Kisan Rimin Zakara: Gwamnan Kano Ya Umarci Jami’ar Bayero Ta Dakatar Da Rushe Gidaje
Published: 7th, February 2025 GMT
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci al’ummar Rimin Zakara da ke karamar hukumar Ungogo domin jajantawa iyalan wadanda rikicin ya rutsa da su wanda ya yi sanadin asarar rayuka uku tare da jikkata wasu da dama.
A ziyarar tasa, Gwamna Yusuf ya gana da iyalan wadanda suka rasu, inda ya jajanta musu tare da bayyana cewa gwamnatin jihar za ta dauki nauyin iyalan mutanen uku da suka rasu.
Ya kuma ba da umarnin a gaggauta biyan kudaden jinya ga duk wadanda suka jikkata tare da samar da kayan abinci don tallafawa iyalan wadanda abin ya shafa.
A cikin nuna jin kai, gwamnan ya bayyana shirin gina sabon masallacin Juma’a a Rimin Zakara a matsayin sadaqatu jariya (dauwamammiyar sadaka) da aka sadaukar da rayukan ukun da suka rasu.
Bugu da kari, gwamnan ya kaddamar da wani tsari na ci gaban al’umma, wanda ya hada da:
Haɗa al’ummar yankin da tashar wutar lantarki ta kasa da Gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana domin samar da ruwa mai tsafta da Samar da cibiyar kula da lafiya ta farko don inganta ayyukan kiwon lafiya da haɓaka hanyar ciyarwa don inganta sufuri a cikin Rimin Zakara.
Gwamna Yusuf ya yi kakkausar gargadi ga jami’an tsaro kan amfani da harsasai masu rai kan ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba, yana mai jaddada cewa irin wannan abu ba abu ne da za a amince da shi ba.
Domin tabbatar da bin diddigin lamarin, gwamnan ya kafa kwamitin bincike da aka dorawa alhakin gano musabbabin faruwar lamarin tare da zakulo wadanda ke da hannu a lamarin.
Hakazalika, gwamnan ya kuma yi wa mahukuntan Jami’ar Bayero ta Kano huduba a ofishinsa tare da umartar su da su dakatar da duk wani mataki na rusa gine gine a wajen.
Ya kuma bayyanawa al’ummar yankin kudurin sa na ganin an shawo kan rikicin fili da aka shafe sama da shekaru 40 ana yi tsakanin al’ummar Rimin Zakara da Jami’ar Bayero Kano.
Shugaban al’ummar yankin, Baba Habu Mikail, ya nuna matukar godiya ga gwamnan bisa yadda ya nuna tausayi, inda ya bayyana cewa al’umma ba za su taba mantawa da alherinsa ba.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gwamna Ziyara Rimin Zakara
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori
Bug da kari Tinubu ya jinjina wa Shugaban jami’ar, Farfesa Wahab Olasupo Egbewole (SAN)da ‘yan tawagarsa wajen maida hankalin da suka yi na bunkasa Jami’ar da kumna kudurinta na muradun ci gaban da ake bukata.
Shi ma anashi jawabin Shugaban Jami’ar Sarkin Katsina, Alhaji. Abdulmumin Kabir Usman, wanda Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Idah ya wakilta, ya nuna jin dadinsa kan irin kokarin da UNILORIN saboda bunkasar ilimi da kumasamar wuraren koyon kaaratu masu kyau da kuma suka dace.
Ya yi ma kallon ayyukan da ak kaddamar a matsayin“ irin abubuwan da ake bukatar gani ke nan”da za su taimakawa lamarin koyarwa, koyo,da kuma bincike, inda ya kara da cewa yadda Jami’ar ta maida hankalinta wajen bunkasa dabarar koyon yin abubuwa zai taimakawa dalibai su tashi da sun koyi abubuwan da zasu yi baya rayuwar da suka yi cikin aji.
A nashi jawabin mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa. Egbewole ya nuna farin cikinsa da godew a Shugaban kasa Tinubu kan yadda ya amince da gaiyar da Jami’ar ta yi ma shi, da kuma taimaka mata wajen tafiyar da bunkasar abubuwan jin dadi.
“Muna nan muna sa ido saboda ci gaban samun abubwan da suke taimakawa ci gaba kwarai da gaske a kowace rana kamar yadda yace yana da amincewa da yardarm ci gaba da samun hakan’’.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA