Jihohi 12 da za a fuskanci tsananin zafin rana — NiMet
Published: 11th, March 2025 GMT
Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya NiMet ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar a fuskanci tsananin zafin rana a wasu jihohin ƙasar na tsawon kwanaki huɗu.
Wata sanarwa da Nimet ta fitar ranar Litinin a Abuja, ta ce mutane su guji fita cikin tsananin zafi musamman daga karfe 12 na rana zuwa karfe 3.
Ainihin abin da ke kawo wa Manchester United koma baya ‘Yarjejeniyar sayar wa Matatar Dangote ɗanyen mai a farashin naira za ta ƙare a ƙarshen Maris’Hukumar ta ce mutane za su ji sauyin al’amura a tsawon lokacin da za a kwashe ana tsala zafin ranar.
Jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci ƙaruwar yanayi na zafin rana sun haɗa da Neja da Kwara da Oyo da Kogi da Nasarawa da kuma Benue.
Sauran sun haɗa da Enugu da Anambra da Abia da Ebonyi da Cross River da birnin tarayya Abuja.
NiMet ta ce wasu jihohin da ka iya fuskantar wannan barazana sun hada da Taraba da Adamawa da Filato da Kaduna da Zamfara da kuma Sakkwato.
Ta kuma shawarci al’umma da su riƙa shan isasshen ruwa a tsawon lokacin – su kuma yi amfani da fanka da na’urar sanyaya ɗaki da kuma zama a wurare masu inuwa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Zafin rana
এছাড়াও পড়ুন:
IAEA ta buƙaci Iran ta bayyana yawan makamashin nukiliyar da ta mallaka
Kwamitin hukumar hana yaɗuwar makamin nukiliya IAEA a Majalisar Dinkin Duniya, ya buƙaci ƙasar Iran da ta bayyana yawan makamashin nukiliyar da ta mallaka.
Wannan dai na zuwa ne bayan kwamitin ya amince da wani ƙuduri da zai tilasta wa Iran bayyana musu yawan makamashin nukiliyarta.
An yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai Kotu ta sami Nnamdi Kanu da laifukan ta’addanciA cewar sabon ƙudurin da ƙasashe 19 suka yi na’am da shi, dole Tehran ta bayar da kai bori ya hau ta hanyar sallama duk wasu bayanai gamsassu, da kuma ba wa ƙwararrun jami’an IAEA damar shiga wuraren da take gudanar da shirinta na bunƙasa makamashi.
Ƙudurin ya kuma ce dole ne Iran ta bayar da damar ziyartar tashoshinta na nukilya, ciki har da waɗanda aka kai wa hari lokacin yaƙi tsakaninta da Isra’ila a watan Yuni.
Ƙasashen Faransa da Birtaniya da Jamus da Amurka ne suka bijoro da ƙudurin wanda Rasha da China da kuma Jamhuriyyar Nijar suka hau kujerar naƙi wajen kaɗa ƙuri’a.
China da Rasha dai sun nuna fargaba kan abubuwan da ka iya biyowa baya, idan aka samar da sabon ƙudurin, wanda suka ce ka iya sa Iran ta bijire wa batun, duba da takun saƙar da aka fuskanta a baya-bayan nan a tsakanin jami’an hukumar IAEA da fadar mulki ta Tehran.