Aminiya:
2025-10-13@17:47:15 GMT

Tinubu ya fi damuwa da siyasa sama da rayukan ’yan Najeriya

Published: 5th, October 2025 GMT

Jam’iyyar ADC ta zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da rashin mayar da hankali kan yadda matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a ƙasar nan.

Jam’iyyar ta ce shugaban yaf i damuwa 2ajen halartar tarukan siyasa da biki, maimakon kare rayukan ’yan Najeriya.

Ɓarayin daji sun kashe kwamandan maharba a Kaduna Mata da yara 95,000 ke mutuwa a sanadin shaƙar hayaƙin girki — Uwargidan Fubara

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta ce maganar da Shugaba Tinubu ya yi a Cocin COCIN a Jos, na batun haɗa kan ‘yan Najeriya, ba komai ba ne illa siyasa kawai.

Jam’iyyar ta ce tun da ya hau mulki, ba a ga wani mataki da ke nuna yana son haɗa kan al’umma ba.

ADC, ta ce Najeriya tana fuskantar mummunar barazana daga ’yan bindiga, don haka ta buƙaci gwamnati ta ɗauki mataki cikin gaggawa domin wanzar da zaman lafiya.

“ADC na cikin damuwa sosai saboda yadda Shugaba Tinubu ke nuna rashin damuwa da yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a ƙasar nan,” in ji sanarwar.

Jam’iyyar ta soki sugaban saboda ci gaba da halartar bukukuwa da tarukan siyasa, alhali ana kashe mutane da yin garkuwa da su a sassan ƙasar.

ADC ta kafa misali da yadda ’yan bindiga suka addabi ƙananan hukumomi tara a Jihar Kwara, inda mahara ke tilasta wa mazauna yankunan bayar da abinci, abin sha, da kuɗi a matsayin fansa.

Jam’iyyar ta ce wannan babban gazawa ce ta gwamnati, kuma har yanzu fadar shugaban ƙasa ba ta ɗauki mataki ba.

Har ila yau, ta sake kafa misali da Jihar Kogi, inda ’yan bindiga suka kashe fasinjoji tare da sace mata da yara.

Ta ƙara da cewa sama da makarantu 180 a Arewacin Najeriya aka rufe saboda rashin tsaro, lamarin da ya tilasta wa gomman yara zaman gida.

Jam’iyyar ta ce irin waɗannan abubuwa suna faruwa kusan a dukkanin sassan ƙasar nan; daga Filato zuwa Zamfara, Benuwe zuwa Neja, Kaduna zuwa Kwara, inda ake yawan kashe mutane da yin garkuwa da su.

Duk da haka, Gwamnatin Tarayya tana ci gaba da cewa tana samun “ci gaba.”

ADC ta ce wannan magana ba ta dace ba saboda ana ci gaba da zubar da jinin al’umma.

Sanarwar ta ƙara da cewa yayin da al’umma a karkara ke tserewa daga gidajensu, ake rufe makarantu, Shugaba Tinubu yana halartar bukukuwa da jana’izar ’yan siyasa.

A cewar ADC, wannan yana nuna cewa ya fi damuwa da harkokin siyasa sama da rayukan ’yan ƙasa.

Haka kuma, ta soki yadda Tinubu yake zama a fadar gwamnati yana aike saƙon ta’aziyya bayan kisan jama’a, maimakon ɗaukar mataki tun kafin irin waɗannan hare-hare su auku.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan Najeriya Rayuka Siyasa Tsaro Jam iyyar ta ce

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda Ake Gurasa Ta Semovita

Abubuwan da ake bukata:

Semovita (kamar kofi 3-4), Yis (Babban Cokali da rabi, idan kuna so ya tashi sosai), Suga (Babban cokali 2), Gishiri ( rabin cokali), Man gyada ko buta (Babban Cokali 2), Ruwa mai dumi (kusan 1–1½ kofi, gwargwadon yadda Semon ya sha)

 

Yadda za a hada:

Za a samu roba sai a zuba Semobita, yis, Sikari da Gishiri a kwano, a juya su da kyau, sannan a zuba ruwa, a zuba ruwan dumi a hankali a cikin hadin, a na gaurayawa har sai ya koma kulli.

Sai a zuba man gyada ko Bota a ciki, a ci gaba da murzawa har kullun ya yi laushi ba ya manne ba.

Sannan sai a rufe rubar da leda ko zani, a barshi a wuri mai dumi ko a kaishi rana na tsawon awa 1–2, har ya ya tashi.

A shafa man gyada a cikin abin gashi sai a dora a wuta idan ya yi zafi sai a rika zubawa daidai yadda kuke son girmanta, haka har ku gama.

Wannan gurasa da semovita ya kan fi dan nauyi kadan idan aka kwatanta da wanda aka yi da Fulawa na Alkama, amma yana dadi kuma yana daukar lokaci.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Girke-Girke Yadda Ake Lemon Tsamiya (Tamarin Juice) October 4, 2025 Girke-Girke Yadda Ake Hada Sushi September 27, 2025 Girke-Girke Collins Whitworth Zai Kafa Tarihin Shiga Kundin ‘Guinness World Record’ Tare Da Goyon Bayan Indomie September 25, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dan Majalisar Tarayyar Kaduna ya bar Jam’iyyar PDP
  • Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
  • Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22
  • Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?
  • Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)
  • Yadda Ake Gurasa Ta Semovita
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Yi  Afuwa Ga Wasu Mutanen Da Kotuna Su Ka Hukunta
  • An Gudanar Da Taron Hadin Kai Na Raya Albarkatun Kasa Tsakanin Sin Da Mozambique
  • Barin PDP Zuwa Wata Jam’iyyar Alamun Rashin Jarumta Ne – Gwamnan Bauchi
  • Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP