsu ta shiga cikin shirin tare kuma da sanya shi a cikin tsarin jihar na samar da abinci mai gina jiki.

 

Ya kara da cewa, shirin zai kuma taimaka matuka wajen kara bunkasa fannin aikin noma na jihar baki-daya.

 

A nata jawabin, Babbar Sakatariya a ma’aikatar aikin noma da samar da wadataccen abinci, Pharm. Elijah ta bayar da tabbacin cewa; gwamnatin jihar za ta bayar da kason kudi a kan lokaci tare kuma da yin rangwame wajen sayen kayan aikin noma cikin rahusa.

 

Ta bayyana cewa, gudunmawar shirin na IFAD ya taimaka matuka wajen kara bunkasa fannin tattalin arziki da kuma fannin aikin noma na jihar.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Noma Da Kiwo Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara October 11, 2025 Noma Da Kiwo Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina October 3, 2025 Noma Da Kiwo Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo October 3, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro
  • Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
  • Rashin Amincewa Da Kasashen Yamma Yana Haifar Da Sabon Tunani Kan Huldar Kasa Da Kasa
  • Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja
  • An Yi Girgizar Kasa Mai Daraja 5 A Ma’aunin Richter  A Kasar Habasha
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Yi  Afuwa Ga Wasu Mutanen Da Kotuna Su Ka Hukunta
  • Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa
  • Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe
  • Iran Tana Goyon Bayan Duk Wani Shirin Zaman Lafiya Da Ya Hada Da Kawo Karshen Kisan Kiyashi A Gaza
  • CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa