Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
Published: 30th, January 2025 GMT
Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya mika gaisuwar sabuwar shekara da fatan alheri ga kasar Sin yayin da ta shiga sabuwar shekarar gargajiya. Cikin sakonsa a jiya Laraba, Cyril Ramaphosa ya bayyana kwarin gwiwar shekarar Maciji za ta ci gaba da karfafa matsayin Sin na karfin samar da kyawawan abubuwa da hikima da wadata na bai daya ga duniya.
Shi ma a jiyan, shugaban Zambia Hakainde Hichilema, ya aikewa shugaban kasar Sin Xi Jinping gaisuwar sabuwar shekarar gargajiya ta kasar, yana mai fatan samun ci gaban kasashen da al’ummominsu.
Kotu Ta Bayar Da Belin Sowore Kan Naira Miliyan 10 Kafar CMG Ta Samu Nasarar Yayata Shirin Shagalin Murnar Bikin Bazara A Kasashen WajeA ranar Talata kuma, shugaban Angola Joao Lourenco ya mika gaisuwar sabuwar shekara ga gwamnati da al’ummar Sinawa, yana mai fatan karfafa dangatakar kasarsa da Sin.
Shi ma shugaban Maldives Mohamed Muizzu, ba a bar shi a baya ba, domin a jiya Laraba ya aikewa takwaransa Xi Jinping da al’ummar Sinawa gaisuwa da fatan alheri a sabuwar shekara. Ya kuma yi fatan sabuwar shekarar za ta kawowa al’ummar Sin wadata da koshin lafiya da farin ciki. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
এছাড়াও পড়ুন:
Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya
Babban sakataren MDD António Guterres, ya bayyana a jiya Talata cewa, jerin shawarwarin da Sin ta gabatar wato shawarar raya duniya, shawarar tabbatar da tsaron duniya, shawarar raya wayewar kan al’ummun duniya, da kuma jagorantar harkokin duniya, sun dace da ka’idar kundin tsarin MDD.
Guterres ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida a wani taron manema labarai da aka yi a ranar. Ya ce shawarwarin da Sin ta gabatar sun mutunta manufar kasancewar bangarori da dama, kuma sun goyi bayan MDD a matsayin cibiyar hadin gwiwar kasa da kasa, tare da dukufa kan inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban da warware rikice-rikice cikin lumana.
Guterres ya kara da cewa, yanzu ana fuskantar rarrabuwar kawuna a fagen siyasa ta duniya da kuma karuwar yaduwar rikice-rikice, da ma rashin hukunta masu laifi. Bugu da kari, sabbin fasahohi suna ci gaba da bullowa “ba tare da bin wani tsari ba”, yayin da rashin daidaito ke kara tsananta. A wannan yanayi, babban taro karo na 80 na MDD mai tsawon mako guda da za a fara a mako mai zuwa, zai ba da duk wata dama ga tattaunawa da shiga tsakani.(Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp