2025-11-27@22:30:53 GMT
إجمالي نتائج البحث: 12019
«Barista Sani»:
Rundunar ’yan sandan Jihar Anambra ta gano gawar wasu mata uku ’yan ƙasar Kamaru da ake zargin waɗanda suka yi garkuwa da su domin neman kuɗin fansa sun kashe su. Haka kuma, rundunar ta ce ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a lamarin, Nonso Augustine Akpeh da Kingsley Akpeh, waɗanda ake...
Ana fargabar cewa wata mata mai suna Success ta kashe wata yarinya mai shekaru bakwai, Alicia Olajumoke, a unguwar Rumueme da ke birnin Fatakwal na Jihar Ribas. Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa matar da ake zargin tana da kusanci da dangin mahaifiyar yarinyar, wacce ita kaɗai ce a wurin iyayenta. El-Rufai ya koma...
Sufeto Janar na ’Yan sandan Nijeriya, Olukayode Egbetokun, ya sanar da cewa sun aiwatar da umarnin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na janye dakarunsu daga gadin ɗaiɗaikun mutane da ake kira VIP. IG Egbetokun ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a yau Alhamis, yana mai cewa zuwa yanzu sun janye dakaru 11,566 daga...
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana jimaminsa kan rasuwar babban malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi, lamarin da ya ce ya kaɗu matuƙa da ya samu labarin. Tinubu ya ce jagoran na ɗarikar Tijjaniya mutum ne mai daraja da ƙima, sannan ya bayyana shi a matsayin madubi wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa....
Iran ta yi Allah wadai da matakin gwamnatin Ostiraliya na ayyana Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) a matsayin “mai tallafawa ta’addanci,” “Matakin da gwamnatin Ostiraliya ta dauka wani abu ne mai laifi ne mai hadari, wanda aka tsara a karkashin gwamnatin Sahayoniya don karkatar da hankalin jama’a daga kisan kare dangi da aka...
Shugaban Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa ya soki kalaman takwaransa na Amurka Donald Trump na cewa ba zai gayyace shi taron kasashen gungun G20 mafiya karfin tattalin arziki na duniya a shekara mai zuwa a Florida. Ramaphosa ya ce abin takaici ne yadda Trump ke ci gaba da daukar matakai bisa labaran da ba na...
Kungiyar raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta yi Allah wadai da juyin mulkin da ya faru a ranar Alhamis a kasar Guniea Bissau, kwanaki uku bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu, inda ta kira shi da “barazana kai tsaye ga zaman lafiyar kasar da yankin.” Wannan “juyin mulkin soja” ya zama...
Kasashen Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi Allah wadai da “karuwar yawan tashin hankalin” da yahudawa ‘yan gudun kama wuri zaman ke yi wa fararen hular Falasdinawa, tare da yin kira ga Isra’ila da ta kare al’ummar Yammacin Kogin Jordan. “Wadannan hare-haren dole ne a daina su. Suna kawo cikas ga kokarin da ake...
An sake tabbatar wa ma’aikatan Gwamnatin Tarayya FG da suka yi ritaya cewa za a biya su wani bangare na kudaden ariyas a cikin wannan watan, kamar yadda hukumomin da abin ya shafa suka yi alkawari. Mataimakin Sakataren ƙungiyar masu karɓar fansho ta ƙasa, Alhaji Ahmed Gazali, ya bayar da wannan tabbaci yayin da...
Ɗan wasan gaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid, Kyalian Mbappe ya samu nasarar zura kwallaye huɗu rigis a ragar Olympiacos a wasan mako na biyar na kofin zakarun nahiyyar turai da suka buga a yammacin jiya Laraba. Real Madrid dai caskara Olympiacos 4-3 ne a wasan, lamarin da ya ba ta damar haɗa...
Daga Usman Muhammad Zaria Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, Dr. Builder Muhammad Uba, ya aiwatar da wani aiki na da naira miliyan biyar domin tallafa wa aiwatar da Shirin Tallafawa Yara Mata (AGILE) a yankin. Aikin ya hada da gyaran ajujuwa biyu da samar da muhimman kayan aiki, ciki har da injunan...
