Zaɓen 2027: ’Yan Najeriya za su yanke wa Tinubu hukunci — PDP
Published: 25th, April 2025 GMT
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa zaɓen 2027 zai kasance ne kai tsaye tsakanin Shugaba Bola Tinubu da ’yan Najeriya da gwamnatinsa ta jefa su cikin mawuyacin yanayin rayuwa.
Shugaban riƙo na PDP, Umar Damagum, ya jaddada cewa zaɓen “Tsakanin Jam’iyyar APC ne da ’yan Najeriya,” yana mai nuni da wahalar da talakawa ke fuskanta a ƙarƙashin mulkin APC.
Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su haɗa kai don magance abin da ya kira “wahalar da aka kawo mana da gangan.”
Damagum ya kuma yi tsokaci kan sauya sheƙar Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da tsohon Gwamna, Ifeanyi Okowa, tare da mambobin majalisar zartarwarsu, zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
’Yan bindiga sun kashe ango, sun sace amarya a Nasarawa NAJERIYA A YAU: Dalilin da zazzaɓin cizon sauro ba ya jin maganiA hirarsa da tashar talabijin ta Channels, Damagum ya nuna rashin jin daɗi, yana mai cewa PDP ta kasance mai matuƙar goyon baya ga Jihar Delta kuma ba ta cancanci irin wannan siyasar ba.
Amma duk da sauya sheƙar, ya tabbatar da juriya da kuma ƙarfin PDP.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan Najeriya sauya sheka Zaɓen 2027
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi.
Ministan Noma Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa.
Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya.
Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa.
Ya jaddada cewa gwamnati za ta tallafa musu da kayan noma na zamani da wuraran kasuwanci domin inganta tattalin arziki.
A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi na Jigawa ya yaba da samun Cibiyar Cigaban Karakara ta Pulse ta farko a Jigawa, yana mai cewa za ta kawo sauyi a harkar noma da rayuwar jama’ar karkara.
Haka zalika, shi ma Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya ce haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu zai taimaka wajen ci gaban tattalin arziki.
Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu, Alhaji Builder Muhammad Uba, ya jaddada goyon bayansa ga shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu tare da yabawa gwamnatin Namadi kan sauya fasalin noma a jihar.
Usman Muhammad Zaria