Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kashe Naira Tiriliyan 4.2 Don Aikin Manyan Hanyoyi
Published: 7th, February 2025 GMT
Wannan ya hada da kilomita 65 daga Legas zuwa Ogun da wani karin da zai tashi daga Kalabar ta Akwa Ibom, wanda titin zai ginu a karkashin ‘Engineering, Procurement, and Construction’ (EPC) da tsarin za su kula da shi na tsawon shekaru goma bayan ginawa.
Majalisar zartarwar ta amince da kashe naira biliyan 470.
Shi kuma babban hanyar Lagos zuwa Ibadan ya samu amincewar naira biliyan 195 domin a gina shi a karkashin asusun shirin inganta hanyoyi na shugaban kasa (PIDF), da ke da manufar rage cunkoso da inganta sufuri a manyan hanyoyin da ake yawan bi.
Sai dai hanyar Abuja zuwa Kano wanda aka jima da bayar da shi ga kamfanin ‘Julius Berger’, yanzu an sake fasalta shi yadda za a samu nasarar kammala aikin a kan lokaci. Ministan ya ce yanzu aikin ya koma kilomita 118 kuma za a sanya wutar layi.
Ministan ya ce dukkanin ayyukan masu inganci ne za a yi kuma da nufin kyautata rayuwar al’ummar kasa da kare rayukan a yayin tafiye-tafiye, ya ba da tabbacin gwamnati na sanya ido wajen gudanar da nagartaccen aiki.
কীওয়ার্ড: Gwamnatin Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Shettima Ya Jagoranci Tawagar Gwamnatin Tarayya Don Yi Wa Iyalan Ogbeh Ta’aziyya
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp