Illolin Da Manufar Haraji Kan Kayayyaki Ta Haifar A Kan Amerikawa
Published: 22nd, April 2025 GMT
Kamfanoni da masana’antun America da dama sun dakatar da harkokinsu, dubban mutane sun rasa aikin yi. Don haka wannan mataki bai haifar da sakamakon da Mr. Trump ke bukata ba, musamman idan aka yi la’akari da yadda kasuwar hannayen jari ta shiga cikin rudani, gami da hali na rashin tabbas da manoman America suka samu kansu biyo bayan maida martani da China tayi na ramuwar gayya.
Sabo da haka a nan za mu iya bugun gaba mu ce “Kwalliya bata biya kudin sabulu ba” a kan matakin da shugaba Trump ya dauka na sanya haraji akan kayayyakin da ake shiga da su America daga China da sauran kasashen duniya.
Tabbas Mr. Trump ya fahimci babban kuskuren da ya tafka na daukar wannan mataki na rashin sanin ya kamata. Watakila yana jin kunyar ya fito ya fadawa duniya cewa ya janye wannan mataki, shi ya sanya ya fake da cewa ya jinkirta ci gaba da aiwatar da harajin har zuwa kwanaki 90, ko da yake ya ce ban da China. Babu makawa nan ba da jimawa ba shugaba Trump zai lashe aman da ya yi, musamman idan talakawan America suka gaza jimrewa matsatsin tattalin arziki sakamakon hauhawar farashin da rashin aikin yi da sakamakon wannan mataki da Trump ya dauka. (Lawal Mamuda)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: wannan mataki
এছাড়াও পড়ুন:
Nazarin CGTN: Ana Kara Bayyana Rashin Gamsuwa Da Sabuwar Gwamnatin Amurka Daga Ciki Da Wajen Kasar
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp