Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [3]
Published: 11th, March 2025 GMT
Wannan magana ta al-imam Ibnu Juzai tana bayani ne kan abubuwa huɗu da ke hana mutum bin Allah da kuma yadda za a magance kowanne daga cikinsu. Ga ƙarin haske akan haka:
1. Shaiɗan: Shaiɗan shi ne abokin gaban mutum na ƙoli tun daga haihuwarsa har mutuwarsa. A matsayinsa na maƙiyi, burinsa shi ne ya ɓatar da mutum daga bin Allah.
Maganin Shaiɗan: Babban maganin Shaiɗan shi ne neman tsari da kariya a kansa a wurin Allah, da sɓa masa, Wato mutum ya yi ƙoƙarin yin akasin abin da Shaiɗan ke umarta. Idan Shaiɗan yana kiran mutum zuwa ga zunubi, ya yi ƙoƙarin kaucewa.
2. Son Zuciya: Zuciyar mutum tana da buƙatu da sha’awa, kuma tana iya karkatar da shi daga tafarkin gaskiya. Idan mutum bai kula ba, zuciyarsa za ta janyo masa son abin da bai dace ba, ko kuma nuna ƙyama ga abin da Allah ya shar’anta wanda hakan zai kai mutum da barin Allah da addinsa. Don haka; dole ne mutum ya kula da gyaran zuciyarsa.
Maganin Son Zuciya: Maganin son zuciya shi ne mutum ya fi ƙarfin ta, Wato mutum ya tilasta wa zuciyarsa bin gaskiya, ko da kuwa tana son akasin haka. Tanƙwara ta ta bi gaskiya, yana nufin horar da zuciya kan gaskiya da bin umurnin Allah. Hakan na faruwa ne ta hanyar tilasta wa kai yin biyayya, ta hanyar salla da azumi, da ambaton Allah, da kasancewa cikin kyawawan ayyuka tare da addu’a Allah Ya tsarkake ta.
3. Duniya: Duniya tana da ruɗi da ƙawanyar ƙyaleƙyale, tana janyo hankalin mutum zuwa ga jin daɗi kamar samun dukiya, ko matsayi, da sauran abubuwan da ke iya karkatar da shi daga bin Allah. Allah ya bayyana cewa duniya ruɗi a wurare daban-daban a cikin Alƙur’ani, hakanan Hadisai masu yawa sun yi bayani a kan ruɗin da duniya take yi wa mutane.
Maganin Duniya: Guje wa ƙyaleƙyalenta da ruɗinta, Wato mutum ya fahimci cewa duniya ba ta da daraja idan aka kwatanta da lahira, kuma bai kamata ya jefa kansa cikin ruɗinta ba, domin ba ta da tabbas. Mutum ya kasance mai tsoron Allah da ƙoƙarin bin dokokinsa a kowane hali.
4. Halittu (Mutane): Mutane na iya zama sanadin da zai hana mutum bin Allah, musamman idan yana koyi da su a kan abin da ba daidai ba. Akwai waɗanda za su janyo mutum cikin halayen banza ko su hana shi aikata alheri, ta yadda hakan zai lalata masa zuciya, domin zama da maɗaukin kanwa yana kawo farin kai.
Maganin Mutane: Karkata ga Allah Shi kaɗai, wato mutum ya yi ƙoƙarin maida hankalinsa ga Allah kaɗai, ba wai ya dogara da mutane ko kuma ya dinga yin abubuwa don faranta musu ba. Hakanan mutum ya nilisanci biyayya ga mutane idan a cikin abin da yake ɓata; Idan mutane suna jagorantar mutum zuwa ga ɓarna, ya kamata ya guje musu.
Zaɓar abokai nagari yana taimaka wa mutum wajen zama nagari. Ya zaɓi waɗanda za su taimaka masa wajen bin Allah, ba waɗanda za su janye shi zuwa ga halaka ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Abu Razina Nuhu Ubale Paki
এছাড়াও পড়ুন:
Afirka Ta Kudu Ta Caccaki Amurka Kan Korar Jakadanta Daga Washington
A ranar Juma’a ce Amurka ta bai wa Jakadan Afirka ta Kudu, Ebrahim Rasool, wa’adin sa’o’i 72 ya tattara komatsai ya fice daga ƙasar.
Hakan na kunshe cikin wata ’yar takaitacciyar sanarwa da mai magana da yawun ma’iakatar harkokin wajen Amurka, Chrispin Phiri ta fitar.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya zargi Ebrahim Rasool da kasancewa “dan siyasar wariyar launin fata mai kyamar Amurka,” lamarin da ya kara rura wutar rikicin diflomasiyya da ya kunno kai tsakanin Washington da Pretoria.
A cikin watan Fabarairun da ya gabata ne Shugaba Donald Trump ya wallafa wani saƙo a shafinsa na sada zumunta na Truth Social cewa Amurka ta dakatar da duk wani tallafi da take bai wa Afirka ta Kudu, sakamakon zarginta da ƙwace gonakin fararen fata na ƙasar.
Wannan dalili ne ya sa shugaba Trump ya sanar da cewa duk wani manomi da aka kwace wa gona, kuma yake fatan koma wa Amurka to zai samu izinin zama ɗan ƙasar cikin sauƙi.
Matakin da Amurka ta dauka na korar jakadan Afirka ta Kudu “abin takaici ne,” kamar yadda ofishin shugaban ƙasar Cyrill Ramaphosa ya bayyana a ranar Asabar, yana mai kira ga “gyara diflomasiyya” tsakanin kasashen biyu.