Ƴan Nijeriya 85 Za Su Iso Lagos Daga Amurka A Yau
Published: 17th, February 2025 GMT
Gwamnatin Amurka ta fara aiwatar da matakan korar ‘yan Nijeriya daga ƙasar, inda ake sa ran mutane 85 za su iso Lagos, yayin da wasu 116 ke tsare.
Jakadan Amurka a Nijeriya, Richard Mills, ya bayyana haka yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Ministan harkokin wajen Nijeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, a Tafawa Balewa House da ke Abuja.
A nata ɓangaren, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu ta bayyana damuwa kan yadda ake gudanar da tsare-tsaren korar mutanen, inda ta buƙaci da a bi ƙa’idojin da suka dace na ƙasa da ƙasa. Ta jaddada cewa dole ne a samar da hanyoyin da za su rage raɗaɗin korar, musamman ga waɗanda ba su aikata wani laifi na tashin hankali ba.
এছাড়াও পড়ুন:
An tallafawa iyalan jami’an ‘yan sanda da Naira miliyan N13.4m a Borno
Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta gabatar da cakin kuɗi Naira 13 da dubu ɗari 4 da 28 da ɗari 6 da 59.95 ga ’yan uwan ’yan sanda 10 da suka mutu a bakin aiki.
Taron gabatar da kuɗin wanda aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Maiduguri, na da nufin bayar da tallafin kuɗi ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.
Yadda aka kama mai garkuwa da mutane yana tsaka da cin kasuwar shanu a Neja ’Yan sanda sun kama mutum 5 kan kisan Kanawa 2 a BenuweJami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana hakan ne manema labarai a hedikwatar rundunar da ke garin Maiduguri.
Kwamishinan ’yan sanda, CP Naziru Abdulmajid ne ya gabatar da jawabin a madadin Sufeto-Janar na ’yan sanda (IGP), Kayode Adeolu Egbetokun.
Wannan shiri yana ƙarƙashin Ƙungiyar ’yan sandan Najeriya (Group Assurance Life and IGP Welfare Scheme) wanda aka tsara don rage wahalhalun da iyalan ma’aikatan da suka yi sadaukarwa ke fuskanta.
Kwamishina Abdulmajid ya jajantawa iyalan waɗanda suka rasu, yana mai tabbatar musu da jajircewar sufeto-janar na ’yan sanda na tabbatar da jin daɗin jami’an da ke aiki da kuma jaruman da suka mutu.
Ya jaddada cewa, sadaukarwar da waɗannan jami’an suka yi ba za a taɓa mantawa da su ba, kuma rundunar ta ci gaba cewa za ta ci gaba sadaukar da kai wajen tabbatar da jin daɗin iyalan da suka bari.”
Kwamishinan ’yan sandan ya kuma shawarci waɗanda suka ci gajiyar kuɗaɗen da su yi amfani da kuɗaɗen cikin adalci, inda ya buƙace su da su saka hannun jari a harkar kasuwanci mai ɗorewa da zai taimaka wajen tabbatar da makomar waɗanda suka mutu na jami’an na su.
Da yake jawabi a madadin waɗanda suka ci gajiyar shirin, Jerry Joel ya bayyana matuƙar godiya ga rundunar ’yan sandan Najeriya da babban sufeton ’yan sandan ƙasar bisa goyon bayan da suka bayar a wannan lokaci mai cike da ƙalubale a gare su.