HausaTv:
2025-07-31@13:55:35 GMT

Mutanen Algeriya sun bukaci a rufe ofishin jakadancin Amurka a kasarsu

Published: 5th, April 2025 GMT

Dubun-dubatar al’ummar kasar Aljeriya sun gudanar da wani gagarumin gangami da jerin a wannan Juma’a a birnin Algiers babban birnin kasar, domin yin Allawadai da laifukan yaki da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take aikatawa a kan al’ummar yankin zirin Gaza.

Kamar yadda kungiyar Movement of Society for Peace ta yi kira, dubban  ‘yan kasar Aljeriya ne suka fito domin nuna goyon baya ga al’ummar Palasdinu a gaban hedikwatar jam’iyyar da ke unguwar  al-Mouradia, babban birnin kasar Aljeriya.

Sai dai hukumomin Aljeriya sun kewaye masu zanga-zangar don hana fadada zanga-zangar zuwa wuraren da jama’a ke taruwa.

Masu zanga-zangar sun yi ta rera taken nuna rashin amincewarsu da kisan kiyashin da “Isra’ila” ke yi a Gaza, inda suka yi Allah wadai da saka al’ummar Gaza a cikin yunwa da kuma ci gaba da aiwatar da  kashe-kashen da Isra’ila ke yi, da nufin tilasta wa al’ummar Palasdinu kauracewa gidajensu da yankunansu . Masu zanga-zangar sun kuma yi kira da a rufe ofishin jakadancin Amurka da ke Aljeriya, saboda rawar da Amurka ta take takawa wajen mara wa Isra’ila baya ga laifukan Isra’ila a Gaza.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: zanga zangar

এছাড়াও পড়ুন:

Adadin Falasdinawan da Isra’ila take kashewa a Gaza yanzu ya haura 60,000

A ci gaba da hare-haren da dakarun Isra’ila ke kai wa a Zirin Gaza, yanzu adadin Falasdinawan da suka kashe ya kai 60,034.

A cewar wasu alkaluma daga Ma’aikatar Lafiya ta Gaza, baya ga wannan, adadin wadanda aka raunata kuma a yanzu sun haura 145,870.

Ma’aikatar ta kuma ce har yanzu ana zargin akwai mutanen kuma da ke karkashin baraguzan gine-ginen da aka rusa, wadanda ba za a iya ciro su daga ciki ba.

Fiye da kaso daya cikin uku na mutanen yankin na shafe kwanaki ba su ci abinci ba, kamar yadda wani rahoton samar da abinci mai lakabin IPC na Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar.

Rahoton ya ce ana samun karin hujjoji da ke nuna ana fama da yunwa da karancin abinci da kuma karuwar mace-mace masu alaka da yunwa a yankin da sama da mutum miliyan biyu da dubu dari daya ke rayuwa a cikinsa.

Hukumomi daban-daban na Majalisar Dinkin Duniya dai sun yi gargadin cewa ana fama da matsananciyar yunwar da aka kirkira da gangan a Gaza, inda a iya wannan watan, rahotanni suka tabbatar da mutuwar mutum 63, dalilin yunwar.

Hukumomin dai sun dora wa Isra’ila duk alhakin matsalolin, kasancewar ita ta yi wa yankin kawanya ta kuma hana a shigar da kayan agaji.

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya ce: “Abubuwa ne ga su nan a Zahiri, ba a boye suke ba. Falasdinawan da suke Gaza na cikin mawuyacin hali da tsananin bukatar agaji.

“Wannan ba wai gargadi muke yi ba. Gaskiya ce ga ta nan karara. Dole kayan agaji su ci gaba da kwarara. Abinci, ruwan sha, magunguna da man fetur dole su ci gaba da shiga ba tare da kowanne irin tarnaki ba,” in ji Guterres.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tallafin matar Tinubu na N1bn ga ’yan gudun hijirar Binuwai ya bar baya da kura
  • Majalisar Dattawa Ta Yi Allah-wadai Da Zanga-zangar Ƙin Jinin ’Yan Nijeriya A Ghana
  • Adadin Falasdinawan da Isra’ila take kashewa a Gaza yanzu ya haura 60,000
  • Kwamandan NDA Ya Bukaci Dalibai Su Dage da Karatu a Taron FGC Malali
  • Amincewa Da Kasar Falasɗinu: Birtaniya Ta Gindaya Wa Isra’ila Sharuɗɗa
  • An Fitar Da Kudaden Farfado Da Sassan Birnin Beijing Da Bala’in Ambaliyar Ruwa Ya Shafa
  • Kasar Iran Ta Musanta Yin Katsalandan A Tattaunawar Neman Tsagaita Bude Wuta A Gaza
  • Kasar Faransa Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta’addancin Da Aka Kai Birnin Zahedan Na Kasar Iran
  • An fara shigar da kayan agaji a Gaza
  • Mutanen Sweida Na Kasar Siriya Suna Fama da Rashin Abinci da Ruwa