Rasha Za Ta Kara Yawan Alkamar Da Take Kai Wa Kasashen Afirka
Published: 15th, March 2025 GMT
Cibiyar da take fitar da amfanin gona zuwa waje ta kasar Rasha, ta sanar da cewa; a cikin shekarar 2024 an sami karuwar kayan abincin da take fitarwa zuwa wasu kasashen Afirka da kaso 19% da kudin da su ka hau da dala biliyan 7.
Wasu kasashen da Rashan za ta linka yawan alkamar da take aikewa su ne Moroko, Najeriya da kuma Kamaru.
Yawan alkamar da kasar Rashan za ta aike zuwa Moroko ta kai ton 124,000,a 2024 kuwa yawan alkamar da ta aikewa ita ton 54,000.
Ita kuwa kasar Najeriya yawan alkamar da Rashan ta aike mata ta tashi daga ton 48,000 zuwa ton 131,400.
Alama ce muhimmin kayan abincin da kasar Rasha take aike wa nahiyar Afirka. A shekarar 2024 da ta gabata ta kai wa nahiyar alkama da kudinta su ka kai dala biliyan 7.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Olisa Metuh ya sauya sheƙa zuwa APC, ya ce PDP ta manta da shi
Tsohon mai magana da yawun jam’iyyar PDP na ƙasa, Olisa Metuh, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Ya ce ya yanke wannan shawara ne saboda PDP ta kasa goyon bayansa lokacin da yake cikin matsaloli.
Sojoji sun ceto ’yan mata 12 da ISWAP suka sace a Borno ’Yan bindiga sun sace amarya da ƙawenta 14 a SakkwatoMetuh, ya daina shiga harkokin siyasa kusan shekaru uku da suka wuce, ya amma ya dawo siyasa ne ta hanyar sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki.
Ya bayyana hakan ne a lokacin bikin cikarsa shekaru 60 a duniya, wanda ya gudana a Abuja.
Manyan ’yan siyasa da dama sun halarci taron, ciki har da gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Anyim Pius Anyim, da tsoffin gwamnonin Abiya, Ebonyi da Imo.
Da yake magana da ’yan jarida bayan taron, Metuh, ya ce yana son ya taimaka wajen ci gaban Najeriya ta hanyar komawa APC.
Ya ce Najeriya na fuskantar ƙalubale, kuma yana son ya bayar da gudummawarsa a aikace.
Ya ce: “Lokacin da na shiga matsala, ban ga jam’iyyata ba. Na kasance a kotu tare da iyalina kawai.
“Amma Shugaba Tinubu, wanda nake suka a kai a kai, shi ne ya turo Femi Gbajabiamila ya zo ya duba ni ya kwantar min da hankali.”
Ya ce yana yi wa PDP fatan alheri, amma zai ci gaba da rayuwarsa ba tare da ita ba.
Haka kuma ya bayyana cewa har yanzu akwai jagorori masu ƙarfi a tsagin ’yan adawa, don haka Najeriya ba za ta zama ƙasa mai jam’iyya guda ɗaya ba.
Metuh, ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu ya sha yi masa tayin shiga APC, amma ya ƙi amincewa.
A cewarsa: “Shugaban ƙasa ya so na jam’iyyarsa tun 2015. Har bayan da na daina siyasa a 2022, ya sake gayyata ta, amma na ki. Yanzu da na koma siyasa, ina son na taimaka wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya.”