An ceto mutum 5 bayan gini ya rufta a Legas
Published: 25th, September 2025 GMT
Wani gini mai hawa biyu da ake ginawa ya rufta da safiyar ranar Alhamis a yankin Alimosho da ke Jihar Lagos, inda ya danne ma’aikata da dama.
Ginin, wanda yake a titin Modupeola kusa da madakatar mota ta Mangoro, ya rushe da misalin ƙarfe 4 na safe.
Muhimman abubuwa 7 da Najeriya ta fada yayin jawabinta a taron MDD FBI ta sanya la’adar N15m kan dan Najeriyar da take nema ruwa a jalloMutane da jami’an agajin gaggawa sun garzaya wajen domin ceto waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin baraguzan ginin.
Bayan wani lokaci, an ceto maza biyar da ransu, sannan an garzaya da su asibiti.
Ɗaya daga cikinsu, mai shekara 44 wanda ya samu munanan raunuka, an tura shi zuwa LASUTH.
Gwamnatin Jihar Legas ta fara bincike don gano musabbabin rushewar ginin, tare da yin alƙawarin ɗaukar matakan da suka dace domin hana aukuwar irin wannan a nan gaba.
Shugabar Hukumar Kashe Gobara na Jihar Legas, Margaret Adeseye, ta ce sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 5:39 na safe kuma suka isa wajen da misalin 6 6:24 na safe.
Ta bayyana cewa ainahin ginin tsarin ƙasa ne, amma ana ƙoƙarin mayar da shi bene mai hawa biyu.
“An ceto ma’aikatan da ke ginin maza guda biyar duk sun samu rauni, babu wanda ya rasu,” in ji ta.
Jami’an kashe gobara daga Ikeja da Agege sun isa wajen domin gudanar da aikin ceto.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 9, Sun Ƙwato Naira Miliyan 5 A Borno
Uba ya ce dakarun sun ci gaba da bincike da fatattakar ƴan ta’addan don hana su sake samun damar motsi a yankin Arewa maso Gabas.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA