Shugaban Hukumar Makamashin Nukliya Ta Kasar Iran Ya Ce Dukka Ayyukan Makamashin Nukliya A Cikin Gida Suna Tafiya Da Karfinsu
Published: 12th, April 2025 GMT
Shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran ya ce kasashen wamma suna son kebe kansu da fasahar nukliya a tsakaninsu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Muhammad Eslamu shugaban hukumar AEOI yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa kamfanin makamashin nukliya na kasar Iran ya kafa a kasar Iran kuma ba wanda ya isa ya kauda shi.
Ya ce JMI ta wuce wasu kasashen yamma a ayyuka da kuma sani da sarrafa makamashin Uranium, wanda ya tada hankalin wadannan kasashe, kuma suke sun han awasu kasashen duniya bin sawun kasar Iran na zama yentattu a wannan fage.
Islami ya kara da cewa kamfanin makamashin nukliya na kasar Iran ya kai wani matsayinda yana taiamakawa sauran kamfanoni na cikin gida ba tare da bukatar dogaro da kwararru ko kuma taimakon kasashen waje ba. Ya ce a halin yanzu iran na samar da wutan lantarki mai karfin magewats 20,000 tare da Makamashin Nukliya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: makamashin nukliya na kasar Iran ya
এছাড়াও পড়ুন:
Mutum 6 sun jikkata a rikici manoma da makiyaya a Jigawa
Aƙalla mutum shida ne suka jikkata bayan da wani rikici ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a ƙauyen Kangire da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa.
Ishak Ibrahim Fanini, mai taimaka wa shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu, Muhammad Uba, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Sojoji sun ceto mutum 7 da ’yan bindiga suka sace a Kano DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed kan zargin kalaman tayar da hankaliA cewarsa, an zargi makiyaya da shigar da dabbobinsu cikin gonakinsu wasu manoma.
Wannan ya haddasa faɗa tsakanin manoma da makiyayan.
Ya ƙara da cewa shugaban Ƙaramar Hukumar ya gudanar da taron sulhu tsakanin ɓangarorin biyu, inda ya gargaɗi su kan tayar da rikici a yankin.
Wannan sabon rikici ya faru makonni kaɗan bayan irin wannan ya auku a watan Oktoba, inda mutane uku suka mutu sakamakon rikicin manoma da makiyaya a Ƙaramar Hukumar Birniwa.
Rikicin manoma da makiyaya ya zama babban matsala a Jigawa da sauran yankunan Arewa.
Masana sun ce wannan rikici na yawan faruwa ne saboda matsalolin muhalli, tsadar rayuwa.
Sun bayyana cewa sauyin yanayi da yaɗuwar hamada a Arewacin Sahel sun tilasta wa makiyaya da dama yin ƙaura don ciyar da dabbobnsu.
Sai dai shigarsu yankunan da ake noma a Jigawa, ya haifar da rikici saboda lalata gonaki.