Gwamnan Jigawa Ya Halarci Taron Ranar Ma’aikata Ta Bana
Published: 2nd, May 2025 GMT
Gwamna Umar Namadi ya bi sahun kungiyoyin kwadago domin tunawa da irin gudunmawar da ma’aikata ke bayarwa wajen ci gaban jihar Jigawa.
Da yake gabatar da jawabinsa, Gwamna Namadi ya yaba da jajircewar ma’aikatan Jigawa, inda ya bayyana ma’aikata a matsayin masu kawo ci gaba.
Ya bayyana cewa, ma’aikata a dukkan bangarori suna aiki da gaske a matsayin injin da ke ba da kuzarin motsa al’umma zuwa ga ci gaba.
Ya kuma kara jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da walwalar ma’aikata, inda ya bayar da misali da nasarorin da aka samu da suka hada da aiwatar da mafi karancin albashi na Naira 70,000, gina gidaje masu saukin kudi ga ma’aikatan gwamnati, da kuma shigar da sama da Naira biliyan 7 a cikin shirin bayar da gudunmawar fansho na jihar.
Gwamnan ya karkare da sako mai ratsa jiki ga ma’aikata, yana mai cewa, “Watakila ba za ku ji dadin aikinku dari bisa dari ba, amma ina tabbatar muku, guminku ba zai tafi a banza ba.
Kwamared Sunusi Alhassan Maigatari, wanda ya yi magana a madadin kungiyar kwadagon, ya amince da wannan ci gaba, inda ya bayyana Gwamna Namadi a matsayin gwamnan al’umma.
Ya kuma yabawa ajandar gwamnati mai dauke da abubuwa 12, wadanda suka samar da fa’idodi masu inganci da suka hada da daukar dimbin ma’aikata a sassa masu muhimmanci, shirin ba da lamuni na noma ga ma’aikata, da kafa shagunan dake sayarda kaya da rahusa domin dakile matsalolin tattalin arziki.
USMAN MZ/Dutse
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Neja Ya Musanta Rikici Da Mataimakinsa.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago ya bayyana dangantakarsa da mataimakinsa, Kwamared Yakubu Garba a matsayin cikakkiya da jituwa.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai kan dangantakarsa da mataimakinsa bayan bikin ranar ma’aikata a Minna.
A cewarsa, “mu kungiya ce, ba za su iya karya mu ba, hankalinmu yana kan manufa, kuma za mu cimma ta.”
Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da marawa gwamnatinsa baya, tare da tabbatar da cewa wata sabuwar Nijar za ta yiwu.
Binciken da aka gudanar ya nuna cewa mataimakin gwamnan jihar Neja, Kwamared Yakubu Garba bai halarci bikin ranar ma’aikata ta bana a Minna ba wanda wasu al’ummar Nejar din suka yi zargin cewa rashin jituwar da ke tsakanin gwamnan jihar Neja da mataimakinsa tayi tsamari.
KARSHEN ALIYU LAWAL.