Rahotanni da ke fitowa daga kasar suna nuni da cewa, Yawancin fararen hula da aka kashe a tashe-tashen hankulan da suka faru a wannan Juma’a, dakarun sabuwar gwamnatin kasar ta Syria ne suka kashe su, kamar yadda binciken kungiyar kare hakkin bil Adam ta (SOHR) ya tabbatar.

Ayyukan tashe-tashen hankulan sun yi sanadin Kisan mutuwar fararen hula 162 a lardunan gabar tekun Syria, ciki har da mata da kananan yara, in ji rahoton kungiyar ta SOHR.

Akasarin wadanda aka kashe dai kamar yadda aka gani a wasu fayafayin bidiyo da aka dauka, jami’an tsaron sabuwar gwamnatin Syria ne da suke da alaka kungiyoyi masu tsatsauran ra’ayi irin su Tahrir Sham da makamantansu da suke da alaka da Alqaida ne suka kama mutanen, bisa tuhumar cewa suna da alaka da tsohuwar gwamnatin Bashar Assad, a kan haka suka yanke musu hukuncin kisa a nan take kuma suka kashe su.

Kungiyar ta ce wannan matakin na nuni da irin mawuyacin hali mai matukar hadari da Syria ta fada a ciki, inda ake ci gaba da cin zarafi  jama’a da kuma muzguna musu da sunan daukar fansa a kan tsiraru marasa rinjaye.

Wasu daga cikin Hotunan da aka dauka sun yadu a shafukan sada zumunta, wadanda suke nuni da manyan laifukan yaki. Rahoton ya ce wasu daga cikin faifan bidiyo sun nuna lokacin da jami’an tsaron sabuwar  suka harbe wasu ‘yan kasar Syria da ba su dauke da makami, wadanda aka wulakanta su kafin a yi musu kisan gilla.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

IRGC Ta Ja Kunnen Kasashen Turai Dangane Da Taimakon Da Suke Bawa HKI

Janar majid Khatami Shugaban Bangaren Leken Asiri Na dakarun IRGC masu kare juyin juya halin musulunci ya bayyana cewa, rundunarsa tana sa ido akan take –taken kasashen Turai dangane da ayyukan sharrin da HKI take gudanarwa a yankin. Ya kuma kara da cewa rundunarsa tana da hanyoyin wadanda zata yi amfani da su , wanda daga karshe turawan ne zasu cutu a goyon bayan da suke bawa HKI.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya nakalto Janar Majid Khatami yana fadar haka a lokacinda yake jawabi a taron addu’a da girmama Ghulam Hussan Ghaiba a nan Tehran. Dangane da marigayin ya bayyana cewa ya kasance cikin wadanda suka je yakin kare kasa na shekaru 8, kuma a cutu da makaman guban da sadam ya jefa a yakin don haka tun lokacin yake fama da matsalolin rashin lafiya har zuwa lokacin da bar duniya a cikin yan kwanakin da suka gabata.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yansanda Sun Ceto Mutane 28 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Katsina
  • DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure
  • Kwamitin Neman Sabuwar Karamar Hukumar Kanya Babba Ya Gabatar Da Takardar Bukatarsa Ga Majalisar Dattawa
  • Mutanen Sweida Na Kasar Siriya Suna Fama da Rashin Abinci da Ruwa
  • Sin Za Ta Ba Da Tallafin Kula Da Yara A Fadin Kasar
  • Gwamna Namadi Ya Biya Sama Da Naira Biliyan Daya Ga Tsofaffin Ma’aikata
  • An Yanke Hukuncin Kisa Kan Yan MKO A Nan Iran
  • IRGC Ta Ja Kunnen Kasashen Turai Dangane Da Taimakon Da Suke Bawa HKI
  • Iran Da Afganistan Sun Tattauna Dangane Da Komawar Afganawa Gida
  • Gwamnatin APC ta jefa ’yan Najeriya cikin ƙangin talauci — Shugabar LP