Iran Ta Bukaci Mayar Da Martani Kan Aniyar Isra’ila Ta Mamaye Yankunan Kasashe Domin Kafa ‘Babbar Isra’ila’
Published: 14th, August 2025 GMT
Kasar Iran ta jaddada wajabcin daukar kwararan matakai na kasa da kasa don dakile muradun gwamnatin mamaya na mulkin mallaka
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Ismail Baqa’i ya yi Allah wadai da kalaman fira ministan gwamnatin ‘yan sahayoniyya da ake nema ruwa a jallo a kotun kasa da kasa ya yi dangane da abin da ake kira “Kafa kasar babban Isra’ila”.
A cikin wani rubutu da ya wallafa a safiyar yau Alhamis, Baqa’i ya yi ishara da yadda ake ci gaba da keta doka da kuma aikata munanan laifuka da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta ke tafkawa, musamman ma mamaye yankunan Falasdinawa da kisan kare dangi da ake ci gaba da yi a kan al’umma Falasdinu.
Baqa’i ya ci gaba da cewa: Amincewar da fira ministan gwamnatin ‘yan sahayoniyya ya yi na cewa yana da ”aiki na tarihi da na ruhi” don tabbatar da wannan muguwar tunani tun daga kogin Nilu har zuwa Fırat, wata shaida ce karara ta mulkin mallaka ta masu yanke shawarar wannan gwamnati ta miyagun al’umma da kuma kai hari kan ‘yantacciyar kasa mai ikon domin mamaye yankunan kasashensu, kuma wajibi ne a yi Allah wadai da wannan muguwar manufa ta tunanin mamaye yankunan kasashen musulmi daga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar hadin kan kasashen musulmi, da dukkanin gwamnatoci, a matsayin wannan furuci na cin zarafi da keta ƙa’idodi da manufofin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da dokokin dokokin ƙasa da ƙasa.”
Iran
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ya Bayyana Isra’ila A Matsayar ‘Yar Yaudara August 14, 2025 Hizbullahi Ta Yaba Wa Iran Kan Irin Gudumawarta Ga Lebanon Da Gwagwarmaya August 14, 2025 Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Fatali Da Batun Kafa Gwamnatin Hadaka A Kasar Sudan August 14, 2025 Larijani a Beirut: Iran A Shirye take ta taimaka ma Lebanon August 14, 2025 Masar ta yi Allawadai da furucin Netanyahu kan shirin kafa Isra’ila Babba August 14, 2025 Hamas ta aike da sakon jinjina ga al’ummar Yemen kan goyon bayan Gaza August 14, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 130 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 129 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 128 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 127 August 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Majalisar Dinkin Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
China Ta Sha Alwashin Maida Martani Kan Harajin Trump A Kanta Na 100%
Kasar China ta maida martani kan kasar Donal Trump na kasar Amurka, wanda ya karawa kasar kudaden fito 100% na kayakin kasar da ke shigowa Amurka.
SHafin yanar gizo na ArabNews ya nakalto kasar China a jiya Asabar tana cewa zata dauki matakan da suka dace kan Karin kudanen fito na 100% wanda shugaban Trump yayi. Kuma ta yi kira ga Trump kan cewa ya rungumi tattaunawa da kasar China ya fi masa kan barazana gareta.
Ma’aikatar kasuwanci na kasar China ta bayyana cewa, basa son yakin kudaden fito amma basa tsoronta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Yi Girgizar Kasa Mai Daraja 5 A Ma’aunin Richter A Kasar Habasha October 12, 2025 Shugaban Kasar Najeriya Ya Yi Afuwa Ga Wasu Mutanen Da Kotuna Su Ka Hukunta October 12, 2025 An Yi Musayar Wuta A Tsakanin Masu Tsaron Iyakokin Kasashen Afghanistan Da Pakistan October 12, 2025 Afirka Ta Kudu Ta Ce Babu Wata Makarkashiya A Mutuwar Jakadanta A Kasar Faransa October 12, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Yunkurin Balair Na Yiyuwar Shiga Gwamnatin Gaza. October 11, 2025 Cuba Ta Bayyana Bada Kyautar Noble Ga ‘Yar Kasar Veunzuelas machado A Matsayin Abin Kunya. October 11, 2025 Kasar Indunusiya Ta Hana Tawagar wasan Jiminastik din Isra’ila Visar Shiga Kasarta October 11, 2025 Ammar Hakim Ya Gargadi Kasashen Yamma Da su Kiyayi Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gidan Kasar. October 11, 2025 Sarkin Morocco Ya yi Magana Tun Bayan Barkewar Zanga-zanga A Kasar . October 11, 2025 Wani Dan Majalisar Dokokin Kasar Iran Ya Ja Kunnen Amurka Kan Taba Jiragen Dakon Man Kasa October 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci