Sharhi: Kalankuwar Kona Rayayyu Da Wuta A Gaza
Published: 20th, April 2025 GMT
Sojojin mamayar HKI sun fara aiwatar da wani sabon kisa ta hanyar amfani da sabon salo akan Falasdinawa. Kai kace tsawon watanni 18 da su ka dauka suna amfani da makamai mabanbanta wajen kashe mutanen Gaza, bai isha sun cimma manufofin da su ka Sanya a gaba.
Sabon salon kisa wanda ya yi kama da “Kalankuwar Masu Cin naman mutum” bayan sun soya shi, shi ne abinda yake faruwa.
Isra’ila ta kai hari da jirgin yakin maras matuki na kunar bakin wake akan sansanonin ‘yan hijira da su ka yi dandazo a wuri daya. Iyalan Abur-Rus ne wannan jirgin kunar bakin waken ya fada a kansu ya kashe da dama daga cikinsu ta hanyar kona su da ransu. Mutane 20 ne su ka kone kurmus a cikin wadannan iyalan na Abu-Rus.
A daidai lokacin da daruruwan mazauna wannan sansanin ‘yan hijirar su ka taru domin su kashe wutar da harshenta ke toroko da tashi sama, jikin iyalan Rus yana ci gaba da konewa har su ka yi shahada ba tare da an iya ceto su ba.
Bayan da wuta ta lafa, sauran danginsu da su ka saura da su ka zo daga nesa, sun dauki sa’oi ba tare da sun iya tantance wane da wane ba.
Wannan salon kisa na kone Falasdinawa da ransu, bai tsaya a cikin iyalan Abur-Rus ba, Isra’ila ta sake aike wa da wani jirgin saman maras matuki na kunar bakin wake zuwa wani sansanin ‘yan hijirar. Wannan karon a unguwar “Razana” dake Beit-Lahiya a Arewacin zirin Gaza. Shi ma jirgin kunar bakin waken ya fada kan hemar iyalai guda da su ka kunshi Uba, Uwa, da ‘ya’yansu 4 tare da kone su kurmus.
Kafin akai abinda ya saura na gangar jikin shahidai zuwa asibitin “Indonesia” dake Arewacin Gaza, wani jirgin sama maras matuki na kunar bakin wake, ya fada akan hemar wasu iyalan a sansanin ‘yan hijira na Jabaliya. A wannan karon iyalan “Asliyyah’ ya fada wa, ya yi sanadiyyar shahadarsu, su 7 baki daya. Sun kuwa kunshi kananan yara 5 da mahaifansu.
Da gari ya waye, mutanen sansanin ‘yan hijira na Jabaliya sun tashi da wani kisan kiyashin akan makarantar Ayyubiyyah, dake karkashin hukumar Agaji. Wani jirgin maras matuki na ‘yan mamaya ya kai harin kunar bakin wake akan wannan makaranta a daya daga cikin dakuna, da ya yi sanadiyyar shahadar ‘yan hijira 6 da kuma jikkatar wasu gwammai.
**
A daidai wannan lokacin da HKI take shan jinin Falasdinawa ta hanyar kona su a raye, jiragen yakinta suna kai wasu hare-haren a gidan iyalan Najjar dake Jabaliya. An kuwa sami shahidai 3. Haka nan kuma sun kai wasu hare-haren a wata gona a garin Khan-Yunus da ya yi sanadiyyar shahadar mutane 2.
Su ma manyan bindigogin HKI suna ci gaba da kai nasu hare-haren babu kakkautawa a sassa daban-daban na Gaza,musamman a unguwanni da suke gabashin birnin Gaza, da su ka hada ‘ al-tuffah’ shjaiyyah, da Sha’af da Beit Hanun.
Bai zama abin mamaki ba da hukumar lafiya ta duniya ( W.H.O) ta siffata Gaza da cewa ta zama “babbar makabarta”. Ta kuma kara da cewa; “Isra’ila tana kai wa hemomin ‘yan hijira hare-hare cikin sani, da kuma manufa.” Haka nan kuma hukumar ta ce; “Babu wani wuri wanda yake da aminci a cikin fadin Gaza”.Sannan ta kara da cewa; An hana ta shigar da kayan agaji na magunguna da sauran kayan aiki na likitanci saboda tarnakin da Isra’ila ta gindaya. Ta kuma Karkare da cewa; “Rashin abinci mai gina jiki a Gaza ta kai koli.”
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kunar bakin wake maras matuki na Isra ila ta
এছাড়াও পড়ুন:
Yaƙin Gaza: Hamas da Isra’ila sun fara sakin fursunoni
A safiyar Litinin ɗin nan ƙungiyar Hamas ta saki rukunin farko na ’yan ƙasar Isra’ila bakwai da ta yi garkuwa da su a Zirin Gaza.
A ɗaya ɓangaren kuma Falsɗinawa sun yi cincirindo a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan domin tarbar ’yan uwansu kimanin 2,000 da Isra’ila za ta sako.
Tuni jami’an kungiyar agaji ta Red Cross suka shiga gidan yarin Wada a safiyar domin ɗaukar wani fursuna Bafalasdine da za fitar, wanda ke fama da rashin lafiya.
Hamas ta mika su ne ga kungiyar Red Cross a Gaza a yayin da ake da ran sako wasu ƙarin mutum 13 na gaba a Litinin ɗin nanm a cewar hukumomin Isra’ila.
Wannan na faruwa ne a yayin da Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya taka muhimmiyar rawa a sulhun, yake ziyara a ƙasar Isra’ilan a safiyar Litinin.
Zaɓen Kamaru: Tchiroma Bakary na da kwarin gwiwa a yayin da ake jiran sakamako Afuwar Tinubu za ta buɗe hanyar ci gaba da aikata miyagun laifuka — AtikuWannan na zuwa ne bayan yarjejeniyar zaman lafiyar da ɓangarorin biyu suka sanya hannu a kai a baya-bayan nan.
A bangare guda kuma Falsɗinawa sun yi cincirindo a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan domin tarbar ’yan uwansu kimanin 2,000 da Isra’ila za ta sako, a matsayin ɓangarenta na musayar fursunonin yaƙin.
Ma’aikatar Harkokin Gida ta Isara’ila ta fitar da jerin sunayen mutanen da aka saki da shekarunsu:
Eitan Abraham Mor, 25 Gali Berman, 28 Ziv Berman, 28 Omri Miran, 48 Alon Ohel, 24 Guy Gilboa-Dalal, 24 Matan Angrest, 22Na gaba ake da ran muka su ga iyalansu a wani sansanin soji a Kudancin Isra’ila.
A ɗaya bangaren kuma kungiyar kula da Fursunoni ta Palastinu ta fitar da jerin sunayen mutane 1,718 da Isra’ila za ta sako.