Hamas: Harin Isra’ila kan Gaza bayan amincewarmu da Shirin Trump ya fallasa karyar Netanyahu
Published: 5th, October 2025 GMT
Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta ce; ci gaba da kai munanan hare-hare da kisan kiyashi da Isra’ila ke yi kan al’ummar Palasdinu a Gaza ya fallasa ikirarin karya na Firayim Minista Benjamin Netanyahu kan rage ayyukan soji kan fararen hula.
A cewar sanarwar, sojojin mamaya na Isra’ila (IOF) na ci gaba da aikata munanan laifuka da kisan kiyashi a duk fadin zirin Gaza, inda a cikin kasa da sa’oi 24 Isra’ila ta kashe Falastinawa Fararen hula sama da 70, da suka hada da mata da kananan yara.
Kungiyar Hamas ta sake sabunta kiran da take yi ga kasashen duniya da na larabawa da na Musulmi da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, inda ta bukaci daukar matakin gaggawa na kariya da taimaka ma al’ummar Palastinu da kuma yin matsin lamba don kawo karshen kisan kiyashi da yunwa da ke ci gaba da lakume rayukan al’ummar Gaza.
Har ila yau, kungiyar ta yi kira ga ‘yantattun mutane a duniya da su ci gaba da kara kaimi ga fafutukarsu wajen nuna goyon goyon baya ga al’ummar Falastinu, da kuma kalubalantar zaluncin da suke fuskanta, da kuma daukar matakan ladabtarwa na shari’a a kan Isra’ila a mataki na kasa da kasa.
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa Isra’ila ta amince da mataki na farko na janyewa daga wasu yankuna na Gaza, lamarin da ya ce na a matsayin wani bangare na tattaunawar da ake yi na tsagaita wuta a Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin HKI Sun Bada Sanarwan Fara Aiwatar Da Shirin Trump Na Tsagaita Wuta A Gaza October 4, 2025 Janar Qa’ani: An Boye Ranar Fara Yakin Tufanul Aksa Har Haniyya Bai Da Labarisa October 4, 2025 Iran Na Shirin Cilla Tauraron Dan’adam Da Sandarerren Makamashi A Cibiyar Chabahar October 4, 2025 Iran: Gasar Fasahar Kere-kere Na Shekara Ta 2025 Zai Sami Halattar Wakilai Daga Kasashe 65 October 4, 2025 Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 146 October 4, 2025 Kissoshin Rayuwa : Sirar Imam Hassan(a) 145 October 4, 2025 Kissoshin Raytuwa: Sirar Imam Hassan(a) 144 October 4, 2025 Kissoshin Rayuwa : Sirar Imam Hassan (a) 145 October 4, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar ImamHassan(a) 143 October 4, 2025 Kissoshin Rayuwa : Sirar Imam Hassan (a) 142 October 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin Lebanon
Wani mai magana da yawun rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (UNIFIL) ya tabbatar da cewa Isra’ila ta gina katanga kan iyakar da ta ratsa zuwa cikin yankin kasar Lebanon kusa da garin Yaroun, abin da tawagar ta bayyana a matsayin keta kudurin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701.
“Isra’ila ta shafe shekaru da dama tana gina katanga a gefen Layin da aka Shata da ya raba yankunan Falastinu da Isra’ila ta mamaye da Lebanon, amma a cikin wannan yanayi katangar Isra’ila ta ratsa layin da ya raba bangarorin biyu,” in ji mai magana da yawun UNIFIL. “Don haka muna nuna rashin amincewa da wannan mataki, Wannan, a bayyane ya keta kuduri mai lamba 1701 da kuma hurumin kasar Lebanon.” Inji shi.
Dakarun Masu Sanya ido kan zaman lafiya a kudancin kasar Lebanon UNIFIL sun yi nazarin wurin kuma kuma tabbatar da cewa katangar ta ketare Layin da aka shata.
A cewar UNIFIL, sun gano cewa katangar tana cikin kasar Lebanon kuma ta kai kimanin mita murabba’i 4,000 a cikin kasar Lebanon”. Mai magana da yawun rundunar ya kara da cewa, tawagar ta sanar da sojojin na Isra’ila a hukumance game da keta dokar da suka yi, inda suka mayar da martanin cewa za su dubi lamarin.
UNIFIL ta jaddada cewa za ta ci gaba da bin diddigin lamarin, da kuma ci gaba da Magana tare da dukkan bangarorin da abin ya shafa don tabbatar da cewa an kiyaye doka da kuma yin aiki da kudiri mai lamba 1701.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Matsalolin Tsaro A Yankunan Bakin Ruwa A Kasar Siriya Ya Kai Zanga-Zangar Lumana November 26, 2025 Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu November 26, 2025 Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yawaba Pakistan Saboda Goyon Bayanta November 26, 2025 EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi November 25, 2025 Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Tashar Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru Mafaka Ta Wucin Gadi November 25, 2025 China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Velayati: Alakar Iran da Iraki tana da karfi November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci