2025-09-17@21:52:07 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6281

«gwamnatin jihar»:

    Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani guda 20, tare da riguna ruwa (life jackets) 2,000, domin rage haɗurran da ke aukuwa sakamakon ambaliya da nutsewar jirage a sassan jihar. An ƙaddamar da jiragen ne a ƙaramar hukumar Wamakko a ranar Laraba, inda gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirin gaggawa na tallafa wa al’ummar da ke fama da illar ambaliya da haɗurra a ruwa. Microsoft ya ƙwace shafukan wasu kamfanoni 340 a Najeriya An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB “Mun dauki wannan mataki bayan rahotannin da muke samu na yawaitar hatsarurruka da rasa rayuka da dukiya sakamakon jiragen katako da mutane ke amfani da su,” in ji Gwamna Ahmad...
      Wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Folasade Boriowo, ya fitar, ta ce a karon farko cikin shekaru da dama, daliban Nijeriya za su ci gaba da karatun tarihin Nijeriya tun daga Firamare 1 zuwa karamar Sakandare 3 yayin da daliban SSS 1 – 3 za su koyi sabon darasin da aka samar na ‘Civic and Heritage Studies’, wanda ya hada tarihin Nijeriya da Ilimin zamantakewar Jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya bukaci ma’aikatar kananan hukumomi da ta karfafa matakan yiwa kananan hukumomin jihar 27 jagoranci akan sha’anin mulki da harkokin kudi domin inganta ayyukan su. Shugaban Kwamatin, Alhaji Aminu Zakari ya yi wannan kiran a karshen ziyarar kwanaki 3 da kwamatin ya yi a ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar a Dutse. Alhaji Aminu Zakari wanda shi ne wakilin mazabar Gwiwa a majalisar dokokin jihar Jigawa, ya ce ziyarar kwamatin na da nufin tantance yadda ma’aikatar ta ke gudanar da ayyukan ta, ta fuskar harkokin mulki da na kudi da kuma dangantakar aiki tsakanin ta da kananan hukumomin jihar 27 kamar yadda tsarin mulki ya dorawa majalisa nauyi. A nasa jawabin, mataimakin shugaban...
    Gwamnatin Jigawa ta amince da sabon tsarin ka’idojin aiki domin aiwatar da shirin kula da lafiyar mata masu juna biyu, da jarirai da ƙananan yara kyauta a cibiyoyin lafiya na  jihar. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya bayyana haka bayan zaman majalisar zartarwa da aka gudanar a gidan gwamnati Dutse. Ya ce ka’idojin za su taimaka wajen inganta nagartar hidima, fayyace karewar ma’aikata, da kuma tabbatar da gaskiya, da bin doka da tsari a asibitoci. Kwamishinan ya ƙara da cewa matakin ya dace da manufar gwamnatin jihar na rage mace-macen mata da yara da kuma tabbatar da samun ingantacciyar kulawa ga kowa. Ya ce za a fara aiwatar da tsarin nan take, tare da horas da shugabannin asibitoci...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye dokar ta-baci a Jihar Rivers daga ƙarfe 12 na daren 17 ga watan Satumban 2025. Shugaban Ƙasar, a wata sanarwa da ya sanya wa hannu, ya ce dokar ta-bacin da ta dakatar da Gwamna, Mataimakiyarsa, da ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida ta cimma manufarta na dawo da zaman lafiya a jihar. Tinubu ya bayyana cewa ya yi amfani da Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ne a watan Maris na 2025 sakamakon durƙushewar mulki a Jihar Rivers. A cewarsa, rashin jituwa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Majalisar Dokokin Jihar, da kuma lalata muhimman kadarorin gwamnati sun jefa jihar cikin rikici. “Lamarin ya kai ga Babbar Kotun...
    Saboda wannan baiwa daga Allah, iyalai da ‘yan uwan mai akuyar suka sanar da shirye-shiryen gudanar da bikin murnar haihuwar ‘ya’yan akuyar a ranar Lahadi mai zuwa a Garun Dakasoye, karamar hukumar Garun Malam ta Jihar Kano, inda za a yi musu suna da kuma karatun Alkur’ani mai girma.   A nasa bangaren, mahaifin budurwar, Malam Aliyu dake Garin Dakasoye, ya tabbatar da cewa za su gudanar da bikin domin nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa wannan ni’ima da ya ba su.   Ya kara da cewa: “Mun gode wa Allah bisa wannan arziki, kuma muna sa ran gudanar da bikin tare da sanya musu suna domin nuna godiya ga Allah mai daukaka.” Daga kanmu, magana ta ƙare....
    Da safiyar yau 17 ga watan Satumba, aka bude dandalin tattauna batutuwan tsaro na Xiangshan karo na 12 da zai dauki kwanaki 3, daga raneku 17 zuwa 19 ga wannan nan, bisa jigon “daukaka tsarin duniya da inganta neman ci gaba cikin lumana”, a nan birnin Beijing. Tawagogi sama da 100 na gwamnatocin kasashe daban-daban da yankuna da wakilan kungiyoyin kasa da kasa ne ke halartar taron, inda yawan masu rajista ya wuce 1,800. Da safiyar yau, taron ya shirya tarukan tattaunawa guda 6 bisa jigon “ma’anar cimma nasarar yakin duniya na kin tafarkin murdiyya” da “madaidaitan hanyoyi da manyan kasashe za su bi na yin mu’ammala”, da “hanyoyin warware rikice-rikicen shiyya-shiyya”, da “cika shekaru 80 da kafuwar MDD: samun...
    Ministan sadarwa na Iran Sitar Hashimi ya bayyana cewa, an sami nasara a gwajin da aka yi na sabon tauraron dan’adam, mai suna “Nahid 2” wnada aikinsa shi ne samar da hanyoyin sanarwa na internet masu nagarta. Ministan sadarwar ya kuma ce dukkanin bangarorin tauraron dan’adam din sun yi aiki yadda ake so a yayin gwajin da hakan yake a matsayin wani ci gaba a fagen sadarwa a Iran. Har ila yau ministan Sadarwar Sitar Hashimi ya kuma ce; A tsakanin kauyuka 10,000 da ba su da hanyoyin sadarwa, yanzu an rage su da 2000, kuma ana ci gaba da aiki tukuru domin isa ga kauyunan da suke nesa,masu wahalar zuwa. Ministan sadarwar na Iran ya kuma kara da cewa;...
     Babban sakataren majalisar koli ta tsaron jamhuriyar musulunci ta Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa; Za a bunkasa aiki tare a tsakanin Iran da Saudiyya a fagagen tattalin arziki da kuma tsaro. Dr. Larijani ya bayyana hakan ne jim kadan bayan fitowar daga ganawar da ya yi da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mu8hammad Bin Salman. Bugu da kari Dr. Ali Larijani ya ce a yayin ganawarwa da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad Bin Salman, sun tattauna hanyoyin bunkasa alakar kasashensu ta fuskoki mabanbanta, da kara girman wannan alakar ta fuskar tattalin arzki da tsaro fiye da yadda take a yanzu.” Haka nan kuma ya ce, za a yi aiki domin kawar da dukkanin abubuwan da...
    Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Najeriya (NUT) reshen Jihar Gombe, ta ziyarci shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi na jihar, Barista Sani Ahmad Haruna, a ofishinsa da ke Gombe. Shugaban ƙungiyar, wanda shi ne shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, ya bayyana cewa gwamnati da shugabannin ƙananan hukumomi za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen inganta walwalar malamai. Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi Ya ce: “Ba za mu taɓa barin malamai su shiga cikin matsanancin hali ba. Za mu duba matsalolinsu domin tabbatar da walwalarsu da ci gaban ilimi a jihar.” Sani, ya kuma yaba da yadda NUT ke tattaunawa cikin lumana...
     Hukumar tarayyar turai ta gabatar da shawara ga kasashe mambobi da su jingine aiki da yarjejeniyar da aka kulla ta kasuwanci da HKI saboda yakin Gaza. A yau Laraba ne dai hukumar tarayyar turai din ta bijiro da wannan shawarar ga kasashen mambobi,sai dai kuma babu cikakken goyon baya daga mafi yawancin kasashen kungiyar da zai sa a yi aiki da shi. Ita kuwa jami’ar harkokin wajen ta tarayyar turai din Kaya Kalas ta gabatar da shawarar a kakaba takunkumi akan wasu ministoci biyu na HKI da kuma ‘yan share wuri zauna da suke amfani da akrfi akan Falasdinawa. Da akwai kungiyoyin kare hakkin bil’adama guda 84 da suke yin kira a yanke duk wata alaka ta kasuwanci da zuba...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yabawa Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jiha bisa ƙirƙirar Kyautar Malami Mafi Nagarta, yana mai bayyana hakan da ɗaya daga cikin manyan manufofin da za su ƙarfafa koyo da koyarwa a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Yaɗa Labaran sa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa bikin na farko na bada lambar yabo da aka gudanar a Dutse ya dace domin girmama malamai da suka yi fice ta hanyar jajircewa da sadaukar da kai. Ya ƙara da cewa wannan mataki zai ƙara kwarin gwiwa, ya samar da gasa mai kyau, tare da inganta darussa a makarantu. Namadi ya jaddada cewa ingancin ilimi bai tsaya kan gina...
    Gwamnatin Kano ta raba kayayyakin aiki na zamani na kimanin Naira Miliyan 250  ga cibiyoyin horas da sana’o’in hannu biyu da ke Kofar Mata da Gwale, domin yaƙi da shan miyagun kwayoyi da aikata laifuffuka a tsakanin matasa, ta hanyar samar da aikin yi. Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Dakta Yusuf Kofarmata, ya ce an amince da tallafin ne bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf don bunƙasa tsare-tsaren ƙarfafa matasa a jihar. Ya bayyana cewa an samar da injinan sarrafa fata guda 26 domin cibiyoyin wadanda al’ummar yankunan suka kafa, amma ba su da isassun kayayyakin aiki. Ya ce Gwamna Yusuf ne ya gina Cibiyar Horaswar ta Gwale  kasancewar nan ce mazabarsa, yayin da Dakta Yakubu Adam ya taka rawa...
    Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, Alhaji Salim Hashim Idris Gwangwazo, ya kaddamar da shirin kula da ido kyauta domin tallafawa jama’a da ke fama da ‘Glaucoma’ da ke lalata rijiyoyin ido, da ‘Cataract’ wato yanar ido da sauran cututtukan ido. An gudanar da shirin ne a Asibitin Kwalli tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar, ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, da Hukumar Lafiyar Farko ta Jiha, da ƙaramar hukumar da masu bada tallafi daga kasashen waje. Shirin ya haɗa da gwaje-gwajen lafiyar ido, da bayar da magunguna da kuma rarraba tabarau kyauta, musamman ga marasa ƙarfi a cikin al’umma. Shugaban ƙaramar hukumar, ta bakin Kwamishinan Lafiya Alhaji Mustapha Darma, ya bukaci jama’a da su ci gaba da tallafawa gwamnati wajen samar...
    Hukumomin a Ƙasar Saudiyya, sun saki wasu ’yan Najeriya uku da aka kama a Jeddah kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi. Waɗanda aka saki sun haɗa da Hajiya Maryam Hussain Abdullahi, Hajiya Abdullahi Bahijja Aminu, da Malam Abdulhamid Saddieq. Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano Sun shafe makonni huɗu a tsare kafin aka tabbatar da cewa ba su da laifi. A wajen taron manema labarai a Abuja, mai magana da yawun Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), Femi Babafemi, ya ce sakin ya biyo bayan tttaunawa da Shugaban NDLEA, Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), tare da Hukumar Hana...
    An garzaya da shi zuwa babban Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Kebbi, inda daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsa. An yi jana’izarsa a babban masallacin Sarkin Gwandu, sannan aka binne shi a makabartar Dukku da ke kan hanyar Makera zuwa Kangiwa. Jana’izar ta samu halartar jami’an kwas5tan, ‘yan uwa, abokai da sauran mu5sulmi daga sassa daban-daban na jihar. Har yanzu al’ummar garin Filgila da kewaye na cikin tashin hankali da fargaba, kasancewar hare-haren Lakurawa na jefa su cikin zulumi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga...
    Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba ta da niyyar gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a 2027. Galadima ya bayyana hakan ne ranar Talata a wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce gwamnatin da jam’iyyar APC ke jagoranta ta kankane cibiyoyin gwamnati don amfaninta. Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo “Wannan gwamnati ba ta shirya gudanar da zaɓen adalci ba. Daga yadda suke tafiyar da al’amura, za ka gane yadda suke tarwatsa jam’iyyun siyasa....
    Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIA) a ranar Laraba ta kaddamar da shirin bayar da kulawar lafiyar gaggawa kyauta ga yara a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), Kano. Shirin, a cewar Darakta a hukumar, Dr. Salahudeen Sikiru, wani bangare ne na fadada shirin lafiyar iyaye da NHIA ke aiwatarwa zuwa ga yara masu rauni da masu bukata ta musamman. Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo Ana zargin mace da kashe ’yar uwarta a kan N800 din barkono Ya ce an fara shirin fiye da shekara ɗaya da ta gabata da nufin rage mace-macen jarirai ’yan kasa da shekaru biyar. “Mun fara wannan shiri fiye da shekara...
    Kungyar Hamas ta bayyana cewa: Gmanatin mamayar Isra’ila ta ƙirƙiri ƙarya don kare kisan gillar da ta yi a Gaza Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta tabbatar da cewa: Zargin da kakakin rundunar sojin mamayar Isra’ila ya gabatar dangane da yin amfani da hasumiyai a birnin Gaza domin aikin soji ba komai ba ne illa karairayi na zahiri da suke nufin kare laifukan da ake aikatawa da kuma boye barnar da ake yi a birnin Gaza, kamar yadda a baya sojojin mamaya suka lalata garuruwan Rafah, Khan Younis, Jabaliya, Beit Hanoun, da Beit Lahiya. A cikin wata sanarwa da kungiyar Hamas ta fitar ta bayyana cewa, zargin mamaya na cewa kungiyar Hamas na amfani da fararen hula a matsayin garkuwar...
    Gwamnatin Jihar Jigawa  ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 75 na shekarar 2025, ga gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi 27. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, babban birnin jihar. Ya bayyana cewa, wannan ƙarin kasafin kuɗi ya samo asali ne daga ƙarin kuɗaɗen shiga domin biyan buƙatun kuɗaɗen da suka taso, da kuma ƙarfafa manyan fannoni da za su kawo ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar. Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, majalisar ta amince da Naira Biliyan 58 ga gwamnatin jiha da kuma Naira Biliyan 17 ga Kananan Hukumomi 27,...
    Ya ce ya sayi layin wayar ne daga hannun wani Audu, ɗan kungiyar Vikings wanda ya tsere yanzu. A wani lamari kuma, ‘yansanda sun kama wasu mutum huɗu da suka shiga gonar wani mutum a Lapai Gwari, inda suka saci kifi da darajar kuɗinsu ta kai Naira 750,000. Babban wanda ake zargi, Hussaini Garba, ya amsa laifi tare da bayyana Ahmed Yusuf, Ibrahim Musa da Abdulazeez Bawa a matsayin mutanen da suke sayen kifin idan ya sato. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin  kasar Iran ta bayyana wasu abubuwan da bata amince da su ba, a jawabin bayan taro na musamman na kungiyar kasashen musulmi ta (OIC) wanda aka gudanar a birnin Doha na kasar Qatar a ranar litinin 15 gawatan Satumba da mukeciki. Sannan ta kara tabbatar da goyon bayanta ga gwagwarmayan da Falasdinawa suke yi da HKI don kwatar kasarsu da ta mamaye. A cikin wani bayanin da ma’aikatar harokokin wajen kasar Iran ta fitar a yau Laraba, Jumhuriyar Musulunci ta Iran, tana kara jaddada goyon bayanta ga al-ummar Falasdina, kuma tana kara jaddada tir da allawai da kissan kiyashin da HKI take yi a Gaza da kuma sauran yankunan falasdinawa da ta mamaye. Kuma tana godewa mutanen kasar Iran...
    Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da gyare-gyaren kundin tsarin mulkin kasar da zai tsawaita wa’adin shugabancin kasar daga shekaru biyar zuwa bakwai da kuma baiwa shugaban kasar damar ci gaba da mulki na tsawon wa’adi maras iyaka. Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar a ranar Litinin da kuri’u 171, yayin da aka kada kuri’a daya tilo da taki amincewa da hakan. A ranar 13 ga watan Oktoba ne aka shirya kada kuri’ar karshe a majalisar dattawa, a cewar sanarwar da shugaban majalisar Ali Koloto Chaimi ya fitar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito. Sannan  kuma shugaban kasar zai sanya hannu kan kundin tsarin mulkin sannan ya zama doka. Shugaban kasar Chadi,...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’ilBagaei ya yi tir da samar da duk wata hulda da HKI sannan tana ganin yin haka yana dai-dai da taimaka mata ko halatta mata ayyukan ta’addancin da take aikatawa a Gaza. Kamfanin dillancin labaran Tasnem na kasar Iran ya nakalto Bagaei yana fadar haka a yau Laraba, a taron mako-mako da ya saba a ma’aikatsa a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa, Iran tana kira ga dukkan kasashen duniya musamman kasashen yankingabas ta tsakiya da su kauracewa Haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) ko ta ina. Ya ce kasashen musulmi da dama, har ma da wasu wadandaba musulmi ba sun dade da katse dangantakarsu da haramtacciyar kasar, babu dangantakar diblomasiyya babu na kasuwanci da...
    Sun jaddada cewa dole ne manyan kafafen sada zumunta su kare ‘yancin yin magana. Sun kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya, ‘yan jarida, da masu fafutukar kare haƙƙin bil’adama su tashi tsaye don hana abin da suka kira yunƙurin mayar da Nijeriya “mulkin kama-karya a intanet.” Lamarin ya biyo bayan wa’adin sati guda da DSS ta bai wa Sowore da ya goge wasu wasu rubuce-rubuce game da Shugaba Bola Tinubu, wanda ya ƙi amincewa. Hakan ya sa hukumar ta shigar da shi ƙara a kotu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
    Kwamitin bincike mai zaman kansa na Majalisar Dinkin Duniya, ya fitar da wani rahoto mai zargin Isra’ila da laifin aikata kisan kiyashi a zirin Gaza. A cikin sabon rahoto da ta gabatar a ranar Talata, MDD ta zargi shugaban kasar Isra’ila Isaac Herzog, da firaministan kasar Benjamin Netanyahu, da kuma tsohon ministan tsaro Yoav Gallant da “kimsa kisan kiyashi.”. Rahoton ya tattara batutuwan da suka shafi farar hula kai tsaye, ciki har da yara, ya kuma bayyana cewa kisan kiyashin da ake yi ya fi yawa fiye da yadda aka yi tashe-tashen hankula a baya. Masu binciken sun kuma tabbatar da cewa da gangan Isra’ila ta haifar da yanayin da ke barazana ga rayuwar Falasdinawa ta hanyar toshe hanyoyin samun...
    Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ondo ta tabbatar da kama wata mata mai suna Iluyemi Bosede bisa zargin kashe yayarta, Tewogboye Omowumi, a Akure, babban birnin jihar. A cewar sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Olayinka Ayanlade, ya fitar a ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne a ranar shida ga Satumba, 2025, bayan wata sa’insa da ta kaure tsakanin matar da marigayiyar kan Naira 800. Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya Jami’in ya bayyana cewa Bosede ta ture ’yar uwarta har ta faɗi ƙasa, lamarin da ya haifar da mutuwarta. Ya ce, “Binciken farko ya...
    Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar SDP a zaben 2023, Adewole Adebayo, ya ce Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ba shi da burin da ya wuce na tara haraji tun yana Gwamna a Legas. Adebayo ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels. Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya A cewarsa, “Kowa ya san cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu sananne ne wajen karbar haraji. Amma wannan tsarin karbar haraji ya fi tsarin da ya tarar da shi wanda ba shi da tsari. “Ya yi hakan a Legas, sannan ya zo Abuja domin ya dora daga...
    Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Jiang Bin, ya ce a baya bayan nan babban jirgin ruwan dakon jiragen sama na kasar Sin mai suna Fujian, ya doshi yankin tekun kudancin kasar, inda ya ratsa ta zirin Taiwan, a kan hanyarsa ta gudanar da gwaje-gwaje da samar da horo. Jami’in wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, ya ce hakan bangare ne na ayyukan da aka saba gudanarwa lokaci-lokaci a wani bangare na kirar jirgin. Jiang Bin, ya yi tsokacin ne yayin da yake amsa wata tambaya mai nasaba da hakan da aka yi masa, yana mai cewa, bulaguron jirgin ya dace da dokokin kasa da kasa da ayyuka masu nasaba, kuma ba shi da wata nasaba da tunkarar wani sashe....
      Ya ce, masu garkuwa da mutanen sun afka gidansa ne a daren Lahadi a lokacin da mazauna gidan ke shirin kwanciya barci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Yobe (ALGON) ta karrama Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, da lambar yabo ta karramawa bisa himmar ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ke gudanarwa a faɗin jihar. Karramawar, wacce aka bayyana a matsayin irinta ta farko a tarihin Jihar Yobe, shugabannin ƙananan hukumomi 17 na jihar suka ba da ita ga gwamna. Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno Da yake jawabi, shugaban ƙungiyar ALGON a Jihar Yobe, kuma shugaban ƙaramar hukumar Damaturu, Alhaji Bukar Adamu, ya yaba da yadda Gwamna Buni yake gudanar da harkokin mulki na bai ɗaya. Ya ce nasarorin da aka samu sun haɗa da fannoni na...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi. Ministan Noma  Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta  Jihar Jigawa.   Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya. Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sojojin Najeriya sun kashe aƙalla mayakan ƙungiyar ISWAP 8, ciki har da manyan kwamandojinta biyu a Jihar Borno. Wata majiyar leƙen asiri daga rundunar haɗin kai ta OPHK ta bayyana cewa an kashe ’yan ta’addan ne a wata arangama da suka yi da sojojin a kan hanyar Maiduguri zuwa Baga a safiyar ranar Litinin. DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala A cewar majiyoyin, an yi arangamar ce a kusa da Garin Giwa da ke gab da ƙauyen Kauwa, lokacin da ’yan ta’addan suka yi wa dakarun da ke sintiri kwanton ɓauna. “A yayin wannan artabu, an kashe ’yan ta’adda takwas, ciki...
    Majiyar sojojin kasar Yamen sun sanar cewa a ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da HKi ke yi, Jiragen yakin HKI sun kai hari kan tashar jirgin ruwan hudaidai dake kasar kuma sun samu nasarar kakkabo makaman. Kakakin sojin kasar yamen yahya Saree ya fadi a cikin shafinsa na x cewa makaman kariya da muke dasu sun kalubalanci hare haren da Isra’ial ta kai a tashar jirgin ruwa na Hudaida, Isra’ila ta harba makamai masu linzami 12 a tashoshin jiragen ruwanta guda 3. Gidan rediyo isra’ila ya sanar cewa babban dalilin kai harin shi ne don a hana gudanar da ayyuka na tsawon makwanni, bayan gyara wuraren da suka lalace a hare-haren baya bayan nan da aka kai,...
    Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Jihar Kano ta haramta shirya duk wata muƙabala tsakanin mawaƙan yabon Annabi (S.A.W), tare da gayyatar mawaƙa Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi su bayyana a gabanta. Hukumar ta kuma gayyaci mawaƙan ne tare da sauran waɗanda suka jagoranci muƙabalar da fitattun mawaƙan biyu suka yi ranar Litinin, da su bayyana a gabanta cikin sa’o’i 24. Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu Hakan na zuwa ne ƙasa da kwana ɗaya bayan ɓullar wata muhawara da aka yi tsakanin Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi kuma ta karade shafukan sada zumunta, wacce hukumar ta bayyana a matsayin karya dokokin aikinta. Shugaban...
    Hukumar Tsaron Farin Kaya a Nijeriya DSS, ta gurfanar da fitaccen ɗan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore a kotu. A ƙunshin ƙarar da DSS ta gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta haɗa da shafukan sada zumunta na X da kuma Facebook, inda take zarginsu da ba da ƙofar aibata Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Bida Poly ta sa sojoji kula da jarrabawar ɗalibai Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku Darekan shigar da ƙara na Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, M.B Abubakar da wasu lauyoyi huɗu —M.E. Ernest da U.B. Bulla da C.S. Eze da kuma E.G. Orubor, ne suka shigar da ƙarar a madadin Gwamnatin Tarayya da kuma hukumar ta DSS. DSS wadda ta kafa hujja da sashe na...
    “Bayan karbar mukaminsa na sabon kwamandan hukumar NSCDC na jihar Kano, kwamared Bala Bodinga ya umurci jami’ansa da su sadaukar da kansu ga muhimmin aiki na tabbatar da amincin muhimman kadarori da ababen more rayuwa na kasa.   “Kwamandan jihar ya ba da umarnin cewa, ba dare ba rana, cikin sa’o’i 24, dole jami’an hukumar su rika yin sintiri da sanya ido domin dakile ayyukan barayi da masu aikata laifuka a lunguna da sako na jihar,” inji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yadda kasashen yammacin duniya suka ki sauke nauyin dake wuyansu, ya danne wa kasashe masu tasowa hakkinsu. Misali, a lokacin da ake samun bazuwar annobar COVID-19, dimbin kasashen yamma sun yi ajiyar alluran rigakafi a gida, inda suka hana fitar da su zuwa ketare, da musayar fasahohi masu nasaba da su. Sai dai a lokacin, hukumomi masu kula da harkokin kasa da kasa, kamar su Hukumar Lafiya ta Duniya, da Majalisar Dinkin Duniya dukkansu sun kasa tilasta musu sauya manufofinsu. Wannan tsarin kasa da kasa, idan mun bar shi haka ba tare da wani sauyi ba, to, wata rana za mu ga an koma tsarin zalunci na zamanin mulkin mallaka, wanda zai yi barazana ga hakkin rayuwa, da raya kai...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya tabbatar da haƙƙin kasashe na haɓakawa da amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Isma’il Baqa’i, ya yi ishara da shawarar da Iran ta gabatar na daftarin kudurin da ya haramta kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukiliyar kasashe masu zaman lafiya, yana mai cewa: Dukkanin kasashe na da hakkin yin amfani da makamashin nukiliya don zaman lafiya da kuma hakkin samun ingantacciyar kariya daga duk wani hari ko barazanar kai hari. A cikin sakon da ya aike ta dandalin X a yau Talata, Ismail Baqa’i ya yi ishara da shirin Iran a babban taron hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA) da ake...
    Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta ce: Laifin da Isra’ila ta yi na kashe ‘yan jaridun Yemen babban ta’addanci ne Kungiyar kare hakkin bil’ adama ta Human Rights Watch ta tabbatar da cewa: Harin da yahudawan sahayoniyya suka kai a ranar 26 ga watan Satumba kan ‘yan jaridun kasar Yemen, wanda ya yi sanadiyar mutuwar ‘yan jarida sama da 30, laifi ne da ba za a iya kubutar da girman laifin kan wanda ya aikata ba. A cikin rahoton baya-bayan nan, kungiyar ta fitar ta bayyana cewa, ta tattara bayanan harin da makiya yahudawan sahayoniyya suka kaddamar a ranar 10 ga watan Satumba kan hedkwatar kafafen yada labarai a kasar Yemen, kuma ta yi la’akari da wannan...
    Mai kuɗin Afrika kuma Shugaban Matatar Mai ta Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya zargi wasu manyan masu harkar mai da shirya maƙarƙashiya domin kashe matatarsa. Ɗangote ya yi zargin cewa miyagun ’yan kasuwan suna ƙoƙarin kashe matatar mansa mai darajar dala biliyan 20, kamar yadda aka kashe masana’antar tufafi ta ƙasar. Ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Legas yayin bikin cika shekara ɗaya da fara samar da fetur a matatar, inda ya ce tafiyar ta kasance cike da ƙalubale tun daga farko. “A gaskiya tafiyar shekara ɗaya da ta wuce ta yi mana matuƙar wuya. Mun zo mu sauya tsarin kasuwancin man ƙasa. Amma wasu na ganin mun raba su da hanayar cin abinci bakinsu,” in ji shi....
    Sojoji biyu sun ji rauni bayan wani harin kwanton baya da ’yan bindiga suka kai kan ayarin motocin Kwamandan kwamandan Rundunar Sojoji ta 382 Ƙaramar Hukumar Faskari ta jihar Katsina. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Ruwan Godiya, kan hanyar Sheme–Kankara, lokacin da tawagar Operation Fansan Yamma (OPFY) ke wucewa. Ganau sun ce sojojin na kan hanyar ziyartar sansanonin sojoji a yankunan Faskari da Mabai da Ɗan Ali lokacin da aka kai musu hari. Sai dai sun yi nasarar tunkarar ’yan bindigar har suka kuvuta, kodayake sojoji biyu sun samu raunuka na harbi kuma aka kai su asibitin sojoji domin jinya. An kai wa sojojin harin ne a rana ɗaya da shugabannin al’ummar Faskari suka zauna da wakilan ’yan bindiga...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matakin hana malaman da ba su da rajista hawa mumbari a Neja yana ci gaba da yamutsa hazo a ciki da wajen jihar. Yayin da wasu suke ganin wannan mataki bai dace ba, wasu kuwa gani suke faduwa ta zo daidai da zama, wato matakin ya zo a daidai lokacin da ake bukata. NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kan tanadin Dokar Kasa game da wannan batu. Domin sauke shirin, latsa nan
    Babban daraktan kamfanin dillancin labaran kasar Qatar ya bayyana cewa taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da ke tafe yana nuni da wani muhimmin sauyi na hadin kan kasashen larabawa da musulmi dangane da laifukan da ake aikatawa kan al’ummar Palastinu. A cewar Pars Today, dukkanin idanuwa a ranakun Lahadi da Litinin (15-16 ga Satumba, 2025) za su kasance a Doha, babban birnin kasar Qatar, wanda zai karbi bakuncin taron gaggawa na shugabannin kasashen Larabawa da na Islama, don ba da amsa ga baki daya kan harin da Isra’ila ta kai kan Qatar. Ana gudanar da wannan taron gaggawa ne a cikin yanayi na musamman na yanki da na duniya kuma ya biyo bayan harin da...
    Ministan tsaro na kasar Venezuela Vladimir Padrino López ya gargadi gwamnatin Amurka dangane da duk wani kokari na kaiwa kasar Venuzuela hare hare saboda kifar da gwamnatin shugaba Nicolas Madoro. Tare da fakewa da fasakorin kwayoyi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Vladimir yana cewa take-taken gwamnatin Amurka na sojojin da ta kawo a teken carebian ya yi kama da takalar yaki ne da kasar Venezuela , kuma idan haka ne, to sojojin sa a shirye suke su fuskance su, su kumakare kasarsu. Kamfanin dillancin labaran IP nakasar Iran ya bayyana cewa, Amurka ta fara kai ruwa rana da gwamnatin shugaba Madoro ne tun lokacinda shugaban Amurka Donal Trump ya bayyana shugaban kasar ta Venezuela a...
    Shugaban kasar Iran yana mai jaddada cewa wajibi ne kasashen musulmi su karfafa hadin kai da hadin kai don mayar da martani ga ayyukan gwamnatin sahyoniyawan, inda ya ce: Wajibi ne kasashen musulmi su tsaya tsayin daka tare da daukar matakai na zahiri a fagen tattalin arziki, al’adu da zamantakewa, yanke alakarsu da gwamnatin sahyoniyawan. Masoud Pezeshkian shugaban kasar Iran a jiya litinin kafin ya tashi zuwa kasar Qatar domin halartar taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da kungiyar hadin kan kasashen larabawa dangane da harin da gwamnatin sahyoniyawan ta kai wa birnin Doha, ya bayyana cewa: “Gwamnatin yahudawan sahyoniya ba ta amince da wani iyaka ga kanta ba, kuma tare da goyon bayan Amurka, ta...
    Ya ce kuma kayan da ake fitarwa zuwa waje waɗanda ba man fetur yanzu su kusa yin kai da kai da fetur. Ya ƙara da cewa ajiyar kuɗaɗen ƙasar a waje ya haura kusan dala biliyan 42, daga biliyan 32 lokacin da Tinubu ya hau mulki. Har ila yau, ya ce an biya bashin da ya haura biliyan bakwai, ciki har da miliyan 800 da ake bin jiragen saman Nijeriya. Fadar Shugaban Ƙasa ta ce yanzu jihohi na iya biyan albashi da fansho a kan lokaci, sannan suna da rarar kuɗi don ayyukan raya ƙasa, abin da ba a saba gani ba a baya. “Bayan shekara biyu da watanni biyar kacal a ofis, Shugaba Tinubu ya cimma abubuwa da dama....
    “Sauran motocin da ke cikin ayarin, ciki har da wacce ke ɗauke da shugaban majalisar, da ƙyar suka iya tsayawa wanda tsakaninsu mitoci kaɗan ne daga wurin da haɗarin ya afku,” in ji wani ganau.   Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, an garzaya da jami’an ‘yansandan da suka samu raunuka zuwa babban asibitin Gumel a sume amma daga baya sun farfaɗo.   Da yake magana kan lamarin, mataimakin shugaban majalisar, Aqeel Akilu, ya yi godiya ga Ubangiji cewa, ba a rasa rayuka ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
    A yau Litinin ne tawagogin kasashen Sin da Amurka, suka sake tattaunawa a rana ta biyu, game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya a birnin Madrid na kasar Sifaniya. A jiya Lahadi, sassan biyu sun gudanar da zaman farko ne a fadar Santa Cruz, inda ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Sifaniya yake. A cewar kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, sassan biyu za su tattauna batutuwan da suka hada da matakin Amurka na kakaba jerin haraji daga bangare guda, da keta matakan kayyade fitar da hajoji, da batun dandalin TikTok. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
    Bikin hada-hadar ba da hidima na Sin wato CIFTIS na bana da ya kare a jiya a nan Beijing ya jawo hankalin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 85 da suka gudanar da baje koli da tarurruka, kusan kamfanoni 500, ciki hadda wasu daga cikin manyan kamfanoni 500 dake sahun gaba a duniya da manyan kamfanoni masu jagorantar bangarorinsu, sun halarci bikin, kuma an cimma nasara a fannoni sama da 900. A yayin da duniya ke fuskantar rashin tabbas, bikin CIFTIS ya karfafa mu’amala da kuma samun riba da juna. Alkaluma na nuna cewa, a shekara ta 2024, jimillar cinikin ba da hidima na Sin ya fara wuce dala tiriliyan 1 a karon farko, wanda ya zama sabon tarihi, kuma...
    Hukumar ƙididdigar a Najeriya NBS ta bayyana cewa an samu raguwar hauhawar farashin kaya a watan Agusta idan aka kwatanta da watan Yulin da ya gabace shi. Cikin sabbin alƙaluman da NBS ta fitar a ranar Litinin sun nuna cewa an samu raguwar kashi 1.76 a watan Agustan saɓanin watan Yulin, wanda ya nuna karo na hudu ke nan a jere hauhawar farashin yana sauka. NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas Kundin Bajinta na Guinness ya taya Hilda Baci murna Rahoton na hukumar NBS na zuwa ne kwanaki bayan da Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin karya farashin kayan abinci ƙasar. A watanin baya-bayan an riƙa samun raguwar hauhawar farashin kayyaki a...
