’Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in FRSC a Benuwe
Published: 21st, March 2025 GMT
Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wani jami’in Hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) Nathaniel Terwanger Kumashe a ƙauyensa da ke ƙaramar hukumar Tarka a Jihar Benuwe.
An samu rahoton cewa wanda aka yi garkuwan ya taso ne daga Makurdi sansaninsa, domin halartar jana’izar ɗan uwansa da ya rasu a lokacin da aka ɗauke shi zuwa wani wuri da ba a san inda yake ba.
Wani kawun wanda aka yi garkuwan, tsohon mai baiwa gwamnan Jihar Benuwe shawara kan harkokin sufuri, Cif Yimam Aboh, ya shaidawa manema labarai a Makurdi ta wayar tarho cewa an ɗauke jami’in, Insfekta Kumashe a daren Laraba da misalin ƙarfe 10 na dare.
Ya ce, ’yan bindigar sun yi ta harbi don tsoratar da ’yan uwa da maƙwabta kafin su yi awon gaba da wanda suka yi garkuwan daga gidansu da ke Tse Aboh, Uchi-Mbakor a ƙaramar hukumar Tarka.
Ya kuma bayyana cewa, Kumashe ya koma gidansa ne bayan rasuwar ɗan uwansa wanda za a yi jana’izarsa a yau lokacin da masu garkuwar suka farwa gidan.
A halin da ake ciki, jami’ar hulɗa da jama’a ta Hukumar FRSC a Benuwe, Ngozi Ahula, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ƙara da cewa an kai rahoton lamarin ga ’yan sanda.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: garkuwa da mutane jihar Benue
এছাড়াও পড়ুন:
Akwai hannun ƙasashen waje a rashin tsaron Najeriya —Sheikh Gumi
Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Mahmud Abubakar Gumi, ya yi zargin cewa ƙasashen waje na taimaka wa ƙungiyoyin ’yan ta’adda Najeriya.
Sheikh Ahmad Gumi ya danganta ƙaruwar matsalar tsaro a Najeriya a baya-bayan nan da irin maganganun da ƙasashen waje suka riƙa yi a kai.
A yayin wata hira da BBC Hausa, malamin ya bayyana cewa yanayin taɓarɓarewar tsaro a baya-bayan nan ya nuna akwai alamun hannun ƙasashen waje a ciki.
Tsohon hafsan sojin, ya ce matsalar tsaro ta ragu a sassan ƙasar nan sai baya-bayan nan da ƙasashen waje suka fara magana a kai.
Ya bayyana cewa an samu aminci a hanyar Abuja zuwa Kaduna, wadda baya ta kasance tarkon mutuwa, amma sai kwanan nan matsalar ta fara dawowa bayan maganganun ƙasashen waje.
Ya ce manoma a yankin Birnin Gwari sun ci gaba harkokin nomansu, bayan samuwar zaman lafiya, abin da ya gare su a baya lokacin da ake ganiyar rashin tsaro.
“Akwai maganar da ƙasashen waje suka yi, kuma mun jima muna cewa ƙasashen waje ke taimak aa ’yan ta’adda da irin muggan makamai da suke amfani da su.
“Akwai attajirai da shugabannin ƙasashen waje da ke yin katsalandan ga harkokin wasu ƙasashe.”
Don haka ya ce ba abin mamaki ba ne samun ƙaruwar hare-haren ta’addanci da aka yi a Najeriya bayan maganganun ƙasashen waje a kan matsalar tsaro a ƙasar.
Kan matsayinsa game da tattaunawa da ’yan bindiga, ya ce: “Kowa ya san su. Amma abin da mutane ba sa magana a kai shi ne: me ya sa mutanen da muka taɓa rayuwa lafiya da su suka juya mana baya suka zama annoba a cikin al’umma? Akwai dalili.”
“Mutane biyu ne ba za a yi mamakin abin da suke yi ba: mahaukaci da jahili. Babu wani bayani da za ka yi musu da zai sa su fahimci cewa aikata laifi ba daidai ba ne.”
“Babu abin da suka sani face ɓarna. Amma wa zai yi musu nasiha su daina? Lokacin da muka yi ƙoƙarin kusantar su muka gaya musu cewa haramun ne sata, ƙwace dukiyar mutane haramun ne, yin garkuwa da mutane haramun ne, gwamnatin da ta gabata ba ta ba mu goyon baya ba.
“Da an ba da wannan goyon bayan, watakila da zuwa yanzu an warware wannan matsala.”
Sheikh Gumi ya yi gargaɗi cewa muddin ba a magance tushen matsalar ba, to akwai sauran rina a kaba.
Ya kuma ja hankali jama’a su fahimci cewa matakin yaki da ta’addanci da ya ɗauka, musamman neman sulhu da ’yan bindiga ba, ba ya nufin goyon bayan ayyukansu.
“Addininmu ya haramta zalunci; Duk abin da muke yi, muna yi ne domin Allah,” in ji shi.