Tubabbun ’yan Boko Haram 5,000 sun koma cikin jama’a
Published: 31st, January 2025 GMT
Mayaƙan Boko Haram aƙalla 5,000 da suka tuba sun koma cikin al’umma da iyalansu, a cewar Cibiyar Yaƙi da Ta’addabnci na Ƙasa.
Cibiyar, wadda ke ƙarƙashin Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa Kan Sha’ani Tsaro ta bayyana cewa babu ko mutum ɗaya da cikin tubabbun mayaƙan na Boko Haram da ya sake ɗaukar makami.
Ta bayyana cewa gwamnatin Jihar Borno ta tabbatar cewa wata shida bayan kammala ba su horo da sauya tunanin tsofaffin mayaƙan, amma har yanzu babu labarin ko mutum ɗaya daga cikinsu da ya yi tubar muzuru.
Shugabar Sashen Daƙile Rikice-rikice Masu Alaƙa da Tsattsauran Ra’ayi (PVEA) ta Cibiyar, Ambasada Mairo Musa Abbas, ce ta bayyana haka a yayin taron gwamnonin yankin Tafkin Chadi a Maiduguri, Jihar Borno.
NAJERIYA A YAU: Anya Jam’iyyar PDP Za Ta Kai Labari A Fagen Siyasar Najeriya Kuwa? KAROTA za ta kashe N250m wajen gyaran motoci 5 a Kano Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-RufaiDa take jawabi kan kula da masu ficewa daga Boko Haram da kuma kawo ƙarshen kungiyoyi masu ɗaukar makamai, Ambasada Mairo ta jaddada muhimmancin amfanin da matakai da dabaru na bai-ɗaya a tsakanin gwamnonin ya kin domin magance matsalar tsaron.
Ta ce shirin Operation Safe Corridor da ke karɓa ta tare da sauya tunanin tubabbun ’yan Boko Haram ya yi nasarar sauya tunanin tsofaffin mayaƙan ƙungiyar guda 5,000.
A cewarta, Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) tana aiki da sarakunan gargajiya da malaman addini a duk ƙananan hukumomi 774 da ke faɗin ƙasar nan domin sanya ido kan yanayin rayuwar tubabbun mayaƙan da suka dawo cikin al’umma.
Ta kuma jinjina wa tsarin da Gwamnatin Jihar Borno ta jagoranta kan tubabbun mayaƙan da masu tsattsauran ra’ayi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram Mayaƙan Boko Haram
এছাড়াও পড়ুন:
INEC Ta Gudanar da Taron Masu Ruwa da Tsaki Kafin Zaɓen Cike Gurbi na Babura/Garki
A wani ɓangare na shirin gudanar da zaɓen cike gurbi na Babura/Garki a Majalisar Tarayya, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) reshen Babura ta shirya muhimmin taron masu ruwa da tsaki domin tabbatar da sahihin zaɓe mai inganci da haɗin kai.
A jawabinsa yayin taron, jami’in zaɓe na ƙaramar hukumar Babura, Malam Hafiz Khalid, ya gabatar da cikakken jadawalin ayyukan zaɓen.
Ya jaddada muhimmancin haɗin kai da gaskiya a kowane mataki, yana mai bayyana zaɓen a matsayin aikin gama gari da ke buƙatar goyon bayan duk masu ruwa da tsaki.
Mahalarta taron sun bayar da shawarwari masu amfani tare da gabatar da muhimman tambayoyi da suka shafi inganta sahihanci da nasarar zaɓen.
Wasu daga cikin batutuwan da aka tattauna sun haɗa da shirye-shiryen kayayyakin aiki, tsaro, wayar da kan masu zaɓe, da sauransu.
An kammala taron da sabunta ƙudurorin haɗin guiwa daga dukkan mahalarta, wajen tabbatar da gudanar da zaɓen cike gurbi cikin lumana, ‘yanci, adalci, da sahihanci a yankin Babura/Garki.
Wakilin Rediyon Najeriya ya bayyana cewa, taron da aka gudanar a ofishin INEC na Babura, ya samu halartar masu ruwa da tsaki da suka haɗa da Hakimin Babura, jami’an tsaro, wakilan jam’iyyun siyasa, jami’ai daga Ƙungiyar Direbobin Ƙasa (NURTW), Ƙungiyar Masu Motocin Haya (NARTO), ƙungiyoyin farar hula (CBOs), da sauran jami’an INEC.
Usman Muhammad Zaria