Sharri Jonathan ke wa Buhari don lashe zaɓen 2027 —Garba Shehu
Published: 4th, October 2025 GMT
Tsohon mai magana da yawun marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya mayar da martani kan maganar tsohon Shugaba Goodluck Jonathan da ya ce ƙungiyar Boko Haram ta taɓa naɗa Buhari a matsayin wanda zai shiga tsakanin a tattaunawarsu da Gwamnatin tarayya.
A yayin taron ƙaddamar da littafin “Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum” wanda tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor (mai ritaya) ya rubuta, Jonathan ya bayyana cewa mayaƙan Boko Haram sun taɓa zaɓar Buhari a matsayin mai shiga tsakani domin tattaunawarsu da gwamnati.
Jonathan ya ce a lokacin mulkinsa, gwamnatinsa ta kafa kwamitoci daban-daban don tattaunawa da mayaƙan Boko Haram domin samun zaman lafiya.
Sai dai a martaninsa bayan labarin ya karaɗe kafofi sada zumunta, Garba Shehu ya ce ƙarya Jonathan yake shararawa saboda yana neman jan hankalin masu jefa ƙuri’a domin takararsa a zaɓen 2027.
Wata mata ta banka wa kanta wuta a Bauchi Boko Haram ta wuce yadda mutane ke tsammani — JonathanGarba Shehu ya ce: “Ya zama tilas mu mayar martani ga wannan mummunar magana ta tsohon Shugaba Jonathan da ya yi cewa Boko Haram ta taɓa nada marigayi Buhari a matsayin mai shiga tsakaninsu. Idan wannan wani salo ne na neman farin jini don takararka ta 2027, muna shaida maka, Mista Jonathan, cewa ka fara saka da baƙin zare.”
Ya kara da cewa: “ Shugabannin Boko Haram irin su Muhammad Yusuf — wanda ya kafa ƙungiyar — ko Abubakar Shekau, ba su taɓa naɗa Buhari ba ya zama wakilinsu. Sanin kowa ne cewa, Shekau na yawan tsine masa da yin barazana gare shi saboda aƙidunsu sun yi hannun riga.”
Garba Shehu ya tunatar da cewa a 2014, Buhari ya tsallake rijiya da baya daga harin bam da Boko Haram ta kai masa a Kaduna, inda wasu daga cikin ma’aikatansa suka ji rauni.
Ya ce ƙara da wannan harin ne ya nuna cewa Buhari da ƙungiyar Boko Haram suna gaba da juna.
Ya kuma jaddada cewa ko a lokacin da ake ta raɗe-raɗin ya karaɗe ƙasa cewa Boko Haram sun naɗa Buhari a matsayin mai shiga tsakani, shi Buhari da kansa ya musanta hakan ta bakin tsohon Sakataren Jam’iyyar CPC, Injiniya Buba Galadima.
A wancan lokacin, Buba Galadima ya ce: “Na yi magana da Buhari da misalin ƙarfe 10 na dare, amma ya shaida mini ko labarin ma bai ji ba. Ya ce babu wanda ya tuntuɓe shi, kuma bai san ko wa ya ƙirƙiri wannan magana ba.”
Shehu ya ce, a lokacin na, labarin ya samo asali ne daga wani ɓangare na Boko Haram da ake zargin abokan hamayyar Buhari ne suka tallafa musu don ɓata masa suna, inda wani mai suna Abu Mohammed Ibn Abdulaziz ya yi taron manema labarai a Maiduguri cewa suna son Buhari da wasu fitattun ’yan asalin Jihar Borno su shiga tsakani a tattaunawarsubda gwamnati.
Shehu ya ce daga bisani shugaban Boko Haram na ainihi, Abubakar Shekau, ya fito ya karyata Abdulaziz da cewa ba shi da izinin yin magana a madadinsu.
A ƙarshe, Garba Shehu ya ce: “Idan Dakta Jonathan yana son lashe zaben 2027, ya nemi wata magana ta gaskiya da zai faɗa wa ’yan Najeriya, ba ƙage ba.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram Buhari Garba Shehu Zaɓe Buhari a matsayin Boko Haram ta Jonathan ya Shehu ya ce Garba Shehu
এছাড়াও পড়ুন:
Yajin Aikin ASUU: Ba za mu biya duk wanda bai yi aiki ba — Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya, ta gargaɗi Ƙungiyar Malaman Kami’o’i ta Ƙasa (ASUU), cewa za ta aiwatar da dokar “babu aiki, babu albashi” idan malaman suka ci gaba da yajin aikin da ka iya zai kawo cikas ga harkokin karatu.
A wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta fitar da yammacin ranar Lahadi, Ministan Ilimi, Maruf Tunji Alausa, da Ƙaramar Ministan Ilimi, Suwaiba Sa’id Ahmed, sun ce gwamnati tana da niyyar magance ƙorafe-ƙorafen ASUU ta hanyar tattaunawa cikin lumana.
Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja“Gwamnati ta nuna gaskiya, haƙuri da kyakkyawar niyya a tattaunawarta da ƙungiyar,” in ji sanarwar.
Ministocin sun bayyana cewa yawancin buƙatun ASUU, kamar ƙarin kuɗin koyarwa da inganta yanayin aiki an riga an biya musu.
Sauran matsalolin kuma suna ƙarƙashin kulawar kwamitocin gudanarwar jami’o’i, waɗanda gwamnati ta sake kafawa don su kula da batutuwan da suka rage.
Sai dai duk da waɗannan matakan, ASUU ta zaɓi shiga yajin aiki.
Ministocin sun ce wannan mataki bai nuna haɗin kai ko adalci ga ɗalibai da jama’a ba.
Sun ƙara da cewa: “Gwamnati ta yi tsayin daka wajen tabbatar da zaman lafiya da daidaita karatu a jami’o’i.
“Amma sun yi gargaɗi cewa, dokar “babu aiki, babu albashi” tana nan daram a tsarin dokokin ƙwadago na Najeriya, kuma gwamnati za ta yi amfani da ita idan aka katse harkokin karatu.
Gwamnati ta roƙi ASUU da ta sake tunani tare da dawowa teburin sulhu, inda ta ce ƙofarta a buɗe ta ke don tattaunawa da yin sulhu.