An kori shugaban hukumar leken asiri ta cikin gidan Isra’ila
Published: 21st, March 2025 GMT
Gwamnatin Isra’ila ta sanar da korar shugaban hukumar liken asiri ta cikin gidan kasar Ronen Bar, wanda Firaministan kassar Benjamin Netanyahu ya ce bai gamsu da kwarewarsa ba hasali ma ba’a yarda da shi.
“Gwamnati baki daya ta amince da shawarar Firaminista Benjamin Netanyahu na kawo karshen wa’adin” Ronen Bar, wanda zai bar ofis idan aka nada magajinsa ye zuwa ranar 10 ga watan Afrilu, in ji ofishin Firayim Minista a cikin wata sanarwa.
Rashin gamsuwa da aikin na kokaren shugaban hukumar ta Shin-bet, ta fito fili a baya bayan bayan bayannan da suke fitowa game da harin kungiyar Hamas na ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
Ronen Bar, wanda aka nada a watan Oktoba 2021 na wa’adin shekaru biyar, ya tabbatar tun kafin yanke hukuncin cewa zai kare kansa a gaban “hukumomin da suka dace”.
A cikin wata wasika da ya aikewa jama’a da yammacin Alhamis, ya bayyana cewa dalilan da suka sa aka kore shi daga aiki, wanda Benjamin Netanyahu ya sanar a ranar Lahadi, ya dogara ne da “sha’awar kansa” da nufin “hana bincike kan al’amuran da suka shafi harin ranar 7 ga Oktoba da wasu muhimman batutuwa da Shin Bet ke bincikar su.”
Dama shugaban hukumar ya amince kwanan baya da gazawar hukumar da ayek jagoranta wajen hana harin na Hamas.
A cikin wata sanarwa da aka fitar kwanan baya, shugaban hukumar ta Shin Bet, Ronen Bar, ya amince da cewa, hukumar ta ” gaza a cikin aikinta” na dakile ayyukan Operation Al-Aqsa, tare da kutsawa manyan sansanonin Isra’ila bayan da sojoji da ‘yan sandan gwamnatin suka yi kaca-kaca da su, kuma y ace ya dauki nauyin gazawar a wuyansa.
Hukumar ta amince da gagarumin gibi a cikin tattara bayanan sirri da kuma dogaro da matakan kariya da ake da su, wanda ya haifar da rashin fahimtar kungiyar Hamas, tare da sauran kungiyoyin gwagwarmaya.
Wannan na zuwa ne kwanaki bayan wani “binciken cikin gida” ya nuna cewa, an gaza wajen dakile harin na Hamas.
Binciken da sojojin Isra’ila suka gudanar ya soki yadda gwamnatin kasar ke dogaro da bayanan sirri da kuma raina karfin Hamas, kura-kuran da suka haifar da mummunan sakamako ga gwamnatin Isra’ila.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: shugaban hukumar
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Nada Aisha Mujaddadi Sabuwar Shugabar Hukumar InvestJigawa
Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya amince da nadin Aisha Shehu Mujaddadi a matsayin shugabar Hukumar Kula da Zuba Jari ta Jihar Jigawa (InvestJigawa).
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar ga manema labarai.
Sanarwar ta ce “Aisha Mujaddadi ta samu digirinta na farko a fannin tattalin arziki a Jami’ar Maiduguri a shekarar 1996, ta kara inganta iliminta da samun digiri na biyu a fannin Gudanar da Kasuwanci (MBA) daga Jami’ar Bayero, Kano a shekarar 2011.“
Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa Aisha Mujaddadi ta samu gogewa na tsawon shekaru 19 a fannin aikin shawarwari na ci gaban kasa da kasa, inda ta yi aiki a kan muhimman ayyuka da shirye-shirye tare da Bankin Duniya, Ma’aikatar Harkokin Waje, Harkokin kungiyar kasashen renon Ingila da Ci Gaban Birtaniya (FCDO), da Tarayyar Turai (EU), wanda hakan ya bata kwarewar da ta dace da sabon mukaminta.
Ya kara da cewa, Aisha Mujaddadi ta kasance a cikin kwamitoci da dama a matakin jiha da na tarayya, kuma ta taba zama memba a kwamitin gudanarwa na Hukumar Tara Haraji ta Jihar Kaduna.
Sakataren Gwamnatin a jaddada cewa an yi nadin ne bisa cancanta, kwarewa da gaskiya, wanda ke nuna amincewar wannan gwamnati da kwarewar Aisha Mujaddadi.
Ya bayyana fatan cewa sabuwar Darakta Janar din za ta sauke nauyin da aka dora a kanta tare da kawo ci gaba mai ma’ana ga Jihar Jigawa.
Ya kara da cewa, nadin Aisha Shehu Mujaddadi a matsayin Darakta Janar na InvestJigawa ya fara aiki nan take.
Usman Muhammad Zaria