Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 116
Published: 2nd, May 2025 GMT
114-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin Alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Mutahhari ko cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddin Romi ko kuma cikin wasu littafan, da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a wannan shirin.
//… Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin kisser Imam Al-Hassan limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All…(s) kuma da na farko ga Fatimah (S) diyar manzon All..(s) kuma jakansa na farko da muke kawo maku, a shirimmu da ya gabata mun tsaya inda muka bayyana cewa, Bayan wasikun da sahabban manzon All…(s) suka rubutawa sauran sahabban da suka rage a sauran garuruwan, musulmi da kuma wadanda suke ribadi a kan iyakokin daular musulmi suna kiransu da cewa, su dawo madina don tsaida khalifancin manzon All..wanda khalifa Uthman ya maida shi wasa.
Mun karanta wani bangare da wasikun da suka rubuta, sannan mun bayyana suka amsa kirar. Mun kuma bayyana wasu sunayen wadanda suka taho daga kasar Masar, Da wasu da suka zo daga Kufa da kuma wasu da suka zo daga Basra.
Daga karshe munji yadda mutanen Masar suka rubutawa Khalifa wasika suna gargadinsa kan ya gyra, al-amuran khalifanci, ya kuma tuba daga laifukan da ya aikata,
Mun yadda khalifa ya tsorata ya aiki, Mugira yayi masu magana amma sun ki magana da shi, haka ma Amru dan Asi. Daga karshe sai da ya fake da da Amirul muminina, (a) wanda yayi masu magana suka amince, kuma suka karbi wata takarda ta shaida kan cewa ya sha Alwashin zai gyar, zai yi aiki da alkur’ani mai girma da sunnar manzon All..(s), zai basu hakkokinsu, da kudadensu. …sannan Amirul muminina (a) shi ne mai lamuninsu, kan hakan. Aamma mun ke cewa suna Tafiya sai Marwan dan Hakan ya je ya fada masa, ya warware alkawalin da ya dauka, ya haw mimbari ya fadi cewa mutanen masar sun tafi ne, bayan sun gano cewa abinda ake zarginsa da sub a gaskiya bane.
A lokacinda Khalifa ya haw kan mimbare ya fadi haka, sai muryoyi suka tashi suna ta fada masa, Uthman ka ji tsoron All..ba gaskiya ne ka fada ba. A nan sai yayi sauri ya shiga cikin gida.
Sai labarin ya kaiwa mutanen kasar Masar wadanda suke kan hanyar komawa gida bayan sun karbi takarda daga Khalifa kan ya tuba kuma zai gyra. Daga nan suka sake dawowa Madina, tare da niyyar abu biyu ko khalifa ya sauka daga matsayinsa na Khalifan musulmi don bai cancanta ba, suna ganin Marwan dan Hakam ne kawai yake jujjuya shi yana halakashi, idan ya ki kuma su kasheshi kamar.
A nan sai al-amura suka rincabewa Khalifa, inda yan tawaye daga kasashen daban –daban sun yi wa gidansa kawanyan, kuma suna neman kashe shi ne kawai. Wasu malaman tarihi sun bayyana cewa. Al-amura sun kai ga khalifa Uthman bai da kuma wanda zai taima masa a kan wadanda suke son kashe shi, sai ya aikawa Mu’awiya dan Abu Sufyan ya taimaka masa da mayaka, wadanda zasu kare shi.
A cikin wasikar da ya rubuta masa ya zo kamar haka
{Lalle mutanen Madina sun kafirta, sun kuma tube bai’arsu, sun sabawa bai’arsu ka aika mani mayaka daga cikin mutanen sham da suke tare da kai ko menene tsananin hakan…}.
Amma Mu’awiya ya jinkirta aika masa mayaka daga wajensa duk da cewa ya fada masa irin mummunan halin da yake ciki, a lokacinda Uthman ya ga Mu’awiya yayi jinkiri sai ya aikawa Yazi dan Asad wali a kasar Sham, yana kodaitarda da shi ya gaggauta zuwa ya taimaka masa daga irin mummunan halin da yake ciki.
A lokacinda wasikar Uthman ta isa gareshi, Sai yaziz ya yi gaggawa ya tara mayaka don zuwa Madina, karkashin jagorancin Yazid Al-Kasri, sai mu’awiya, sai Mu’awiya ya umurceshi da ya je amma ya tsaya a yankin Zi-Khashab kada ya shiga Madina.
Sojojin Yazid sun tsaya a Zi-Khashab har aka kashe Uthman. Kuma dalilin da ya sa Mu’awiya yayi haka shi ne, don yayi amfani da neman jinin Khalifa Uthman a kan duk wanda ya haw kan kujerar Khalifanci, sannan ya kwaci iko ya maida ita ga Banu Umayya.
Don haka Mu’awiya yana daga cikin wadanda suka taimaka wajen kashe Khalifa Uthman. Don da ya bar rundunar yazid ta karasa cikin Madina da zasu haka kissan.
Abu’ayyubal Ansari da ya hadu da Mu’awiya dan Abusufyan : Lalle wanda ya hada rundunar Yazid dan Asa isa Madina don taimakawa Uthman kai ne}.
Kafin a kasshe shi dai, Khalifa Uthman ya rubuta wasiku zuwa garuruwa da dama wadanda suka hada da Masar, ga wadanda suka je aikin hajji a Makka a lokacin, yana kama kafa da su, su kubutar da shi daga yan tawaye.
Don haka a lokacinda mutanen Masar suka sami labarin cewa Khalifa Uthman ya yaudaresu ne, baya nufin cika alkawalin da ya dauka, sai suka koma Madina, sannan suka yi wa fadar Khalifa kawanya, suna ta daga murya da faduwarsa, suna bukatar ya sauka kawai, ba zasu karbi wani uzurinsa ba.
Ana cikin wannan halin sai Marwan Dan Hakam ya bullo daga kan gida ya zage su, yana cewa me ya hadaku da sha’anin mulki ne, ? kun zo kwace ne ko? All..ya bakanta fuskokinku.
Kuna son ku kwace mana mulkimmu daga hannummu. Ku tafi, !!!. Daga nan sai suka kara fushi, sai Uthman ya sake neman Imam Ali (a) ya taimaka masa, kuma yaji abinda Marwan dan Hakam ya fada masu. Sai ya zo ya na fada masa:
Amma ka yarda da Marwan, !!! ba zai yarda da kai ba, sai ya karkataka daga addininka, da hankalinka, ka zama kamar taguwa mai rauni tana bin mai ita zuwa duk inda ya jata, wallah Marwan ba mutumin addini ne ba, wallah ina ganin ba zai barka ba sai ya shigar da kai inda ba zai fito da kai ba. Kuma ba zan sake dawowa don kareka ba. Ka zubar da mutuncinka, kuma an rinjayeka a kan al-amarinka.
Don lalle wadanda suka kashe khalifa Uthman sune Marwan da danginsa banu Umayya, kuma hatta matar Uthman Na’ila ta ta tabbatar da hakan, a lokacinda yake fadawa umayyawa,: Wallah ku ne kuka kashe shi, kuma maida yayansa marayu.
Banda haka, ta taba yi wa mijinta Nasiha, kan kada yayi biyayya ga Marwan, tana fada masa, : Duk sanda ka biyewa Marwan zai kasheka.
Banda haka Uthman yana da laifi cikin abinda ya sameshi, saboda , a lokacinda ya tabbatar da cewa danginsa banu umayya sun mamaye al-amura sune suke safiyar da al-amura, sannan shim ai Rauni ne a gabansu, don ba zai iya umurtansu ba, kuma ya san cewa al-umma bata sonsu, to ya sauka mana, ya bawa wanda ya dace. Me yasa zai bar al-umma gaba daya su taru su kashe shi.
Sannan yan tawaye sun san cewa, ba zai iya yin kome ba, saboda duk abinda aka yi da shi, sai Marwan dan Hakam ya warwareshi. Sannan ya tube kansa ya bawa wani, ya ki, har yana cewa: Khalifanci rig ace wacce All..ya Sanya masa ita.
Amma gaskiyar ita ce, khalifa Umar ne ya Sanya matai ta, don shi ne ya yi dubara ta yadda zai kai gareta, a shoran mutane 6 da ya kafa. Ko kuma muna iya cewa Abdurrahman dan Auf ne ya Sanya masa ita, don daga karshe bayan mutuwar khalifa Umar shi ne ya zabi Uthman ya bar Ali (a).
