NAJERIYA A YAU: Dalilin da zazzaɓin cizon sauro ba ya jin magani
Published: 25th, April 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Zazzaɓin cizon sauro, wato maleriya, na cikin cututtuka mafiya shahara da kuma haɗari a Najeriya.
Wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya nuna cewa Najeriya na da kaso mafi girma na mace-macen da cutar take haifarwa a duniya.
Sau da yawa wanda ya kamu da cutar ta maleriya kan sake kamuwa da ita bayan ya warke.
Ko me ya sa magungunan zazzaɓin cizon sauro suka daina aiki a jikin mutane?
NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Amfani Da Kafofin Sada Zumunta Wajen Haɓaka Kasuwanci DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin ArewaWannan batu shirin Najeriya A Yau zai duba yayin da ake bikin Ranar Malaria ta Duniya.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: maleriya zazzaɓi zazzaɓin cizon sauro
এছাড়াও পড়ুন:
Uganda Ta Sanar Da Kawo Karshen Ebola Da Ta Barke A Kasar
Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Uganda ta sanar da cewa, an kawo karshen Ebola da ta bulla a kasar bayan da aka dauki kwanaki 42 ba tare da an sami mutum daya wanda ya sake kamuwa da ita ba.
A wani bayani da ya fito daga hukumar kiwon lafiya ta duniya ( WHO), ta bayyana cewa, a lokacin bullar cutar an gabatar da mutane 14 masu dauke da ita, an tabbatar da 12 daga cikinsu, sai wasu biyu da ba a same ta a tare da su ba.”
Haka nan kuma hukumar lafiyar ta ce, an sami mutuwar mutane 4 daga cikin wadanda su ka kamu da cutar ta Ebola, wasu mutane 10 kuma sun warke.”
Watanni 9 da su ka gabata ne dai aka tabbatar da bullar cutar a birnin Kamfala bayan da wani mutum da yake dauke da ita ya rasu.
Dajukan da kasar ta Uganda take da su, suna a matsayin matattarar cutar ta Ebola ce, wacce a karon farko ta bulla a cikin kasar a 2000.
A yankin yammacin Afirka cutar Ebola ta kashe fiye da mutane 11,000 a tsakanin 2013 zuwa 2016.