Sin Za Ta Buga Karin Haraji Kan Wasu Hajojin Canada Da Ake Shigarwa Kasar Bayan Kammalar Bincike
Published: 8th, March 2025 GMT
Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta sanar a Asabar din nan cewa, za ta kara haraji kar kaso 100 kan wasu kayayyaki da ake shigowa da su kasar daga Canada, bayan da ta kammala bincike kan batun nuna banbanci a hada-hadar cinikayya.
Harajin zai fara aiki ne tun daga ranar 20 ga watan nan na Maris, zai kuma kunshi karin kaso 100 bisa mai rapeseed, da tunkuza, da waken peas, yayin da kuma albarkatun teku, da naman alade da ake shigarwa Sin daga Canada, aka yi musu karin harajin kaso 25 bisa dari.
Mahukuntan kasar Sin sun ce matakin ya biyo bayan binciken da aka gudanar game da nuna banbanci a hada-hadar cinikayya, wanda ya tabbatar da cewa, matakan da kasar Canada ta dauka kan hajojin Sin da ake shigarwa kasar sun haifar da cikas, ga harkokin cinikayyar da aka saba gudanarwa tsakanin sassan biyu, kana sun illata halastacciyar moriyar kamfanonin kasar Sin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun kashe mai juna biyu da wasu mutum 4 a Sakkwato
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe mutum biyar, ciki har da wata mata mai juna biyu a ƙauyen Alkalije da ke Ƙaramar Hukumar Yabo ta Jihar Sakkwato.
Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Litinin lokacin da maharan suka mamaye ƙauyen, inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi.
An buƙaci tsige shugaban APC na Kuros Riba Mai cutar HIV ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe a YobeWani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce maharan sun daɗe suna shigowa daga Jihar Kebbi suna kai hare-hare kan al’ummomin yankin.
“Sun saba zuwa daga Kebbi da Silame, suna kashe mutane ko su yi garkuwa da su. A wasu lokuta ma suna ɗora wa al’umma haraji, idan ba a biya cikin wa’adin da suka bayar ba, sai su kawo hari,” in ji shi.
Wata majiya ta bayyana cewa akwai wasu mutum biyu da suka jikkata sakamakon harbin bindiga da ke karɓar magani a wani asibiti da ke kusa da yankin.
Shugaban al’umma a yankin ya roƙi gwamnati ta kafa ofishin jami’an tsaro a yankin domin daƙile barazanar maharan, yana mai cewa yanzu babu ko ɗaya a yankin.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sanda ta Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce bai samu rahoton lamarin ba tukuna, amma zai bincika.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, bai waiwayi Aminiya da wani ƙarin bayani ba.
Ƙauyen Alkalije na cikin gundumar Kilgori da ke iyaka da Ƙaramar Hukumar Silame da wasu ƙauyuka na Jihar Kebbi.