NAJERIYA A YAU: Dalilan Rikice-Rikice A Jihar Filato
Published: 15th, April 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A yanzu haka, al’ummar Filato na cikin fargaba da tashin hankali sakamakon jerin hare-haren da suka afku a wasu sassan jihar, inda daruruwan mutane suka rasa rayukansu, wasu kuma suka tsere daga muhallansu.
Ko mene ne dalilin sake dawowar rikice-rikicen da suka dabaibaye yankin da ake ganin an fara samun zaman lafiya?
NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar Borno DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan rikice rikicen Jihar Filato da dalilan aukuwarsu.
Domin sauke shirin, latsa nan: https://www.buzzsprout.com/1822045/episodes/16978635-dalilan-rikice-rikice-a-jihar-filato.mp3?download=true
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Filato
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnonin Arewa Za Su Zuba Biliyoyin Naira Don Yaki da Matsalar Tsaro
Daga Aliyu Muraki
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya ce gwamnonin Arewa sun amince su sayi na’urorin zamani na tsaro da kuma daukar matasa aiki don tallafawa ayyukan tsaro domin magance matsalolin rashin tsaro a yankin.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar.
Gwamna Abdullahi Sule, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Arewa ta Tsakiya, ya ce an cimma wannan matsaya ce a taron gwamnonin Arewa da aka yi a Kaduna kwanan nan.
A cewarsa, gwamnonin Arewa sun amince cewa kowace jiha za ta rika bada gudummawar Naira Biliyan Daya a kowane wata na tsawon shekara guda domin samar da kudin da zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro a yankin.
Ya ce kwamitin gwamnonin Arewa zai gina sakatariyarsa a Kaduna, inda gwamnonin Arewa goma sha tara suka bayar da Naira Miliyan Dari Dari na tsawon shekara guda.
Gwamna Abdullahi Sule ya kuma yi karin bayani kan dakatar da ayyukan hakar ma’adinai a jihar Nasarawa, inda ya bayyana cewa wannan dakatarwar ba haramta dukkan ayyukan hakar ma’adinai na tsawon watanni shida ba ce, an dakatar da bayar da sabbin lasisi ne, har sai an kammala tantance sahihan masu hakar ma’adinai.
Manufar tantancewar ita ce gano masu hakar ma’adinai na gaskiya da kawar da masu hakar ma’adinai na fasa-kwauri wadanda ba sa kawo kudaden shiga ga jihar, tare da haifar da matsalolin tsaro.
Gwamnan ya bayyana cewa kasancewar masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a jihar ta zama mafakar ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro, wanda hakan ya sa aka bukaci tsauraran dokoki da ingantaccen tsari.