    Mataimakinsa kan harkokin majalisa Honarabul Attahiru Danmadi ne ya wakilci dan majalisar ya kuma tabbatarwa wadanda lamarin ya shafa kokarinsa kan daukar matakan da suka kamata domin tabbatar da tsaron rayukan su da dawowa da zaman lafiya a yankunan.   Garuruwan da ‘yan bindigar suka tarwatsa a gundumar Kuchi sun hada da Fakku, sha’alwashi, tulluwa da Rafin- gora a inda mutane bakwai suka rasa rai. A gundumar Jabo kuwa kauyukan da lamarin ya shafa su ne; Gesolodi, Hilya, Guraye, Guma, Chakai, Modo, Badariya, Tafki, Balera, Gudumawa da Rafin shinka.   “Mun girgiza kwarai da wannan halin da kuke ciki. A matsayina na wakilin ku, zan ci-gaba da kokarin da ya kamata a majalisa domin ganin jami’an tsaro sun kawo karshen...
        Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Litinin ne dai kungiyoyin kasashen musulmi da na larabawa su ka yi taron gaggawa a birin Doha na kasar Qatar da aka tattauna harin wuce gona da iri da HKI ta kai wa kasar. Bayanin bayan taron ya kunshi bangarori mabanbanta da su ka hada da daukar matakai kwarara domin taka wa HKI birki akan ta’addancin da take yi, da kuma hanyoyin kare kai anan gaba.  Kungiyar kasashen larabawan yankin tekun fasha ta sake jaddada muhimmancin aiki da dokar kafa rundunar hadin gwiwa ta kare kai daga duk wani wuce gona da iri daga waje. Bugu da kari, mahalarta taron sun amince da dukar dukkanin matakan dokoki a fagen duniya domin hukunta jami’an HKI da su ka tafka...
    Rahoton rashin fahimtar da aka fara yadawar, ya biyo bayan taron kwamitin zaman lafiya da kwantar da tarzoma na jihar, wanda Darakta Janar ya jagoranta a ranar 4 ga watan Satumba.   Rashin fahimtar sahihin sakamakon taron ya sa wasu suka rahoto cewa, kwamitin ya dakatar da Malamai daga yin wa’azi.   Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar ba ta da hurumin haramtawa Malaman Addinin Musulunci yin wa’azi sai dai in ya bayyana a fili an taka ƙa’idojin hukumar da ta shimfiɗa”.   A cewar Hukumar, an kira taron ne domin gabatar da fom din rijistar yin wa’azi ko Da’awah da kuma bin tsarin tantancewa.   Ta bayyana shirin a matsayin wani yunkuri na wayar da kan jama’a don “hana...
    Fitacciyar mai girkin nan, Hilda Effiong Bassey, wadda aka fi sani da Hilda Baci, ta sake kafa tarihi a duniya ta hanyar girka tukunyar dafa-dukar shinkafa mafi girma bayan shafe awa takwas tana girkin. Hakan dai na ƙunshe ne cikin wani saƙon taya murna da Kundin Bajinta na Guinness ya wallafa a shafukan sada zumunta. Peter Obi ya kai wa Obasanjo ziyara ’Yan sanda sun sasanta rikicin asibitin AKTH da KEDCO Hilda Baci dai ta dafa shinkafa dafa-duka mafi yawa a tarihi tare da sauran kayan haɗi da sunadaran ɗanɗano wadda nauyinta ya kai kilo 8,780 a yankin Victoria Island da ke Legas. A shekarar 2023 Hilda mai shekaru 28 ta shiga Kundin Bajinta na Guiness World Record bayan shafe...
    Hukumar kula da al’adun gargajiya ta kasar Sin ta sanar a yau cewa, an gano wani dutsen da aka yi sassaka kan sa a kan tsaunin Qinghai-Tibet, wanda ya kasance irinsa daya tilo na daular Qin da har yanzu ke mazauninsa na asalin, kuma a wuri mafi tsawo. Dutsen wanda ke arewacin bakin tabkin Gyaring na gundumar Maduo, dake arewa maso yammacin lardin Qinghai, na wuri mai tsawon mita 4,300. Gano dutsen na tattare da wata muhimmiyar daraja ga tarihi da fasaha da kimiyya. Sarki Qinshihuang na daular Qin ne ya fara hada kan kasar Sin. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
    Yarjejeniyar, a cewar daukacin mahalarta taron, ta nuna wani gagarumin mataki na kawo karshen tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane da satar shanu a Arewa maso Yamma, da kuma yankin Arewa.   Yarjejeniyar wacce Mai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, da shugaban karamar hukumar, Babangida Abdullahi Kurfi suka shirya, ta gudana ne a dajin Wurma, inda ake fama da rashin tsaro.   Manyan jagororin ‘yan bindigan da suka hada da Alhaji Usman Kachalla Ruga da Sani Muhindinge da Yahaya Sani (Hayyu) da kuma Alhaji Shu’aibu duk sun yi alkawarin tsagaita wuta.   Daga baya suka sako mutanen da suka kama kuma suka bar manoma su koma gonakansu ba tare da wata barazana ba.   Sai dai kasa...
    Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta shiga tsakani don sasanta rikicin da ya ɓarke tsakanin Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Shiyyar Kano (KEDCO). Rikicin ya samo asali ne daga katse wutar lantarki da asibitin ya zargi KEDCO da yi, inda ya ce hakan ya kawo cikas ga ayyukan lafiya masu muhimmanci a asibitin, ciki har da zargin mutuwar marasa lafiya. Sasantawar da Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya jagoranta ta biyo bayan zarge-zargen cewa katsewar wutar ta haddasa mutuwar wasu marasa lafiya da ke kan na’urar taimakon numfashi a asibitin. Sai dai KEDCO ya musanta zargin a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, yana mai cewa asibitin na kokarin bata...
    Yarjejeniyar, a cewar daukacin mahalarta taron, ta nuna wani gagarumin mataki na kawo karshen tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane da satar shanu a Arewa maso Yamma, da kuma yankin Arewa.   Yarjejeniyar wacce Mai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, da shugaban karamar hukumar, Babangida Abdullahi Kurfi suka shirya, ta gudana ne a dajin Wurma, inda ake fama da rashin tsaro.   Manyan jagororin ‘yan bindigan da suka hada da Alhaji Usman Kachalla Ruga da Sani Muhindinge da Yahaya Sani (Hayyu) da kuma Alhaji Shu’aibu duk sun yi alkawarin tsagaita wuta.   Daga baya suka sako mutanen da suka kama kuma suka bar manoma su koma gonakansu ba tare da wata barazana ba.   Sai dai kasa...
      Haka kuma, wannan na faruwa ne makonni biyu bayan yin garkuwa da Pastor Friday Adehi na Christian Evangelical Fellowship of Nigeria (CEFN) tare da wani abokin cocinsa bayan kammala wa’azi. Wannan ya kara nuna yadda matsalar garkuwa ke ta’azzara a yankin Kogi East.   A gefe guda, kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Idah, ta bukaci gwamnati a matakai daban-daban da ta dauki matakan gaggawa don kawo karshen satar mutane a jihar. Shugaban kungiyar, Barr. James Michael, ya ce yawaitar garkuwa a kan titunan yankin ya jefa rayukan jama’a cikin hatsari, don haka gwamnati ya kamata ta dauki tsauraran matakai domin kare lafiyar al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
    Antoni Janar na Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke birnin Yamai a Nijar, ya bayyana cewa an kama tsohon Ministan Harkokin Waje, Ibrahim Yacoubou, bisa zargin hannunsa a cikin wata aika-aika ta kisan kai domin yin tsafi. A cewar Maazou Oumarou, lamarin ya samo asali ne daga wani binciken ’yan sanda da aka fara gudanarwa tun a ranar 29 ga Yuli, 2025. KEDCO ya ƙaryata asibitin AKTH kan mutuwar majinyata saboda ɗauke wuta Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja Ya bayyana cewa, an soma gudanar da binciken ne dangane da yunƙurin kisa a wani yanki da ke wajen birnin Yamai, lamarin da ya kai ga cafke ababen zargin a garin Dosso. Wani mutum mai suna Mahamadou Noura...
    KADA ta yi gargaɗi cewa haƙurin jama’a ya ƙare, tana mai jaddada cewa shiru da halin ko-in-kula daga shugabanni ba za a ƙara yarda da shi ba. Sun yi kira da a tabbatar da adalci da kuma mayar da zaman lafiya a yankin, tare da nuna goyon baya ga iyalan mamacin da ɗaukacin al’ummar Garga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Jihar Neja, Umar Mohammed Bago, ya janyo ce-ce-ku-ce a fadin Najeriya bayan da ya sake jaddada cewa duk wani malamin addini da ke shirin yin wa’azi dole ne ya gabatar da rubutaccen wa’azinsa domin tantancewa kafin ya gabatar da shi ga jama’a. A cewar gwamnatin jihar, wannan mataki na da nufin daƙile kalaman ƙiyayya, tsattsauran ra’ayi da barazanar tsaro da ke tasowa daga wa’azin da ba a tantance ba. Da yake jawabi a shirin Politics on Sunday na gidan talabijin na TVC, Gwamna Bago ya musanta zargin cewa dokar ta hana wa’azi gaba ɗaya, yana mai cewa matakin na da nufin tabbatar da zaman lafiya da hana tayar da fitina. Gwamnan ya ce: “Ban hana wa’azi ba. Duk wanda...
    Ministan harkokin wajen Iran ya gana da takwarorinsa na Qatar, Turkiyya, Pakistan da Lebanon a Doha fadar mulkin kasar Qatar Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da takwaransa na Qatar a gefen taron ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a birnin Doha. Doha ta sanar da cewa, fira ministan kasar Qatar kuma ministan harkokin wajen kasar ya yi nazari kan al’amuran yankin na baya-bayan nan yayin ganawarsa da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi. A yayin wannan taro, harin da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar a birnin Doha shi ne babban abin da ake tattaunawa akai. Araqchi yayi Allah wadai da harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai, yana mai tabbatar da goyon bayan Jamhuriyar...
    Kwamitin koli na tsaron kasa ya amince da yarjejeniyar da hukumar makamashin nukiliya ta duniya IAEA Kwamitin koli na tsaron kasar Iran ya yi gargadin cewa, idan aka dauki wani mataki na nuna adawa ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran da cibiyoyinta na makamashin nukiliya, ciki har da sake farfado da kudurorin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da suka kare, za a dakatar da aiwatar da tsare-tsare da yarjejeniyoyin da aka kulla da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA. Sakatariyar kwamitin tsaron kasar Iran ta fitar da wata sanarwa a jiya Lahadi, bayan yarjejeniyar da aka rattabawa hannu tsakanin Seyyed Abbas Araqchi da Rafael Grossi. An yi wannan bayani ne dangane da tsare-tsare da ministan harkokin wajen kasar...
    Gwamnatin Sudan ta ce: Babu batun sasantawa da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces na kasar wadanda take daukansu a matsayin ‘yan tawaye Gwamnatin Sudan ta yi watsi da shawarar sasantawa da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces (RSF) da kasashen kasashe masu shiga Tsakani suka gabatar, tana mai jaddada cewa, tana mutunta duk wani kokari da zai taimaka wajen kawo karshen yakin kasar, matukar dai ya mutunta diyaucin kasar da halaltattun hukumomin kasar. Sa’o’i kadan bayan kaddamar da shirin na bangarori hudu masu shiga tsakani wanda ya hada da Masar, Amurka, Saudiyya, da Hadaddiyar Daular Larabawa, na kiran zaman lafiya a Sudan da kawo karshen yakin, dakarun kai daukin gaggawa sun kai hari kan tashar...
    A ƙalla fasinjoji 17 ne suka rasa rayukansu bayan wata motar haya ta faɗa cikin wata gada da ta ruguje a kan titin Gwalli da ke ƙaramar hukumar Gummi, jihar Zamfara. A cewar hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Zamfara, hatsarin ya faru ne a daren Lahadi lokacin da motar ɗauke da kaya da fasinjoji ta faɗa cikin gadar da ta ruguje. Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, SRC Isah Aliyu, ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa da ya fitar. Kwamandan FRSC na jihar, CC Aliyu Magaji, wanda ya ziyarci wurin hatsarin, ya bayyana matuƙar baƙin cikinsa da asarar rayukan, inda mafi yawansu mata ne. Ya ce hatsarin ya biyo bayan nauyin da aka ɗora wa motar fiye...
    Hukumar jin daɗin jama’a ta Jihar Kwara tare da haɗin gwiwar Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya sun kama wasu mabarata a titunan Ilorin, ciki har da wasu da aka samu da kuɗaɗen ƙasashen waje. Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani mabaraci mai suna Musa Mahmud daga Jihar Kano, wanda aka samu da takardar daloli. Musa Mahmud ya shaida wa manema labarai cewa wani ne ya ba shi takardar Dala a Abuja. Jami’ai sun bayyana damuwa kan yadda masu bara ke riƙe da kuɗaɗen da ba su dace da yanayin rayuwarsu ba. Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki Cire tallafin man fetur shi ne abin da ya dace —Sarki Sanusi II “Za mu...
    Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Barcelona ta koma matsayi na biyu a kan teburin gasar La Liga ta Sifaniya bayan ta lallasa ƙungiyar Valencia a filin wasa na Johan Cruyff da ke birnin Barcelona. Fermin Lopez, Raphinha da Lewandowski ne suka zura ƙwallaye shida a ragar Valencia a wasan da aka buga da misalin ƙarfe 8 na dare agogon Nijeriya. Da wannan nasara, Ƙungiyar da Hansi Flick ke jagoranta ta tara maki 10 a cikin wasanni huɗu da ta buga a gasar. Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Gasar Firimiyar Nijeriya Ta Bana Rashford Na Dab Da Komawa Barcelona A Matsayin Aro An yi tsammanin Barcelona za ta fara buga wasan gidanta a sabon filin Spotify Camp Nou da aka...
    Babban attajirin Afirka kuma Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ɗauki nauyin gina ɗakunan kwanan ɗalibai masu gadaje 250 da Babban Masallacin Juma’a na Ilorin ya tsara a Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara.   An kiyasta aikin zai ci kusan naira biliyan 1.1, kuma an ƙaddamar da shi ne domin samar da hanyar samun kuɗin kula da masallacin. Ana sa ran kuɗaɗen haya da za a samu daga ɗaliban da za su zauna a wurin zai rika shiga asusun kula da masallacin. Sakataren kwamitin amintattu na masallacin, Alhaji Shehu AbdulGafar, ya shaida wa manema labarai a Ilorin cewa Ɗangote ya riga ya sanar da su cewa zai ɗauki nauyin aikin gaba ɗaya. Cire tallafin man fetur shi ne...
    Ma’aikatar tsaron Isra’ila ta ce fiye da sojojin kasar 20,000 ne suka ji rauni tun farkon yakin da aka fara a Gaza a watan Oktoba 2023, inda fiye da rabinsu ke fama da matsalolin lafiyar kwakwalwa, ciki har da ciwon damuwa. A cewar sashen bayar da shawarwari na ma’aikatar, kusan kashi 56 cikin 100 na wadanda suka ji rauni sun kamu da wasu matsalolin lafiyar kwakwalwa, wanda ke nuna irin tasirin matsalar kwakwalwa da wannan rikici ke haifarwa. Ma’aikatar ta kara da cewa kusan kashi 45 cikin 100 na wadanda suka ji rauni suna fama da raunuka a jiki, yayin da kashi 20 cikin 100 na sojojin ke fama da matsalolin kwakwalwa da na jiki a lokaci guda. Share 0...
    Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya koka bisa yawan bashin da Najeriya ke ciyowa da kuma yadda gwamnati ke facaka da kuɗaɗen. Sarkin wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ne, ya kuma bayyana cewa cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi shi ne mafi alheri, yana  mai cewa da Gwamnatin ba ta cire tallafin mai ba, da Najeriya ta daɗe da tsiyacewa. “Adawata a ɓangaren shan man ne, saboda muna ba da aikin yi ga matatun mai a Turai. Muna ba da aikin ga masu tace ɗanyen man,” in ji Sarki Sanusi. Da yake jawabi a Taron Adabi na Duniya na Kano (KAPFEST) da aka gudanar a Kano ranar Asabar, masanin tattalin arzikin ya bayyana...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ambaliyar ruwa na cigaba da salwantar da dukiyoyi da rayukan al’ummomi da dama a sassa daban-daban na Najeriya.   Ko a farkon makon nan, hukumomi sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar a jihohi akalla 11. Sai dai wasu alummomin tuni suka dauki matakai don rage barnar da ambaliyar ka iya yi musu. NAJERIYA A YAU: Masu Nau’in Jinin AS Sun Fi Masu Nau’in AA Lafiya DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku A kan wadannan matakai shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari. Domin sauke shirin, latsa nan
    Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya roƙi Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na KEDCO ya gaggauta dawo masa da wuta bayan rasuwar wasu marasa lafiya da ke samun kulawa ta ceton rayuwada na’ura. Wata sanarwa da kakakin asibitin, Hauwa Inuwa Dutse ta fitar ta nuna takaici bisa rasuwar marasa lafiyan, tana mai cewa mace-macen waɗanda za a iya kauce wa ne idan akwai tsayayyiyar wutar lantarki. Ta bayyana cewa Asibitin yana AKTH yakan biya kuɗin wuta akai-akai daga kuɗaɗen shigansa, kuma yana kashe kuɗaɗe wajen sanya mai a janareto domin amfani idan aka ɗauke wuta daga KEDCO. Don haka, “Hukumar gudanarwar Asibitin AKTH na roƙon Kamfanin KEDCO da ya taimaka wa ayyukan asibitin ta hanyar dawo da wutar a yayin...
    Sarakunan suna bada haɗin kai wajen tafiyar da harkokin gwamnatin ƙasarsu, suna kuma jin basu tare da wata matsala ba tare da matsayinsu. Yawancin Sarakuna da kuma wasu manyan msu Sarautar gargajiya bugu da ƙari suna cikin majlisar dattawa a lokacin. Duk kuma wani lokaci da Sarakunan gargajiya suka fahimci suna fuskantar barazana dangane da tsaronsu, ta haka ne za su fara wasu tafiye- tafiye basu nan basu can, wanda idan ba sa’a aka yi ba, kusan ƙarshen ƙasar ke nan a matsayinta na tarayyar Nijeriya a lokacin. Duk wani ƙoƙarin da Abubbakar Tafawa Balewa ya yi na kasancewa ya zama kamar yadda Kwame Nkrumah na Ghana, wanda a zamaninsa kome ya ce daidai ne sai an bi ko amfani...
    A yau Lahadi ne wakilan kasashen Sin da na Amurka, sun isa birnin Madrid na kasar Sifaniya, domin gudanar da tattaunawa game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya. Cikin kwanaki masu zuwa, sassan biyu za su zanta game da batutuwan da suka hada da matakin Amurka na kakaba haraji, da karya ka’idar kayyade fitar da hajoji, da batun dandalin TikTok, kamar dai yadda kakakin ma’aikatar cinikayyar Sin ya tabbatar a ranar Jumma’a. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ƙwallon ɗaya tilo da kyaftin din ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars Ahmed Musa ya ciwa ƙungiyar tayi sanadiyar samun nasarar farko da ƙungiyar tayi tun bayan fara wannan kakar wasannin ta bana. Pillars ta doke abokiyar karawarta Enugu Rangers da ci 1-0 a wasan da suka buga a filin wasa na Sani Abacha dake birnin Kano inda ɗaruruwan magoya bayan ƙungiyoyin biyu suka shaidi wasan. Kano Pillars Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Gidan Rediyon RFI Hausa Zan Yi Ƙoƙarin Dawo Da Martabar Kano Pillars A Idon Duniya — Ahmed Musa Kafin yanzu ƙungiyar, mallakar gwamnatin jihar Kano ta yi rashin nasara biyu sannan ta buga canjaras ɗaya a wasanni uku da ta buga a wannan kakar, wannan nasarar da Sai...
    Tun daga ranar 18 ga wata, za a kaddamar da fim mai taken 731 a sassan duniya da dama, fim din da ya bayyana yadda rundunar sojojin kasar Japan da suka kutsa kasar Sin suka gudanar da nazari a kan hada makamai da cututtuka tare da gudanar da gwaje-gwaje a jikin al’ummar kasar Sin, a birnin Harbin na lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin, kafin al’ummar kasar Sin su cimma nasarar yaki da su.   A ranar 19 ga watan Agusta, hukumar kula da tsaron kasar Rasha ta fitar da wata takardar sirri da yanzu gwamnati ta mayar da ita ba ta sirri ba, wadda ta nuna cewa, domin neman yin amfani da makaman da aka hada...
    Bikin baje kolin hada-hadar ba da hidima na kasa da kasa wato CIFTIS a takaice na shekarar 2025 da aka rufe a yau Lahadi, ya ja hankalin masu saka jari daga tarin kasashen waje. Manyan jami’an kamfanoni na kasashen waje sun bayyana cewa, suna daukar bikin a matsayin wata babban dandamali na more damammaki tare da kasar ta Sin. Game da dalilan da suka sa ake zabar kasar Sin don gudanar da hada-hadar kasuwanci, mataimakin babban darekta mai kula da harkokin gwamnati da manufofi na kasar Sin na kamfanin Johnson & Johnson Mr. Zhao Jun ya ce, “Da farko shi ne, don biyan bukatun gaggawa na Sinawa kimanin miliyan 1400 a fannin kiwon lafiya. Na biyu a Sin akwai wani...
    A cikin shekaru uku da kafuwarta, gidauniyar Misilli, ta mayar da yara 150 makarantar boko a Jihar Gombe, ciki har da mata 88 da maza 62, tare da ɗaukar nauyin kuɗaɗen karatunsu. Wannan mataki ya taimaka wajen rage nauyin iyaye marasa hali, inda suka samu ’yancin zaɓar makarantun da ke kusa da su. Ambaliya: NEDC ta raba wa mutum 2,200 kayan agaji a Yobe An yi wa zakarun wasan motsa jiki ruwan kuɗi a Akwa Ibom Shirin AGILE ya tallafa wa gidauniyar da litattafai domin ƙarfafa wannan yunƙuri, lamarin da shugabar shirin a Gombe, Dokta Amina Haruna Abdul, ta yaba da shi tare da alƙawarin yin haɗin gwiwa. Ita ma, Dokta Hauwa Yahaya Umar daga SUBEB, ta ce irin wannan...
    Ya zuwa ranar Alhamis 11 ga watan nan, lokacin da aka kammala taron baje kolin kasa da kasa na hada-hadar zuba jari da cinikayya na kasar Sin karo na 25, an riga an sanya hannu kan yarjejeniyar gudanar da ayyukan zuba jari a sassa daban daban da yawansu ya kai 1,154, tare da tsara shigar da jarin da ya kai kudin Sin yuan biliyan 644. Yayin taron, tarin kusoshin manyan kamfanonin kasa da kasa sun shaida cewa, har kullum kasar Sin ta zamo wuri da aka fi aminta da shi ta fuskar zuba jari da samar da ci gaba tsakanin sassan duniya. Game da hakan, shugaban kungiyar bunkasa cinikayya ta Amurka dake kudancin kasar Sin Harley Seyedin, ya ce wani...
    Masana’antar Kannywood Na Tsananin Buqatar Addu’a – Hauwa Garba Dole Mu Hada Kai Da ‘Yan Siyasa Don Ciyar Da Masana’antar Kannywood Gaba -Shugaban MOPPAN Ko za ka faɗawa masu karatu ɗan taƙaitaccen tarihinka? Ni haifaffen ɗan Zaria ne, wani gari da ake cewa, Samaru ana yi masa laƙabi da Samarun Zaria. Kuma nan nake a Hayin Dogo layin Ɗahiru Baban Naira. A nan na tashi tare da iyayena, mahaifina ana ce masa Malam Hassan mai maganin gargajiya, gida mai almajirai. Bayan na taso iyayena suka kai ni makarantar Allo, bayan nayi shekaru biyu aka dawo da ni aka saka ni a firamare. Na samu na yi ‘primary three’ dan ko gamawa ban yi ba, daga nan aka ƙara kai ni...
    Gwamnatin Tarayya ta sanar cewa Samun Lambar Tantance Haraji (Tax ID) zai zama wajibi ga duk ƴan  Nijeriya da ke hulda da bankuna da sauran ayyukan hada-hadar kudi daga ranar 1 ga Janairu, 2026. Wannan sabon umarni yana cikin Dokar Gudanar da Haraji ta Nijeriya, 2025, wacce shugaban kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kwanan nan. A karkashin Sashe na II, bangare na 4 na dokar, dukkan mutane da kungiyoyi da abin da haraji ya shafa dole ne su yi rajista a hukumomin haraji da suka dace kuma su samu Katin Tantance Haraji (Tax payer Identification Card). Dokar ta ba hukumomin haraji ikon bayar da Tax ID a madadin wadanda suka gaza yin rajista, ko su ki karbar bukata idan...
    A cewar sanarwar, bisa wannan sanarwar, fadar ta shugaban ƙasa, ta yanke duk wata huɗɗa da Umunubo. Sanawar ta kuma jaadda cewa, ya zama wajbi ɗaukacin masana’antun da ke a ƙasar nan, su nesanta kansu, da yin dukka wata huɗɗa da Umunubo da sunanan gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu. Idan za a iya tunawa, Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa, fadar shugaban ƙasa, ba ta fitar da wata ƙwaƙwarar sanarwa, kan maƙasudin soke takardar ɗaukar aikin da aka yiwa Umunubo ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    An gano gawar Haneefa, yarinya ’yar shekara uku da ruwa ya tafi da ita lokacin da yayarta Fatima, ke goye da ita yayin ambaliyar da ta rutsa da su a Tudun Jukun da ke Zariya, a Jihar Kaduna. An tsinci gawar ne bayan kwanaki shida da aka kwashe ana nemanta, a gangaren ƙasan Kilaco, unguwar Gyallesu, da misalin ƙarfe 11 na safiyar ranar Lahadi. Ambaliya: NEDC ta raba wa mutum 2,200 kayan agaji a Yobe Likitoci sun janye yajin aikin da suka fara bayan kwana biyu Babban jami’in ƙungiyar Red Cross a Zariya, Abdulmumin Adamu ne, ya tabbatar da gano gawar, inda ya ce hakan ya kawo ƙarshen binciken neman mutanen da ruwa ya tafi da su. A ranar 8...
    Sama da kashi casa’in (90%) na kabilu da mabiya addinai da ke raye cikin Nijeriyar yau, ba su damu da samar da shugabanci nagari cikin Kasar ba a aikace, sai dai kawai a mafarkance. Za a iya gane hakan ne ta hanyar nazartar aiyukansu hada da furuce-furucensu!!!. Da daman mutane ba sa zaɓar wani kansila da zuciya guda, sai don ya dare kujerar ne ya biya musu bukatunsu na daidaiku. Haka Ciyaman, haka “yan Majalisun jiha, haka Gwamna, haka” yan Majalisun taraiya, haka ma kujerar Shugaban Kasa. A tunanin akasarin mutane a yau, bukatunsu na daidaiku, shi ne mazaɓa, shi ne karamar hukuma, shi ne jiha, kai, kacokan ma shi ne Nijeriya. Saboda haka, wajen samun biyan wadancan bukatu, komai...
    “Shawarar tsarin shugabancin duniya” ta zama kalmar da aka sha karanta a rahotannin kafofin watsa labaru na duniya cikin kwanakin baya. Shugabannin wasu kasashe da dama suna ganin cewa, wannan shawarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a yayin taron koli na SCO da aka gudanar a kwanan baya a birnin Tianjin, tana da muhimmiyar ma’ana a fannin warware matsalolin da suka shafi tsarin shugabancin duniya a yanzu. A halin yanzu, sauyin karfi a tsakanin kasashe masu ci gaba da ma kasashe masu tasowa shi ne sauyi mafi girma da aka samu a sabon zamanin da muke ciki a fagen kasa da kasa, inda tarin kasashe masu tasowa suka bunkasa da sauri. To sai dai kuma tsarin duniya...
    An yi wa ’yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Jihar Akwa Ibom ruwan kuɗi, bayan sun yi fice a gasar wasannin motsa jiki ta ƙasa da aka yi wa laƙaba da IBOM 2025, wacce aka kammala a ƙarshen makon nan. Gwamna Umo Eno, ya bai wa gwarazan ’yan wasan da suka lashe kambin Zinare kyautar Naira 500,000, waɗanda suka samu Azurfa Naira 250,000, yayin da waɗanda suka lashe Tagulla suka tashi da Naira 150,000. A jawabinsa na rufe gasar da aka gudanar a filin wasa na Uyo, babban birnin jihar, Gwamna Eno ya bayyana cewa dukkan ’yan wasan sun fito ne daga ƙananan hukumomi 31 na jihar. Baya ga kyautar da ’yan wasa suka samu, gwamnan ya bai wa kowace...
    Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC), ta raba wa mutum 2,261 da ambaliyar ruwa ta shafa a Potiskum, Nangere da Jakusko a Jihar Yobe, kayan agaji. An raba kayan ne a unguwanni 21 na Potiskum, ƙauyukan Kolo da Ajim a Nangere, da kuma kauyukan Dachia, Yim, Saminaka, Garin Maji da Amshi a Jakusko. Gwamnati ta gargaɗi jihohi 11 kan yiwuwar afkuwar ambaliya a wannan makon Ban taɓa nadamar shiga Kannywood ba — Kabiru Nakwango Kayan da aka bayar sun haɗa da shinkafa, taliya, man girki, da kuma tufafi, kayan mata da shadda. Sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), Dokta Mohammed Goje, ya ce Gwamna Mai Mala Buni ya ba da umarnin gaggauta tallafa wa al’ummar...
    An karrama fitattun fina-finai daban daban a bikin “Golden Panda” da ya gudana jiya Asabar a birnin Chengdu na lardin Sichuan dake kasar Sin. A bana, an gudanar da bikin ne a karo na biyu, wanda kuma gungun sassan bunkasa harkokin adabi da al’adu da gwamnatin lardin Sichuan suka dauki nauyin shirya shi. Bikin na bana, ya hallara baki daga sassan duniya da dama, an kuma gabatar da lambobin yabo ga fina-finai da wasannin kwaikwayo karkashin rukunoni 27. Cikin fina-finan da aka karrama akwai Ne Zha 2, wanda ya lashe lambar yabo ta wasan zane mai motsi mafi kayatarwa. Sai fim din “There’s Still Tomorrow”, wanda ya zama fim mafi kayatarwa. Fim din “She and Her Girls” ya samu yabo...
    A cikin sanarwarsa, Daso ya ce: “Rundunar Ƴansanda ta Jihar Borno na sanar da jama’a cewa an gano gawar wani mutum da ba a tantance ba a kusa da na’urar sauya wuta (transformer) a Jami’ar Jihar Borno, Maiduguri. “Binciken farko ya nuna cewa marigayin ya mutu ne sakamakon jan wutar lantarki yayin da yake ƙoƙarin cire kayayyakin lantarki. “Rundunar ta fara cikakken bincike kan lamarin, kuma tare da haɗin gwiwar Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Borno an kwashe gawar zuwa asibiti domin a gudanar da binciken likitanci yadda ya kamata.” Ya jaddada cewa rundunar ta jajirce wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da yin gargaɗi ga mazauna jihar da su guji aikata lalata kayayyakin gwamnati. Daso ya ƙara da...
    Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗi cewa jihohi 11 na iya fuskantar ruwan sama mai yawa wanda ka iya haddasa ambaliya daga ranar Lahadi zuwa Alhamis. A cikin sanarwar da Cibiyar Gargaɗin Ambaliya ta Ƙasa, ƙarƙashin Ma’aikatar Muhalli, ta fitar, jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Adamawa, Benuwe, Nasarawa, Taraba da Delta. An yi wa zakarun wasan motsa jiki ruwan a Akwa Ibom Ban taɓa nadamar shiga Kannywood ba — Kabiru Nakwango Sauran sun haɗa da Neja, Kebbi, Kano, Katsina, Sakkwato da Zamfara. Sanarwar ta bayyana cewa cikar kogunan Gongola, Benuwe da Neja na ƙara barazana ga al’ummar da ke zaune a gefen kogunan. Gwamnati ta shawarci al’ummar da ke yankunan da abin ya shafa, musamman waɗanda ke kusa...
      A cewar kakakin ‘yansandan, jami’an sun tare wata mota kirar Toyota Corolla mai launin toka mai lamba GGE 473 BH bayan direban ya kasa bayar da kwakkwaran bayanin kansa da kuma motar.   Ya bayyana cewa binciken da aka yi wa motar ya kai ga gano wata bindiga da aka kera a cikin gida, harsashi masu rai guda hudu, fasfon aikin ɗansanda na bogi da kuma waya lambar mota mai lamba FGE 68 a Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Lawal ya ƙara da cewa, ɗaukacin guraren da Jiragen Ruwa ke tsaya, akwai launin da kuma lamba da aka amince,manyan motocin za su rinƙa yin amfani da su, domin yin zirga-zirga  a Tashar ta Apapa. “Misali, a APMT, manyan motocin za su rinƙa yin amfani da lamba  001 mai ɗauke launin ruwan bula, inda kuma a ENL Consortium, za su rinƙa yin amfani da lambApapaETO bisa nufin rage cunkoso a ciki da kuma wajen Tashar ta Apapa.ɗauke da launin rawaya,” Inji Lawal. Ya bayyana cewa, wannan sabon garanbawul ɗin da aka yi, za ta taimaka wajen matsalar ƙetarawa hanyar da manyan motocin ke fuskanta a Tashar ta Apapa. Lawal ya ci gaba da cewa, bisa nazarin da aka gudanar a...
    An yi wa ’yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Jihar Akwa Ibom ruwan kuɗi, bayan sun yi fice a gasar wasannin motsa jiki ta ƙasa da aka yi wa laƙaba da IBOM 2025, wacce aka kammala a ƙarshen makon nan. Gwamna Umo Eno, ya bai wa gwarazan ’yan wasan da suka lashe kambin Zinare kyautar Naira 500,000, waɗanda suka samu Azurfa Naira 250,000, yayin da waɗanda suka lashe Tagulla suka tashi da Naira 150,000. A jawabinsa na rufe gasar da aka gudanar a filin wasa na Uyo, babban birnin jihar, Gwamna Eno ya bayyana cewa dukkan ’yan wasan sun fito ne daga ƙananan hukumomi 31 na jihar. Baya ga kyautar da ’yan wasa suka samu, gwamnan ya bai wa kowace...
    Hakazalika, sojojin na Brigade 12 tare da hadin gwiwar dakarun hadin gwiwa da ’yan banga a wannan rana, sun ceto fasinjoji 17 da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Lokoja ta jihar Kogi.   Hakazalika, dakarun Sashe ta 1 ‘Operation Whirl Stroke (OPWS)’ sun ceto wani a karamar hukumar Katsina-Ala ta jihar Benuwe.   Haka kuma a jihar Filato a wannan rana, dakarun Sashe ta 8 ta ‘Operation Enduring Peace (OPEP)’ sun kama wasu da ake zargin barayin ne a karamar hukumar Mangu tare da kwato makamai da alburusai da kudade.   A wani samame kuma sojojin na Shiyya ta 1 OPWS sun kwato bindiga kirar AK-47 daya da harsashi 29 a wani sintiri a...