Sannan Talha yah ana ruwa shiga gidansa, kuma ya je ya kwace iko da wuraren ajiyar kudade,
Wasu malaman tarihi da dama suna riya cewa, wai Imam Alhassan (a), a (yaum- Aldaddar) watoranda aka yi wa gidan Uthman kawanya, ya fito yana kare Uthman, tare da izinin mahaifinsa (a), har saida ana jika shi da jinin Uthman. Babu shakka, wannan hadisin kirkirarre ne, daga bangaren banu umayya. Sannan Lalle Imam Hassan da mahaifinsa (a) tare da wasu daga cikin sahabban manzon All..(s), muhajirun da ansar basu basu shiga cikin lamarinsa, basu kareshi ba.
Wadanda suka kare shi a lokacin da aka yiwa gidansa kawanya sune banu umayya danginsa, da kuma wasu daga cikin wadanda suka amfana da shi, ko basu kyaututtuka. Kuma da Khalifa Uthman yana da masu goyon baya a cikin mutanen Madina da baza’a kashe shi ba.
Don haka mutanen Madina, sahabbai da wasunsu, sun hadu a kan kyaleshi, a cikin wannan halin ne Imam Hassan (a) shi kadai zai fito sabanin sauran sahabban ya zo yana kare shi.
Don haka gaskiyar al-amarin shi ne, dukkan hadisan da suka yi Magana a kan hakan, raunanane, kamar yadda Allamah Amini ya kawosu daya bayan daya a cikin littafinsa na Ghadir yana warwaresu.
Don haka a lokacinda masu tawaye suka zagaye gidansa, wasu jama’a daga cikinsu, sun shiga gidansa suka kashe shi, daga cikinsu akwai Muhammad Dan Abubakar.
Sun ce Muhammad dan Abubakar ya zare takobi a gabansa, ya ce masa: Wani addini kake ne ya Nathal?
Sai yace bisa addinin Musulunci, kuma nib a Nathal bane, sai shugaban Muminai. Sai yace masa: Ka sauya littafin All..(ma’ana ka ki amfani da shi), sai yace: Littafin All…tsakanina da ku, sai ya kama gemensa ya jashi a kasa, ya ce, masa: Mu a ranar kiyama ba zamu ce: Ya Ubangiji! Lalle mu mun yi biyayya ga shuwagabannimmu da manya-manyanmu sai suka bartar da mu hanya ba. Sai suka farmasa suka kashe shi, suka barshi cikin jininsa. Har ya mutu, sura barashi, a kwace, sauran Banu Umayya sun sun tsere sun barshi. Sai da wasu daga cikinsu suka yi Magana da Imam Ali (a), ya shiga tsakaninsu sai suka yarda a yi masa jana’iza, amma sun ki a bisneshi a makabartan bakiyya, don haka ne suka kaishi wani tsoron makabartan yahudawa da suke madina, wanda ake kira Hashu Kaukab. A zamanin Mu’awiya ne aka hada makabaratan da Bakiyya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Khalifa Uthman ya khalifa Uthman ya Marwan dan Hakam wadanda suka Mu awiya ya
এছাড়াও পড়ুন:
Dubban Mutanen Burkina Faso Sun Yi Gangamin Nuna Goyon Bayan Shugaban Kasa Ibrahim Traore
Kwanaki kadan bayan wani furuci daga babban jami’in sojan Amurka a Afirka akan shugaban kasar ta Burkina, dubban mutanen kasar sun yi gangami na nuna goyon bayan Kaftin Ibrahim Traore
Gangamin na mutanen kasar Burkina Faso, ya biyo bayan maganganun da su ka fito daga kwamandan sojojin Amurka a Afirka Janar Michael Langley wanda ya zargi sojojin dake Mulki da amfani da ma’adanan kasar saboda kashin kansu maimakon yi wa mutane aiki.
Mahalarta gangamin sun daga kwalaye dake dauke da rubutun yin tir da furucin jami’in sojan na Amurka da kuma nuna goyon baya ga shugaban kasar.
Daga cikin mahalarta gangamin da akwai fitaccen mawakin kasar, Ocibi Joan,wanda ya siffata jami’in sojan Amurkan da dabbar daji mai cin mutane yana mai yin kira a gare shi da kasarsa da su daina yin karya.
Haka nan kuma ya kara da cewa: ” Mutanen Burkina ba su fada da kowa,amma a lokaci daya, ba za su bar masu wawason dukiyar kasarsu ba.”
Wani mutum da ya halarci gangamin Haruna Sawadogo ya fada wa manema labaru cewa, idan suna son ganin bayan Kaftin Traore ne, to su fara ta kan mutanen kasar.
Hakan nan kuma jaddada cewa ba za su bari abinda ya faru da Thoms Sankara ya faru dakanar Troare ba.