Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke ziyarar aiki a Vietnam, shugaban CMG Shen Haixiong, ya kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa da shugaban gidan radiyon Vietnam Nguyen Thanh Lam, da shugaban gidan rediyon na Voice of Vietnam Do Tien Sy, kana da shugaban kwalejin yada labarai da fadakarwa na Vietnam Pham Minh Son, a gaban shugabannin kasashen biyu wato Xi Jinping da Tô Lâm.

(Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Majalisar Dattawan Akpabio ya Nemi Sanata Natasha ta Biya Shi Diyyar Biliyan 200

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio ya shigar da Sanata Natasha Akpoti ƙara a kotu kan zargin ɓata masa suna yana mai neman ta biya shi diyyar naira biliyan 200.

Sanata Natasha mai wakiltar jihar Kogi ta tabbatar da karɓar sammacin a shafukanta na sada zumunta, inda ta nuna jin daɗinta tana mai cewa ta samu damar bayyana hujjojinta kan zargin yunƙurin lalata da ta zarge shi da yi a baya.

“Yau 5 ga watan Disamban 2025, na karɓi sabon sammacin kotu kan ƙarar diyya ta naira biliyan 200 da Sanata Godswill Akpabio ya kai ni game da ɓata masa suna da zargin lalata,” a cewar Natasha.

“Na yi farin ciki da Sanata Akpabio ya taso da wannan batu saboda kwamatin ɗa’a na majalisa ya ƙi amincewa ya saurare ni kan batun sakamakon matar Akpabio ta shigar da ni ƙara a kotu.”

A watan Fabrairun 2025 ne Natasha ta zargi Akpabio da neman yin lalata da ita bayan rikicin da ya ɓarke a tsakaninsu, wanda ya kai ga dakatar da ita daga zaman majalisar na tsawon wata shida.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima Ya Isa Abidjan Wajen Rantsar da Shugaba Ouattara
  • Benin : Har yanzu Shugaba Patrice Talon ne a kan mulkin_fadar shugaban kasa
  • Fadar Shugaban Kasar Benin ta ce Har Yanzu Talon Ne a Kan Mulki
  •   Qatar Tayi Gargardi Game Da Gakiyar Yarjejeniyar Gaza Matukar Isra’ila Bata Janye Ba
  • Mutum 3 sun mutum yayin haƙar rijiya a Kano
  • Shugaban Majalisar Dattawan Akpabio ya Nemi Sanata Natasha ta Biya Shi Diyyar Biliyan 200
  • Amurka ta Faɗaɗa Jerin ƙasashen Afrika Da ta Sanya wa Takunkumin Visa
  • Yaƙin M23 Ya ci Gaba a Congo Duk da Sulhu da Rwanda
  • Iran da Rasha sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna guda 20, kwangilolin haɗin gwiwa na fasaha guda biyar
  • ’Yan sanda sun kama tsohon shugaban PCACC, Muhuyi Rimin Gado a Kano