Sojojin Guinea-Bissau sun naɗa Janar Horta Nta Na Man a matsayin sabon shugaban ƙasar na rikon kwarya, kwana ɗaya bayan sun yi juyin mulki tare da kama shugaban ƙasar, Umaro Sissico Embalo. Sojojin dai sun kwace mulkin ne yayin da ake shirin bayyana sakamakon zaɓen kasar mai cike da takaddama. Majalisar Wakilai ta nemi gwamnati...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kaduwa da rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Fitaccen malamin ya rasu a Bauchi ranar Alhamis yana da shekaru 101. Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka...
Majalisar Wakilai a ranar Alhamis, ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta yi amfani da diflomasiyya da duk wasu hanyoyi don tabbatar da dawowar tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan lafiya daga Guinea Bissau, bayan juyin mulkin sojoji a ƙasar. Wannan kuduri ya biyo bayan amincewa da kudurin gaggawa da Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Farfesa Julius...
Daga Sani Sulaiman Gwamnan Jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas, ya yi jimami kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2025, yana da shekaru 102. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan...
Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta sanar da karbar gawawwakin shahidai 15 a jiya Laraba a karkashin yarjejeniyar musayar fursunoni, da kungiyar agaji ta “Red Cross” ta shiga tsakani. Sanarwar ma’aikatar kiwon lafiyar ta Palasdinu ta kuma ce, daga lokacin da aka fara musayar zuwa yanzu,adadin gawawwakin shahidan da su ka karba sun kai 345,...
A ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamban 2025 ce Allah ya yi wa fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma jigo a Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi rasuwa. Ya rasu yana da sama da shekaru 100 a duniya. Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa Sheikh Dahiru Bauchi: Malamin da zuri’arsa ta...
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya kafa tarihin zama mutumin da ya fi kowa yawan zuri’ar da ta haddace Alkur’ani a tarihin duniya. Alkaluma sun nuna cewa shehin malamin, wanda a kwanan nan ya cika shekara 100 a duniya, yana da ’ya’ya da jikoki da ma tattaba-kunne kusan 300 da suka...
Kwamandan rundunar soja ta “Sayyidush-shuhada” dake Tehran Janar Qurbani Muhammad Wali Zadeh ya bayyana cewa; makamai masu linzami da Iran take da su ne, da kuma jiragen sama marasa matuki suke takawa makiya birki.” Janar Qurbani Muhammad Wali Zadeh ya kuma ce; Albarkacin sadaukar da jinanai da shahidai su ka yi ne da kuma kwazon...
Daya daga cikin ‘ya’yan babban malamin addinin musulunci a Najeriya Sayyid Ali Dhahiru Usman Bauchi ne ya tabbatar wa da jaridar “Daily Trust” rasuwar malamin. Sayyadi Ali ya furta cewa: ” Tabbas Shehi ya koma ga mahaliccinsa, mu duka daga Allah muke, kuma zuwa gare shi za mu koma.” Haka nan kuma ya kara da...
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi, a matsayin babban rashi ga al’umma. Gwamnan ya bayyana malamin a matsayin jagoran haɗin kai, zaman lafiya, da fahimtar juna tsakanin Musulmi da mabiya addinai daban-daban. ’Yan sanda sun gano harsasai 210 a kan titin Zariya-Funtuwa Allah Ya yi wa...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta gano harsasai 210 da aka jefar a kan babbar hanyar Zariya zuwa Funtuwa, a unguwar Dogo Itace da ke Samaru, Zariya. Lamarin ya faru ne lokacin da DPO na Samaru tare da tawagarsa suke sintiri a kan hanyar. Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa Juyin mulki ya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A cikin shekarun nan, matsalolin tsaro a Najeriya—kamar ta’addanci, da garkuwa da mutane, da rikicin manoma da makiyaya, da kuma ayyukan ’yan bindiga—suna kara ta’azzara, lamarin da ya sanya al’umma da masana tsaro ke tambayar wace hanya ta fi dacewa gwamatani ta yi amfani da shi wajen kawo...
Bayan an zabi kasar Iran a matsayin mamba a kwamitin zartarwa na hukumar yaki da makaman guba ta duniya, wato ‘ the Chemical Weapons Convention (CWC)’ da kuriun jimillar yan majalisar, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa Iran zata yi amfani da damar da ta samu na bin hakkin mutanen kasar...
Wata cibiyar bincike mai suna “Frensic Architecture’ ta bada sanarwan cewa, HKI tana fakewa da tsagaita budewa juna wuta a Gaza a matsayin dama ta sake shata kan iyakoki a zirin gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto cibiyar tana cewa a halin yanzu HKI ta maida ‘koren layin da Trump ya...
Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta bada sanarwan cewa yawan Falasdinawa wadanda sojojin HKI suke kashewa a Gaza yana karuwa duk tare da abinda suka kira tsagaiya budewa Juna wuta. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto ma’aikatar na cewa a cikin sa’oii 24 da suka gabata sojojin HKI sun kashe Falasdinawa 2...
Tsohon shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan a halin yanzu yana birnin Bissau babban birnin kasar Gunea Bissau bayan da sojoji suka kwace mulki suka kuma hana shiga da fita daga kasar. Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar da daruruwan masu sanya ido a zaben da aka gudanar a kasar a...
Ma’aikatar Ma’adinai da wutan lantarki a yankin Kurdistan na kasar Iraki ta bada sanarwan cewa an dakatar da tura iskar gas zuwa cibiyoyin samar da wutan lantarki a yankin saboda hare-haren da aka kai kan wata cibiyar hakar iskar gas a yankin. Tashar talabijan ta Almayadeentv ta kasar Lebanon ta bayyana cewa wani jirgin yaki...
Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya maƙale a Guinea-Bissau bayan da sojoji suka yi juyin mulki tare da karɓe ragamar mulkin ƙasar. Jonathan da sauran baƙi baƙi masu sanya ido kan zaɓen da aka gudanar, ba za su iya barin ƙasar ba domin sojoji sun rufe iyakokin ƙasar baki ɗaya, tare da dakatar da zaɓen...
An kulle Fadar Shugaban Kasar Amurka ta White House tare da wasu gine-ginen gwamnati da dama, sakamakon harbin ɗan bindigar da ya raunata sojoji biyu a kusa da fadar. A yayin, an harbe masu tsaron fadar biyu har lahira. Gwamna Patrick Morrisey da farko ya ce an kashe sojojin, amma daga baya ya ce yana...
Daga Isma’il Adamu Gwamna Dikko Radda na Jihar Katsina ya sanya hannu kan kudirin kasafin kudin jihar na 2026 na Naira Biliyan 897, makonni uku bayan gabatar da shi a gaban majalisar dokokin jihar. Yayin rattaba hannu a Fadar Gwamnati da ke Katsina, a gaban ‘yan majalisar dokokin jihar, gwamnan ya jinjinawa majalisar bisa gaggawar amincewa...
Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta bukaci maniyyatan aikin hajjin 2026 da su gaggauta biyan kudin kujerun su kafin ranar 24 ga watan gobe. Darekta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taro da shugabannin sassa na hukumar da shugabannin shiyya da...
An naɗa Andrea Thompson, ’yar ƙasar Birtaniya, a matsayin mace mafi ƙarfi a duniya. Wannan na zuwa ne bayan tabbatar da cewa wanda aka bayyana a matsayin zakara — Jammy Booker — tun da farko namiji ne da aka sauya masa halitta zuwa mace, lamarin da ya sa aka soke nasararsa bisa saɓawa dokokin gasar....
Daga Bello Wakili Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkar tsaro a duk fadin kasar, sakamakon karuwar kalubalen tsaro da ake fuskanta. Shugaban ya ce za a dauki sabbin jami’an tsaro nan ba da jimawa ba, wadanda suka hada da na sojiin, ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro — domin karfafa...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya. Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan....
Rahotanni sun bayyana cewa kididdigar da ma’aikatar harkokin wajen yankin falasdinu ta fitar ya nuna cewa sojojin Isra’ila sun kashe akalla yan mata 33000 a ci gaba da yakin kare dangi da take yi kan alummar Gaza. Ma’aikatar fa fitar da wannan sanarwar ce a wajen taron ranar kawo karshen hare-hare kan mata ta duniya...
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya dawo Abuja daga birnin Luanda na Angola, inda ya halarci taron AU–EU karo na 7 a madadin Shugaba Bola Tinubu. Ya wakilci shugaban kasa a taron G20 na 2025 da aka yi a Johannesburg, Afirka Ta Kudu. A Angola, Shettima ya karanta sakon Shugaba Tinubu wanda ya sake...
A yammacin nan ne ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid za ta kece raini da Olympiacos a ci gaba da Gasar Zakarun Turai, duk da rashin wasu manyan ’yan wasanta biyu. Babban mai tsaron ragar Madrid, Thibaut Courtois, da ɗan wasan baya Dean Huijsen, na fama da jinya, lamarin da zai hana su buga wannan...
Jakadan kasar Aljeriya a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya yayi tir da abin da ya kira zalunci isra’ila da kuma ci gaba da kai hare-hare kan mutane kasashen labanon, Syria, da Gaza da kuma gabar yammacin kogin jodan , yayi kira ga majalisar dinkin duniya da ta dauki mataken gaggawa wajen dakatar da wadannan...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya. Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan....
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya. Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan....
Rahotanni sun bayyana cewa wasu masu dauke da makamai sun kama shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Sissoco Embalo a yau Laraba, kwanaki uku bayan da aka yi zaben shugaban kasa. Rahotannin sun ce an yi ta harbe harbe a babban birnin kasar, a yayin da Alummar kasar ke zaman jiran sakamako zagaye na farko na...
Babban sakataren tsaron kasar Iran Dr Ali Larijani a shafinsa na X ya soki siyasar Amurka a lokacin ziyararsa a kasar Pakistan kuma ya jaddada cewa Tehran tana son ayi gaskiya a duk tattaunawa da za’a yi. Kalaman na larijani yana nuna matsayar iran ne kan diplomasiyar iyakoki, yace yanci da mallaka wasu abubuwa ne...
Shugaba Bola Tinubu ya aike da sunan mutum uku zuwa Majalisar Dattawa, domin tantance su a matsayin sabbin jakadan Najeriya. Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne, ya sanar da haka a zaman majalisar na ranar Laraba. Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna Waɗanda...
Sojoji a Guinea-Bissau sun ce sun yi juyin mulki tare da karɓe ragamar mulkin ƙasar. Sun kuma sanar da dakatar da zaɓukan ƙasar tare da rufe iyakokinta nan take. ’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS Wannan na zuwa...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta bayyana sabbin nasarorin da ta samu wajen yaƙi da laifuka a jihar, ta hanyar holen mutum 34 da ta kama da aikata laifuka daban-daban. Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Rabi’u Muhammad, ya ce wannan ci gaba ya samu ne saboda sabbin dabarun aiki da kuma bayanan sirri da aka samu...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta bayyana sabbin nasarorin da ta samu wajen yaƙi da laifuka a jihar, ta hanyar holen mutum 34 da ta kama da aikata laifuka daban-daban. Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Rabi’u Muhammad, ya ce wannan ci gaba ya samu ne saboda sabbin dabarun aiki da kuma bayanan sirri da aka samu...
Daga Salihu Tsibiri Tsohon shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana tabarbarewar tsaro da ake fuskanta, wato ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma hare-haren ’yan bindiga, a matsayin barazana ga siyasar ƙasar nan gabanin zaɓen 2027. Ya yi wannan tsokacin ne a jawabinsa yayin bude zaman taron musamman na yini biyu...
Jami’an tsaro a Jihar Kaduna, sun fara gudanar da babban samame domin kawar da ’yan ta’adda da ’yan bindiga a wasu ƙananan hukumomin jihar. A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce an gudanar da aikin tare haɗin gwiwar sojoji, DSS, NSCDC, KADVS, da kuma...
