Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Siyo Tan Tan 360 Ga Manoma
Published: 14th, April 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Jigawa ta siyo tan tan guda 360 domin tallafawa manoma don ci gaba da habbaka harkokin noma a Jihar.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin kaddamar da shirin noman rani na shinkafa a kauyen Jura dake Karamar Hukumar Auyo.
Ya yi bayanin cewar, gwamnatin ta kuma siyo injin girbin shinkafa guda 70 da sauran kayayyakin noma domin tallafawa manoman shinkafa.
A don haka, Gwamna Umar Namadi ya yi gargadin hukunta duk wanda aka samu ya karkatar da kayayyakin aikin gona da gwamnatin ta samarwa manoman jihar.
Yana mai cewar, fiye da manoma dubu hamsin da biyar ne za su amfana da shirin, wanda wani bangare ne na kokarin gwamnati na bunkasa aikin gona da wadata kasa da abinci.
Kazalika, Gwamnan ya kaddamar da rabon Babura 300 ga malaman gona domin wayar da kan manoma.
Ya kuma bayyana irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu wajen bunkasa harkokin noma.
A cewar sa, wannan shirin yana daya daga cikin muhimman manufofi 12 da gwamnatinsa ta sanya a gaba, wadanda suke daidai da manufofin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na samar da wadataccen abinci ga ‘yan Najeriya.
Namadi ya bayyana cewar, tallafawa harkar noma da samar da malamai a fannin gona na daga cikin manyan hanyoyin cimma burin gwamnati na wadatar abinci da habaka tattalin arziki.
Ya kuma yaba da hadin kai da goyon bayan da manoma ke bayarwa wajen aiwatar da irin wadannan shirye-shiryen da gwamnati ke bullowa da su.
Wakilinmu ya bamu rahoton cewar, kananan manoma za su samu rangwamen kashi 30 cikin 100, yayin matsakaita za su amfana da kashi 20, manyan manoma kuma za su samu kashi 10 akan kayayyakin da za su siya.
Kayayyakin da aka raba sun hada da injinan ban ruwa da takin zamani da magungunan kashe kwari da sauran su.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Karamar Hukumar Bubura Ta Kai Tallafin Kayayyakin Abinci Cibiyar Gyaran Hali
Daga Usman Mohammed Zaria
Majalisar Ƙaramar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa ta bayar da tallafin abinci ga fursunonin cibiyar gyaran hali ta Babura a matsayin wani ɓangare na ayyukan jin ƙai na majalisar.
Yayin ziyarar, Alhaji Hamisu Muhammad Garu ya bayyana cewa, wannan taimako ya biyo bayan lura da bukatun fursunonin yayin da ya kai ziyara ta duba cibiyar a baya.
A cewarsa, manufar bayar da tallafin ita ce don tallafa musu wajen kyautata rayuwarsu da kuma karfafa musu gwiwa su zama mutane nagari bayan sun fito daga gidan gyaran hali.
A nasa jawabin, jami’in da ke kula da cibiyar gyaran hali ta Babura, ASP Muhammad Ali, ya gode wa shugaban ƙaramar hukumar bisa wannan karamci, yana mai cewa taimakon ya zo ne a lokacin da ake matuƙar buƙata.
A yayin hudubarsa ga fursunonin, Babban Limamin Babura, Imam Salisu Aliyu, ya shawarce su da su nemi gafarar Allah, su kuma kara kusanci gare Shi, tare da rungumar canji mai kyau.
Kayan tallafin da aka bayar sun haɗa da buhunan masara, gero, shinkafa, garin rogo, man gyada, sinadaran dandano, gidan sauro da maganin kwari.
Manyan baƙin da suka raka shugaban ƙaramar hukumar a lokacin ziyarar sun haɗa da Hakimin Babura, Sarkin Bai Ringim, Alhaji Muhammad Nata’ala Mustapha, jami’in ‘yan sanda mai kula da yankin, CSP Abdu Jinjiri, da jami’in Hukumar Tsaro ta Civil Defence, CSC Sunusi Usman Chamo, da sauransu.