Rundunar ‘yansandan jihar Yobe ta kama wasu mutane biyu da ake zargin barayin wayar wutar lantarki ne a Damaturu babban birnin jihar. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa, rundunar ‘yansanda ta Karasuwa ce ta kama wadanda ake zargin – Yahaya Mustapha, 28, da Bello Yakubu, 38, da misalin karfe 1:00 na rana a ranar 12 ga watan Afrilun 2025.

‘Yansanda Sun Gano Haramtaccen Wurin Haɗa Makamai A Kano Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutum Ɗaya A Bauchi, Wasu Sun Jikkata Abdulkarim ya ce, wadanda ake zargin sun fito ne daga unguwar Takari da ke karamar hukumar Gashua Bade a jihar, an kama su ne da manyan igiyoyin wutar lantarki a kauyen Waro da ke karamar hukumar Karasuwa. A cewar sanarwar, an kama wadanda ake zargin ne a lokacin da suke loda igiyoyin a kan keke-napep mai kafa uku. Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Emmanuel Ado ya jaddada kudirin rundunar na yaki da masu aikata miyagun laifuka da barnata dukiyoyin jama’a, inda ya bukaci jama’a da su sanya ido tare da kai rahoton duk wasu zarge-zarge ko wasu mutane da ke shirin barnata kadarorin jama’a. Ya kuma yabawa ‘yan jihar bisa yadda suke bayar da sahihan bayanai, wanda hakan ya taimaka wajen bunkasa kokarin rundunar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: da ake zargin

এছাড়াও পড়ুন:

Nakiya ta hallaka yara 4 a Borno

Wata nakiya da ta fashe a garin Banki, da ke Ƙaramar Hukumar Bama, a Jihar Borno, ta yi sanadin mutuwar yara huɗu tare da jikkata wani yaro guda ɗaya.

Rundunar ’yan sandan jihar, ta tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Juma’a.

Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas Ranar Sabuwar Shekara za mu rufe duk na’urar POS mara rajista —Gwamnati

Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 12:40 na rana a bayan tashar motar Banki da ke yankin Wajari.

Wani mazaunin garin, Babagana Mohammed, ya kai rahoton fashewar nakiyar da misalin ƙarfe 1 na rana, wanda hakan ya sa aka tura jami’an tsaro zuwa yankin.

DPO na Banki tare da ƙwararrun sashen cire bam, sun killace wajen domin kare jama’a da kuma fara bincike.

An gano cewa wani yaro mai shekaru 12, Mustapha Tijja, ya samu munanan rauni, kuma an kai shi asibitin FHI 360 da ke Banki, inda ake kula da shi.

Rahotanni sun nuna cewa yaron da ya tsira da ransa, yana tare da abokansa huɗu a bayan tashar motar.

Sun samu wani abun fashewa da ake zargin ajiye shi aka yi a wajen, wanda ya fashe yayin da suke wasa da shi.

Yaran da suka rasu sun haɗa da Awana Mustapha mai shekaru 15, Malum Modu mai shekaru 14, Lawan Ibrahim mai shekaru 12 da Modu Abacha mai shekaru 12

Rundunar ’yan sandan jihar, ta ce al’amura sun daidaita a yankin, yayin da a gefe guda ta ke ci gaba da bincike.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar, CP Naziru Abdulmajid, ya bayyana alhininsa kan faruwar lamarin, tare da bayyana cewa rundunar tana gudanar da bincike.

Ya gargaɗi jama’a cewa: “A guji taɓa ko wasa da duk wani abu da ba a saba gani ba. Duk abun da ake zargi, a gaggauta sanar da jami’an tsaro.”

Rundunar ta bayyana lambobin kiran gaggawa da jama’a za su yi amfani da su don kai rahoto: 0806 807 5581 da 0802 347 3293.

Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce rundunar za ta ci gaba da aiki tuƙuru wajen tabbatar da tsaro da hana irin waɗannan abubuwan faruwa a gaba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dalilin da ya sa ’yan sanda suka kama ni — Muhuyi
  • Nakiya ta hallaka yara 4 a Borno
  • Shugaban Majalisar Dattawan Akpabio ya Nemi Sanata Natasha ta Biya Shi Diyyar Biliyan 200
  • Fyaɗe ga ’yar shekara 12 ya ja wa matashi ɗaurin rai-da-rai a Yobe
  • Yan Sanda Sun Kama Muhuyi Magaji, Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci a Kano
  • Jami’an tsaro sun kama masu garkuwa da mutane 7 a Gombe
  • DSS ta kama likitan da ke duba ’yan bindiga a dazukan Kwara
  • Najeriya: Tinubu Ya Nada Wasu Karin Jakadu 65, Sanatoci Da Tsoffin Gwamnoni Na Daga Cikinsu
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar da Wutar Lantarki a Yankunan Kananan Hukumomin Jihar
  • ’Yan sandan Borno sun kama matashin da ake zargi da kashe makwabciyarsa da wuƙa