Leadership News Hausa:
2025-08-12@07:09:43 GMT

Rikicin Shugabanci Na Barazana Ga Babban Taron Jam’iyyar PDP

Published: 31st, January 2025 GMT

Rikicin Shugabanci Na Barazana Ga Babban Taron Jam’iyyar PDP

An yi kokarin cire Damagum ta hanyoyin siyasa, ciki har da yiwuwar nada sabon shugaba daga yankin arewa ta tsakiya, amma hakan ya ci tura.

Gwagwarmayar bangaranci dai ta kara dagula al’amuran cikin gida na jam’iyyar, inda aka samu bangaren masu biyayya ga fitattun mutane irin su tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Wadannan rarrabuwar kawuna sun gaza samar da fahimtar juna, wadanda suka zama kalubalen da ya haifar da dakatarwar wasu daga cikin jami’an jam’iyyar.

Yayin da watan Fabrairun 2025 ke gabatowa, masu ruwa da tsaki sun nuna damuwarsu na cewa PDP na fuskantar babban kalubale a gabanta.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Tsohon Shugaban PDP Audu Ogbeh Ya Rasu

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP kuma tsohon ministan noma daga 2015 zuwa 2019, Audu Ogbeh, ya rasu a ranar Asabar, 9 ga Agusta, yana da shekaru 78 a duniya, kamar yadda iyalinsa suka tabbatar.

A cikin wata sanarwa, iyalan sun ce: “Ya rasu cikin kwanciyar hankali, ya bar mana gado na gaskiya, hidima da jajircewa ga kasa da al’umma. Mun sami kwanciyar hankali daga yadda ya shafi rayuka da kuma yadda ya kafa misali.”

Ko Nawa Za A Bani Ba Zan Iya Fitowa A Matsayin Kwarto Ko Dan Daudu A Fim Ba -Dan Asabe Olala Jihar Gombe Za Ta Rungumi Shirin Farfado Da Noman Auduga Na Gwamnatin Tarayya – Inuwa

Iyalan sun bayyana cewa za a sanar da yadda za a gudanar da jana’izarsa a nan gaba, tare da godewa abokai, da abokan aiki. Sun kuma roƙi a basu dama domin yin jimamin rasuwar baban nasu.

Rahoton LEADERSHIP ya nuna cewa Ogbeh, wanda ya shahara a siyasa, rubuce-rubuce da aikin gona, ya shugabanci PDP daga 2001 zuwa 2005 kafin ya zama minista a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Babban Dalilin EFCC Na Yi Wa Tsohon Gwamnan Sokoto, Tambuwal, Tambayoyi
  • An Samu Karuwar Adadin Kamfanoni Masu Yin Rajista A Yankin HK
  • Za a gyara tarbiyar tubabbun ’yan daban Kano
  • Manoma 2 Sun Rasu, 2 Sun Jikkata A Wani Rikicin Filin Gona A Yobe
  • Ku Yaƙi Cin Hanci Ba Ƴan Adawa Ba – ADC GA EFCC
  • Ma’aikatan shari’a 97 sun samu ƙarin girma a Borno
  • Cacar Baki Ta Ɓarke Tsakanin el-Rufai Da APC Kan Tazarcen Tinubu A 2027
  • Za a biya ma’aikata 445 garatutin sama da biliyan ɗaya a Kebbi
  • Za a biya ma’aikata 445 garatitun sama da biliyan ɗaya a Kebbi
  • Tsohon Shugaban PDP Audu Ogbeh Ya Rasu