Ba kamar kayayyakin manyan kamfanoni irin su Ajinomoto, Bedan wadanda aka zuba su a cikin kwali, ana sayar da su cikin lafiyayyen mazubi kuma NAFDAC ta amince da su ba, wadannan danyun kaya ne da ba su da wata alama.

Babban abin ban tsoro shi ne ba za a iya gano masana’antunsu don bincikar sahihancinsu ba.

Da alama a yankin Arewacin Nijeriya din ake yin su amma an gaza gano hakan ko kuma an gano amma wa’alla saboda yawan bukatu an kasa dakilewa.

Bincike ya nuna cewa a kasuwar Singer da Abubakar Rimi da ke Kano, ana sayar da buhu mai nauyin kilo giram 25 na wannan sinadari kan Naira 45,000, wanda ke bai wa ‘yan kasuwa damar sayar da su a kanana wurare, ciki har da auna shi da abin da mazauna yankin ke kira ‘mudu’.

A manyan kasuwannin Kaduna da Maiduguri, kasuwar Sabon Gari da ke Sokoto, ana sayar da buhu mai nauyin kilogiram 25 a tsakanin Naira 46,000 zuwa Naira 50,000.

A cikin jaka mai nauyin kilo giram 25, ana iya samun kamar mudu ‘10 zuwa 15 ‘.

Abokan ciniki, ba tare da la’akari da hadarin dake tattare da kiwon lafiya ba, sun fi son wannan haramtaccen samfuri saboda yawan abin da za su samu daga mudu da kuma saukin yin almundahana ta hanyar cakuda shi da gishiri don kara yawansa da samun riba.

A kwanakin baya ne hukumar ta NAFDAC ta rufe wani dakin ajiyar kaya na kamfanin ‘DEE-LITE IMPED Distribution Co. Ltd’ da ke Jihar Sokoto, bayan ta gano wani adadi mai yawa na kayan abinci marasa rajista da suka hada da buhu 5,347 na MSG.

Rumbun ajiyar da ke kan titin Coca-Cola, daura da Western Bypass a Sokoto, an gano ya saba wa ka’idojin hukumar NAFDAC. A cewar hukumar ta NAFDAC, kamfanin ya shigo da haramtaccen samfurin MSG babu izini a karkashin takardar izinin sarrafawa amma an same shi yana sayar da samfurin kai tsaye, wanda haramun ne kuma yana da hadari ga lafiyar dan’Adam.

Wani masani kan harkokin kiwon lafiya da ke zaune a Gombe, Dokta Abdullahi Guruji ya ce ya kamata masu amfani da su su yi hattara da abubuwan da suke amfani da su domin gujewa duk wata matsala a fannin lafiya. Guruji ya ce ya zama wajibi masu amfani da su daina sadaukar da lafiyarsu a kan burin farashin kayan abinci masu arha.

A cewarsa, bai kamata a ce alhakin kare lafiyar mutum ya takaita ga hukumar NAFDAC da SON da sauran hukumomi kadai ba. Ya bukaci kowane dan Nijeriya da ya kula da kansa da kuma sauran ‘yan kasarsa domin kaucewa wannan hatsarin da ke kunno kai a harkar lafiya.

A yayin da yake kira ga masu sayar da abinci da su taka rawar gani a wannan fanni, ya bukace su da su kula da lafiyar kwastomominsu ta hanyar yin amfani da ingantattun kayayyakin dafa abinci.

Sai dai kwarare a fannin lafiyar ya dora wa hukumar ta NAFDAC alhakin kara kaimi a fannin tabbatar da doka da oda inda ya ce yin hakan zai dakile ayyukan marasa kishin Nijeriya da suke jajircewa wajen cutar da ‘yan Nijeriya.

“Duk lokacin da muka ziyarci kasuwa, za mu ceci mutane da yawa daga matsalolin kiwon lafiya ta hanyar rufe shagunan masu sayar da monosodium glutamate, masu sayar da magungunan jabu / marasa inganci, da masu siyar da abubuwan sha masu dandano, na cikin kwalba a cikin sauran abubuwan da ke zama abin sha,” in ji shi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Arewa Hadari Kasuwanni Lafiya ana sayar da

এছাড়াও পড়ুন:

Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya

Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce Gwamnatin Tarayya ta buɗe kofofin tattaunawa da ƙasashen duniya, ciki har da Amurka, dangane da barazanar kasar ta kaddamar da yaki a Najeriya.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa bayan taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta, Ministan ya ce gwamnatinsu ba ta son ƙara yin yamadidi da maganar.

An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8 Kwalara ta kashe mutum 10 a Ƙaramar Hukumar Adamawa

“Babban nauyin da ke kanmu a matsayin gwamnati shi ne tabbatar da cewa gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da ɗaukar mataki a kan duk wata damuwa ta gaskiya da ke da alaƙa da tsaron ’yan ƙasa.

“Amma ba ma cikin yanayin firgici. Muna mayar da martani cikin natsuwa, hankali, da kuma la’akari da muradun ƙasarmu, tare da duba damuwar da ke cikin gida da waje dangane da halin da ake ciki. Amma zan sake jaddadawa, Najeriya ƙasa ce mai ba da ’yancin yin addinai,” in ji ministan.

Ya kuma ce gwamnati na mayar da martani kan waɗannan batutuwa ta hanyar kiyaye mutunci da darajar ƙasar, da kuma haɗin gwiwa da kowa, ciki har da ƙasashen duniya, don magance wannan matsala.

“Muna da iyakoki masu sauƙin shigowa, shi ya sa muke da fahimtar juna da makotanmu. Haka kuma muna da haɗin gwiwa da ƙasashen duniya, ciki har da Amurka, kuma Najeriya za ta ci gaba da tattaunawa. Mun fara magana da gwamnatin Amurka. Hanyoyin sadarwar mu a bude suke. Muna so a warware wannan matsala ta hanyar diflomasiyya.

“Baya ga siyasar lamarin, muna ɗaukar batun da muhimmanci. Amma ina so in ƙara jaddada cewa gwamnati, tun kafin abubuwan da suka faru a kwanakin baya, ta jajirce matuƙa wajen tabbatar da cewa Najeriya ƙasa ce amintacciya ga kowa.

“Shin akwai matsalolin tsaro a ƙasa? Eh, akwai. Shin ana kashe mutane a wasu sassan ƙasa? Eh. Amma shin gwamnati na yin wani abu don dakile hakan? Eh, tabbas akwai. Shin gwamnati na mayar da martani? Eh, tana yi. Amma ana yin hakan cikin cikakken hanyoyin da suka dace, tare da kiyaye daidaito da ake buƙata don fuskantar waɗannan matsaloli kai tsaye,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma
  • Ɗan shekara 2 ya rasu bayan faɗawa rijiya a Kano
  • An gano gawar wata mai shekara 96 a cikin masai
  • Harin bam a masallacin Juma’a ya jikkata sama da mutum 50 a Indonesia
  • An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano
  • Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya
  • Cin zarafin Wakilin NTA ya tada ƙura a Yobe
  • Kwalara ta kashe mutum 10 a Ƙaramar Hukumar Adamawa
  • Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa
  • Matan 500 Za Su Amfana da Gwajin Cutuka Kyauta a Jihar Gombe