Babban Daraktan Hukumar IAEA, Zai Ziyarci Iran ranar Laraba
Published: 14th, April 2025 GMT
Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya zai ziyarci Tehran a ranar Laraba mai zuwa.
Ziyarar ta Grossi na zuwa ne gabanin sabuwar tattaunawar da za’ayi tsakanin Iran da Amurka a ranar Asabar mai zuwa kan batun shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin kasa da kasa Kazem Gharibabadi ya ce shugaban hukumar ta IAEA Rafael Grossi zai ziyarci Tehran a ranar Laraba.
Gharibabadi ya bayyana cewa, babban daraktan hukumar ta IAEA, zai gana da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran (AEOI) Mohammad Eslami.
Ya kara da cewa “ziyarar na cikin tsarin ci gaba da hulda da hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu.”
Ziyarar ta shugaban hukumar ta IAEA za ta zo ne a daidai lokacin da Iran da Amurka ke shirin gudanar da tattaunawar ta biyu, wanda Oman ta shiga tsakani a ranar Asabar data gabata.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya naɗa Janar Christopher Musa sabon Ministan Tsaron Nijeriya
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa tsohon babban hafsan tsaron, Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaron Nijeriya
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ranar Talata.
An yi garkuwa da manoma 11 a Kudancin Kaduna Mutane 9,854 na ɗauke da cutar AIDS a YobeSanarwar ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio wasiƙar sanar da shi sabon naɗin da ya yi.
Naɗin Janar Musa na zuwa ne kwana guda bayan murabus ɗin Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya sauka daga muƙaminsa ranar Litinin saboda dalilai na rashin lafiya.
Aminiya ta ruwaito cewa a jiya Litinin ce Janar Musa ya yi wata ganawar sirri da Shugaba Tinubu, sa’o’i kaɗan gabanin sanar da murabus ɗin Mohammed Badaru.
Musa wanda zai cika shekara 58 a ranar 25 ga Disamba, ya yi aiki a matsayin Babban Hafsan Tsaro daga 2023 har zuwa Oktoban 2025 lokacin da Shugaban Kasa ya sauke shi daga muƙamin a watan Oktoba, bayan wani yunkurin juyin mulki da aka yi.