Sin Za Ta Kara Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar Zuwa 125%
Published: 12th, April 2025 GMT
Duba da cewa, ko a yanzu ma bisa harajin da Amurka ta kakaba, kayayyakin Amurka ba za su iya samun karbuwa a kasuwannin kasar Sin ba, idan har Amurka ta kara yawan haraji kan hajojin Sin, bangaren Sin zai yi watsi da hakan.
Sai dai kuma, idan Amurka ta nace wajen neman illata moriyar kasar Sin, Sin din za ta aiwatar da matakan ramuwa, tare da tunkarar wannan yaki har karshensa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kamfanonin Sin Sun Kera Tare Da Sayar Da Motoci Sama Da Miliyan 31 Tsakanin Janairu Zuwa Nuwamban Bana
Masana’antun kirar motoci na kasar Sin, sun samar tare da sayar da motocin da suka haura miliyan 31 cikin watanni 11 na farkon shekarar bana, wanda hakan ke shaida irin ci gaban da suka samu ta fuskar fitar da hajoji.
A cewar wasu alkaluma daga kungiyar kamfanonin kirar motoci na kasar Sin, tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamban bana, adadin kirar motoci a Sin ya karu da kaso 11.9 bisa dari kan mizanin shekara, zuwa sama da motoci miliyan 31.23, yayin da alkaluman sayar da su ya karu zuwa kusan miliyan 31.13, wanda ya shaida karuwar kaso 11.4 bisa dari kan mizanin shekara.
Kazalika, alkaluman na watanni 11, sun shaida yadda yawan kirar motoci masu aiki da sabbin makamashi a kasar ya karu zuwa miliyan 14.907, karuwar da ta kai ta kaso 31.4 bisa dari, yayin da alkaluman sayar da su ya kai miliyan 14.78, wato karuwar kaso 31.2 bisa dari kan mizanin shekara. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA