Shugaban hukumar al-adun musulunci da sadarwa a nan Iran Mohammad Mehdi Imamipour ya bayyana cewa za’a gudanar da taron kasa da kasa na kare hakkin bil’adama a karon farko a nan kasar Iran tare da mahangar kasashen gabas.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Imanipour yana fadar haka a yau, ya kuma kara da cewa za’a bude tarurrukan ne a nan birnin Tehran, Qom da kuma Esfahan a lokaci guda daga ranar 28 ga watan Afrilu zuwa 2 ga watan mayu.

Labarin ya ce matsalar kare hakkin bil’adama yana daga cikin al-amuran da ake nuna faska biyu a cikin al-amura da dama a duniya, musamman kan abinda yake faruwa a kasar. Imanipour y ace suna son gudanar da taron ko wani shekaru 4.

Ya zuwa yanzu dai inji shi, an gayyaci masana da kwararru daga kasashe 32 a duniya. Sannan an karbi rubuce-rubuce har 491, daga ciki 186 daga Amurka, Austria, Masart, Kenya, Tunisia, Rasha, China, Kazakhstan, Indonesia, Lebanon, Malaysia, Iraq, Nigeria, Serbia, Espaniya da kuma Netherlands. Har’ila yau tare da 305 daga cikin gida.

Daga karshe yace JMI tana son a samarda wata sabuwar mahanga ta kare hakkin bil’ada a duniya sabanin wadanda kasashen yamma suke jagoranta a halin yanzu.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza

Kasashen duniya na ci gaba da yin tir da sabon farmakin soji da Isra’ila ta kaddamar kan Gaza.

Kasashen Biritaniya, Faransa, Italiya, Masar, Jordan, Qatar, Spain, duk sun yi tir da farmakin kan Gaza suna masu cewa zai kara dagula halin kunci da ake ciki.

Kungiyar tarayyar Turai, ta bakin Jami’ar kula da harkokin wajen  ta, Kaja Kalas, ta yi kira da a sanyawa Isra’ila takunkumi domin matsa wa gwamnatin lamba ta kawo karshen hare-haren da take kaiwa Gaza, tana mai gargadin cewa al’amuran jin kai na kara ta’azzara.

“Hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza zasu haifar da mummunan sakamako game da halin da ake ciki da karin hasarar rayuka, da barna & hijira na jama’a,” in ji Kalas a kan X.

A jiya ne Sojojin Isra’ila suka kaddamar da sabon farmakin ta kasa mai manufar mamaye birnin Gaza bayan shafe makwanni ana kai hare-haren bama-bamai ba kakkautawa ba a kan wasu manyan gine-gine domin tilastawa Falasdinawa kauracewa gidajensu.

Farmakin ya zo ne jim kadan bayan da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya gana da firaminista Benjamin Netanyahu a kusa da masallacin Al Aqsa da ke gabashin birnin Kudus da aka mamaye.

Tun da farko dai, wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan yankunan Falasdinawa da ke mamaye, Francesca Albanese ta yi Allah wadai da hare-haren da Isra’ila ke kai wa birnin Gaza, tana mai cewa wani bangare ne na shirin Isra’ila na shafe Gaza.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran da Saudiyya sun bukaci hadin Musulmi game da halin da ake ci a yankin September 17, 2025 Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza September 17, 2025 Akalla Falsdinawa 78 Ne Suka Yi Shahada A Yau A Gaza. September 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari A Tashar Jirgin Ruwan Hudaida Dake Yamen September 16, 2025 Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki 5 A Wajen Taron kere-kere . September 16, 2025 Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta. September 16, 2025 Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana September 16, 2025 Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi September 16, 2025 Pezeshkian: Ta’addancin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Kan Kasar Qatar Zalunci Ne Ga Diflomasiyya September 16, 2025 Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya September 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Bude Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Beijing 
  • Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya
  • Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza
  • Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza
  • Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci
  • Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida
  • Tawagar Yan Wasan Damben Gargajiya Ta Iran Ta Zama Zakara A Damben Ta Duniya
  • An Fara Taron Hukumar Makamashin Nukliya Ta Duniya IAEA Karo Na 69 A Birnin Vienna
  • Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila
  • Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Runduwar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai