Aminiya:
2025-07-31@12:24:45 GMT

Jirgin soji ya kashe fararen hula a Katsina

Published: 17th, February 2025 GMT

Wani jirgin sojin Najeriya ya jefa wa fararen hula bom inda ya kashe fararen hula bakwai a yankin Yani  da ke Ƙaramar Hukumar Safana ta Jihar Katsina.

Mamatan sun hada da mutum shida ’yan gida ɗaya, kamar yadda wani shaida ya bayyana.

Hakan na zuwa ne bayan wasu jami’an tsaro da suka hada da ’yan sanda biyu da wani jami’in Rundunar Tsaron Al’umma na jihar (CWC) sun kwanta dama a yayin musayar wuta da ’yan bindiga a Ƙaramar Hukumar a ranar Asabar.

Wani mazaunin Gundumar Zakka da ke Ƙaramar Hukumar, yankin da abin ya faru, ya bayyana cewa an yi arangamar ne bayan zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar ranar Asabar, inda ’yan bindiga suka shirya kai wa masu zaɓe hari a kauyen Zakka.

Bayan samun rahoton shirin harin ne jami’an tsaron suka je domin daƙile ’yan bindigar, inda a garin haka aka yi musayar wuta tsakanin bangarorin. Wani hafsan dan sanda da jami’in CWC sun rasu, daga bisani wani ɗan sanda da ya ji rauni a arangamar ya cika.

Ya bayyana cewa, “bayan nan ne wani jirgin soji ya zo, watakila domin kai wa jami’an tsaron ɗauki. A nan ne ya jefa bom a yankin Yani da ke ƙauyen Zakka, wanda ya halaka  mutum shida ’yan gida ɗaya, ya kuma jikkata wata mata.”

Wannan ba shi ne karon farko ba da jirgin soji ya kai wa fararen hula hari ba a Ƙaramar Hukumar ta Safana.

A watan Yulin shekara ta 2022 wani jirgin soji ya jefa bom a yankin Kunkumi da ke Ƙaramar Hukumar ta Safana, inda ya kashe aƙalla mutum biyu tare da jikkata wasu tara.

Wakilinmu ya yi duk ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sanda da sojoji da ke jihar game da lamarin, amma hakan ya faskara.

Amma dai kafar yaɗa labarai 4 Deutsche Welle (DW) ta ruwaito labarin harin, tana mai ambato wasu shaidu da suka tabbatar da aukuwarsa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Ƙaramar Hukumar jirgin soji ya fararen hula

এছাড়াও পড়ুন:

Wani mutum ya mutu yayin raba faɗar ma’aurata 

Wani mutum ya rasu yayin da yake ƙoƙarin raba wani mutum da matarsa da fada a yankin Babban Birnin Tarayya.

Da farko mutumin ya faɗi ne a sume kafin daga bisani rai ya yi halinsa a yankin Dogon-Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Abaji.

Wani ganau, Barnabas Yakubu, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da yamma ne ma’auratan, waɗanda makwabta ne ga mamacin, suka fara faɗa ne bayan wata rashin fahimta, shi kuma Ayuba, bayan jin hayaniyar, ya fito daga ɗakinsa don shiga tsakani.

A cewarsa, mamacin ya dawo ne daga gonarsa kuma yana shirin yin wanka lokacin da ya ji maƙwabcinsa yana dukan matarsa.

Ya ce, Ayuba nan take ya ajiye soso da gugar ruwansa ya ruga don shiga tsakani amma ya faɗi sumamme a yayin.

Ayuba, wanda aka yi imanin yana cikin koshin lafiya kafin faruwar lamarin, an garzaya da shi asibiti a garin Gawu, inda likitocin da ke bakin aiki suka tabbatar da mutuwarsa.

Sarkin yankin, bayan samun labarin lamarin, ya sanar da ’yan banga tare da ba da umarnin kama ma’auratan, waɗanda daga baya aka mika su ga jami’an tsaro a Gawu.

Ibrahim, daya daga cikin ’yan bangan, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa, “Mun fahimci cewa ƙaramar rashin fahimta ce kawai ta kai ga faɗan tsakanin makwabcin mamacin da matarsa.”

Ya ƙara da cewa an kai gawar mamacin kauyensa na Paiko a Jihar Neja don binnewa.

’Yan sanda a yankin Gawu sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce har yanzu ana ci gaba da bincike.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ZAMFARA: APC Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Kawo Dauki Don Matsalar Tsaro Na Kara Tsananta
  • ’Yansanda Sun Ceto Mutane 28 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Katsina
  • ’Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina
  • Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Lod Da Ke Jaffa Da Makami Mai Linzami
  • Kwale-kwale Ya Kife Da Fasinjoji 16 A Karamar Hukumar Taura
  • ‘Yan Sanda A Kano Sun Kama Kasurgumin Dan Fashin Nan Barga Da Wasu Mutum 14
  • Wani mutum ya mutu yayin raba faɗar ma’aurata 
  • Jami’an Tsaron Katsina Sama Da 100 Sun Rasu A Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda – Gwamnati
  • ’Yan sa-kai aƙalla 100 da jami’an tsaro 30 sun mutu a bakin aiki a Katsina —Gwamnati
  • An kashe ’yan ta’adda 45 a Neja