Leadership News Hausa:
2025-11-27@20:04:32 GMT

Barcelona Ta Ɗare Kan Teburin Laliga Bayan Doke Real Sociedad

Published: 29th, September 2025 GMT

Barcelona Ta Ɗare Kan Teburin Laliga Bayan Doke Real Sociedad

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta koma kan teburin gasar Laliga bayan doke Real Sociedad da ci 2-1 a wasan da suka buga ranar Lahadi. Joules Kounde da Robert Lewandowski ne suka zura ƙwallayen biyu da suka tabbatar da nasarar.

Da wannan sakamako, Barcelona ta tattara maki 19 daga wasanni bakwai, tana da tazarar maki daya da Real Madrid wadda ta sha kashi a hannun Atletico Madrid da ci 5-2 a ranar Asabar.

Masu riƙe da kofin gasar, Barcelona, na fatan lashe Laliga karo na biyu a jere tun bayan shekarun 2017/2018 da 2018/2019.

Barcelona Ta Farfaɗo Zuwa Matsayi Na Biyu Bayan Lallasa Valencia A Johan Cruyff Atletico Madrid Ta Zazzaga Wa Real Madrid Ƙwallaye 5 A Metropolitano

Haka kuma, dawowar matashin ɗan wasa Lamine Yamal daga jinya ta taimaka matuka, musamman yadda ya bayar da taimako a ƙwallo ta biyu da Lewandowski ya ci. Yamal, wanda aka karrama a kwanan nan da kyautar gwarzon matashin ɗan wasa a Ballon d’Or, ya samu gagarumar karɓuwa daga magoya bayan Barcelona.

Kocin ƙungiyar, Hansi Flick, ya yaba da jajircewar ƴan wasansa, inda ya buƙace su da su ƙara dagewa a sauran wasannin. Barcelona za ta fuskanci Paris Saint-Germain (PSG) a gasar Zakarun Turai ranar Laraba, kafin ta ziyarci Sevilla a gasar Laliga ranar 5 ga watan Oktoba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Barcelona Barcelona ta

এছাড়াও পড়ুন:

Jihar Jigawa Za Ta Rufe Karbar Kudaden Aikin Hajjin 2026 Ranar 24 Ga Watan Disamba

Daga Usman Muhammad Zaria

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta bukaci maniyyatan aikin hajjin 2026 da su gaggauta biyan kudin kujerun su kafin ranar 24 ga watan gobe.

Darekta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taro da shugabannin sassa na hukumar da shugabannin shiyya da sauran ma’aikatan hukumar a Dutse babban birnin jihar.

Yana mai cewar, hukumar aikin hajji ta kasa wato NAHCON ta bayyana ranar 5 ga watan Disamba da ta kayyade a matsayin ranar rufe biyan kudin kujerun aikin Hajjin 2026 a fadin kasar nan.

Ya bayyana cewar ranar itace ranar karshe da hukumar aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta kayyade na biyan kudin kujerun domin maniyyatan da za su sauke farali.

Alhaji Ahmed Umar Labbo, yayi nuni da cewar, a duk fadin kasar nan jihar Jigawa ce kadai ta sami ranar 24 ga watan gobe sakamakon karamci da Gwamna Umar Namadi ya yiwa hukumar na bada lamunin sama da naira miliyan dubu 3 domin kebe kujerun jihar a aikin Hajjin 2026.

Kazalika, ya kara da cewar babu wata jihar da ta sami karamci da tagomashi wajen alkinta kujerun maniyyata fiye da jihar Jigawa.

A don haka, Labbo ya bukaci maniyyata da su gaggauta biyan kudin kujerun su ta hannun shugabannin shiyya ko kuma a shelkwatar hukumar dake Dutse nan da makwanni 4.

Ya kuma kara jaddada kudurinsa na rike kambun hukumar wajen tabbatar da kula da jin dadin alhazai da walwalar su tun daga gida Najeriya har zuwa kasa mai tsarki.

Ahmed Umar Labbo ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa karamcin da yake yiwa hukumar na bada lamunin kudi domin tare kujerun alhazan jihar da sauran ayyukan hukumar domin gudanar da aikin Hajji ingantacce.

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mbappe ya ci ƙwallaye 4 rigis a wasan Madrid da Olympiacos
  • Majalisar Wakilai ta nemi gwamnati ta gaggauta dauko Jonathan daga Guinea Bissau
  • Jihar Jigawa Za Ta Rufe Karbar Kudaden Aikin Hajjin 2026 Ranar 24 Ga Watan Disamba
  • Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniya
  • Real Madrid za ta yi karon-batta da Olympiacos a Gasar Zakarun Turai
  • Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS
  • Reuters: Kungiyar Likitoci Ba Da Iyaka Ba Ta Fice Daga Asibitin Darfur Bayan Bude Wa Ma’aikatanta Wuta
  • Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Bisa Bayyanar Daliban Kebbi, Ya Bukaci a Ceto Sauran
  • Chelsea za ta kece raini da Barcelona a Gasar Zakarun Turai
  • Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina