2025-06-03@11:55:01 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3675
«Kuka Bulukiya»:
Bayan an bari Amer, ya shiga jirgin, suka kama hanyarsu ta tafiya har suka sauka lafiya wanda hakan ya sa ma’aikatan jirgin suka ɗauki hoton da shi don tarihi, inda a ɗayan ɓangaren mutane da dama ke suffanta lamarin a matsayin hujjar ƙarfin niyya da ikon Allah. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
Babbbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yanke wa fitacciyar ’yar Tiktok, Murja Ibrahim wacce aka fi sani da Murja Kunya hukunicn daurin watanni shida a kurkuku. Alƙalin kotun Mai Shari’a Simon Amobida ya kuma ba wa Murja zabin biyan tarar Naira dubu 50. Ya ce saboda yawan mabiyanta a shafinta na Tiktok, an nada...
Kwanan baya, a yayin da ake gudanar da taron kolin ASEAN karo na 46, wasu jami’an diplomasiya na kasar Philippines sun yi shelar daddale wasu yarjejeniyoyi tare da kasar Sin don kiyaye zaman lafiya a tekun kudancin kasar Sin. Duk da haka Philippines ta rika daukar matakan takala a zahiri. Kuma abun da kasar ta...
A cikin wani mataki na ci gaba da sauya fasalin bangarorin noma da kiwo, Gwamnatin Jihar Jigawa na shirin kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da daya daga cikin manyan kamfanonin kiwon kaji na kasar Indiya, wato Srinivasa Farms. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Jigawa, Hamisu Mohammed...
Ma’aikatar kudi ta kasar Sin ta ce kamfanoni mallakin gwamnatin kasar, sun gudanar da ayyukansu yadda ya kamata cikin watanni hudu na farkon shekarar nan ta 2025, inda jimillar kudaden shigarsu ta ci gaba da karuwa bisa daidaito a shekara guda. Alkaluman da ma’aikatar ta fitar a Larabar nan, sun nuna tsakanin watan Janairu zuwa...
Gwamnatin Birtaniya ta sanar da dage takunkumin da ta kakaba wa wasu manyan jami’an gwamnatin Zimbabwe. Birtaniya ta ce ta yi hakan ne domin kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu. Ma’aikatar harkokin wajen Birtaniyar ta bayyana cewa za ta dage takunkumin da ke kan mutum hudu da kuma kamfanin kera makamai mallakar gwamnati a Zimbabwe. Wannan...

Masu Bincike Na Sin Sun Cimma Sabon Sakamako A Fannin Saurin Sadarwa Tsakanin Tauraron Dan Adam Da Doron Duniya
Wasu masu binciken fasaha na kasar Sin, sun cimma sabon sakamako a fannin saurin sadarwa tsakanin tauraron dan adam da doron duniya, inda suka karya matsayin saurin da ake da shi a baya, ta amfani da salon X-band mai tasha guda. Rahotanni na cewa masu binciken, daga cibiyar binciken harkokin sadarwar samaniya ko AIR, karkashin...
Ra’ayoyi daga sassan kasa da kasa sun karkata ga muhimmancin taron kolin ASEAN-Sin-GCC karo na farko da ya gudana a birnin Kuala Lumpur fadar mulkin kasar Malaysia a jiya Talata 27 ga watan nan. Daga mahanga ta shiyya, taron bangarorin uku ya mayar da hankali ga manyan sassa uku, wadanda suka hada da gabashin Asiya,...
Dakarun sojojin Najeriya sun dakile wani harin hadin gwiwa da ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP suka kai a yankin Marte da ke jihar Borno, inda suka kashe wasu da dama daga cikin maharan. Majiyar leken asirin hedikwatar sojan Najeriya ta tabbatar da cewa harin ya faru ne da misalin karfe 1:35 na wayewar safiyar...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump a tattaunawa ta wayar tarho da firai ministan HKI Benyamin Natanyahu ya bukace shi ya daina shiha a cikin tattaunawar da Amurka take da JMI. Kafin haka dai firai ministan ya sha barazanar kai hare-hare kan cibiyoyin nukliyar kasar Iran a dai-dai lokacinda ake tattaunawar. Wanda kuma yake tasiri a...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arachi ya tir da kalaman jakadan Burtaniya a Washington, Peter Mandelson, wanda yayi kira ga Amurka kada ta taba barin Iran ta tashe makamashin Uranium a cikin kasar. Ministan ya kara da cewa Mandelson yana son ya karkatar da tattaunawan da Iran take da Amurka. Ya kuma kara da ...
Majiyar kungiyoyin bada taimakon gaggawa a Gaza sun bayyana cewa ya zuwa lokacin bada wannan labarin a yau Laraba, sojojin yahudawan Sahyoniyya sun kashe akalla mutane 16. Shafin labarai na Arab News ta kasar Saudia ya nakalto Mahmud Bassal kakakin wata kungiyar bada agaji na Gaza yana cewa da misalign karfe biyun dare jiragen yakin...
A wani wasa da masana ke ganin zai matuƙar ƙayatarwa a gasar kofin Unity, yau Laraba za a buga wasa tsakanin manyan ƙasashen Afrika biyu Nijeriya da Ghana, ba kawai wasan ƙwallon ƙafa bane yau, kare mutunci, da ɗaukaka martabar ƙasa da kuma ramuwar gayya duk suka haɗe a wasan da za a buga a...
Idan har Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da bukatar Shugaban Kasa Bola Tinubu ta neman sake ciyo sabon bashi, jimillar bashin da ake bin Najeriya a yanzu zai koma Naira tiriliyan 162. A ranar Talata ce shugaban ya aike wa Majalisar Wakilai takardar neman ta sahale masa ya ciyo bashin, wacce shugaban majalisar, Abbas...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna a ranar Talata ta ci tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i da karin wasu mutum biyar tarar Naira miliyan 900. Kotun dai ta ci tarar tsohon Gwamnan kan laifin kamawa tare da tsare dattawan kabilar Adara da ke jihar a shekara ta 2019. Da take zartar da...
Gwamnatin kasar Ireland ta yi doka a jiya Talata wacce ta hana a shigar da duk wasu kaya da aka kera a matsugunan ‘yan share wuri zauna da a karkashin dokokin kasa da kasa ake daukarsu a matsayin haramtattu. Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Ireland ya fada wa kamfanin dillancin labaurn Faransa cewa;...
Sojojin HKI suna ci gaba da kai hare-hare a sassa daban-daban na yankin zirin Gaza da su ka hada da sansanonin ‘yan hijira da kuma rusa gidajen da su ka saura a tsaye. Tashar talabijin din ‘almayadin” ta bayyana cewa; An sami shahidai 7 da safiyar yau Laraba, bayan harin da ‘yan sahayoniyar su ka...

Arakci: Idan Birtaniya Ta Ci Gaba Da Batun Dakatar Da Tace Uranium A Iran, Za A Dakatar Da Tattaunawa Da Ita
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Akaci ya bayyana cewa; Idan har kasar Birtaniya tana ci gaba a kiran Iran ta dakatar da tace sanadarin uranium a cikin kasarta, to kuwa Iran din za ta yanke tattaunawar da take yi da ita. Ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran ya rubuta a shaifnsa na...
Rhotanni daga jihar ta Beneu sun ce a wani hari da makiyaya su ka kai a yankin Gwe ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 42. Mahukunta a yankin sun sanar da cewa; an gano gawawwakin mutane 32 da aka kashe sanadiyyar harin da aka kai kauyukan Ahume da Aodona, yayin da aka gano wasu gawawwakin mutane...
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ɗaga darajar Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Tarayya da ke Kabo a jihar Kano, zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Kabo. Wannan cibiyar ilimi, wacce aka kafa a shekarar 2022, yanzu ta zama jami’a ta uku ta gwamnatin tarayya a jihar, bayan Jami’ar Bayero Kano da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rashin iya siyan audugar Alada ga mata na kara jefa su cikin matsaloli da dama, a wasu lokuta ma har da cututtuka da ka iya jawo musu matsaloli. A cewar wani rahoto da Asusun yara na majalisar dinkin duniya UNICEF da WaterAid na shekarar 2021 suka fitar,...
Sun kara da cewa, kasashen Afirka za su kafe kai da fata wajen mutunta ka’idar Sin daya tak a duniya, da goyon bayan duk kokarin da kasar Sin ta yi na kare ikon ’yancinta da cimma burin sake hadewar kasar, da yin adawa da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, kana suka ce,...
Da yake magana da tashar talabijin ta ON Sports, Salah ya ce “Zan daina wasa ne kawai idan na fara jin gajiya a jikina”, “Idan ka tambaye ni ra’ayi na, ina tsammanin zan iya taka leda har zuwa shekaru 39 zuwa 40 amma idan na ji ina so in daina, zan daina, na samu abubuwa...
Shuganan Kasa Bola Tinubu ya aike wa Majalisar Wakilai takardar neman amincewarta domin ya ciyo bashin jimillar kudi Naira tiriliyan 39 daga kasasahen waje domin aiwatar da wasu ayyuka. A wasiku ukun da ya aike wa majalisar, wadanda shugabanta, Abbas Tajudeen, ya karanta a ranar Talata, Shugaba Tinubu ya nemi goyon bayan majalisa domin ciyo...
Ya ce, mahajjaciyar ta kamu da rashin lafiya ne jim kadan bayan kammala Tawafi – zagaye dakin Ka’aba, inda daga nan aka kai ta asibiti a ranar Lahadi, a ranar Litinin kuma Allah ya yi mata cikawa. “Kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, an yi jana’izar ta a Makkah a wannan rana, kuma an...

Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Nuna Misali Na Bude Kofa Da Raya Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da ASEAN Da GCC
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi kira ga aiwatar da matakai da za su zamo misali na bude kofa, da raya hadin gwiwa, da dunkule mabanbantan wayewar kai tsakanin Sin da ASEAN da GCC. Li Qiang, ya bayyana hakan ne a Talatar nan, cikin jawabinsa ga bikin kaddamar da dandalin Sin da ASEAN da...
An bukaci Maniyyatan Jihar Jigawa su yi addu’o’i ga jihar da kasa Najeriya domin samun zaman lafiya a yayin zaman su a kasa Mai tsarki. Amirul Hajj na Jihar, Mai Martaba Sarkin Kazaure Dr Najib Hussaini Adamu yayi wannan kiran a lokacin da yake jawabi ga Maniyyatan Jihar a Kasar Saudi Arabia. Amirul...

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Ce: Dole Ne A Dauki Kwararan Matakan Don Dakatar Da Laifukan Gaza
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Dole ne a dauki kwararan matakai don dakatar da laifukan da ake yi a Gaza A yayin ganawarsa da fira ministan Pakistan Shehbaz Sharif da tawagarsa a yammacin yau, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada wajabcin gudanar da ayyukan hadin gwiwa da...
Kafin tashinsa zuwa kasar Oman shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Suna neman kyakkyawar dangantaka da maƙwabtansu Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar kafin ya tashi daga filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Tehran zuwa birnin Muscat a yammacin yau Talata cewa: Makasudin ziyarar tasa zuwa kasar Oman ita ce kulla kyakkyawar...
Gujewar da Trump ta yi daga yakin Yemen ya harzuka mahukuntan gwamnatin Isra’ila da kasashen Larabawa da suka dogara da shi Shafin Jaridar Hill ta Amurka ta buga wani sabon labarin da ke bayyana irin kayen da Amurka ta sha a Yemen da kuma irin dimbin hasarar da Amurkan ta yi domin kare yahudawan sahayoniyya...
An kammala gasar fada tsakanin mutum-mutumin inji cikin jerin gasannin mutum-mutumin inji ta kasa da kasa a ran 25 ga watan nan da muke ciki a birnin Hangzhou dake gabashin kasar Sin. Gasar ta fada tsakanin mutum-mutumin inji da aka yi a wannan karo, ita ce irinta ta farko a duniya, inda kuma ta zama...
A cewar Mukaddashin Daraktan, ‘yan ta’addar sun yi yunkurin kutsawa inda sojojin suke, amma suka gamu da karfin soji. Ya kara da cewa, Rundunar Sojan Sama ta bayar da bayanan sirri tare da karfafawa sojin kasa, wanda ya kai ga halaka sauran ‘yan ta’addan da suka tsere. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
Ya zama wajibi duk wata kasa dake son samun ci gaba mai dorewa, ta rike asalinta, ta kare al’adunta, ta zabar wa kanta hanya mafi dacewa da ita kamar yadda kasar Sin ta yi, domin har kullum, Sin za ta ci gaba da zama abin koyi ga sauran sassan duniya. Daga kanmu, magana ta...
’Yan sanda sun kama babban wanda ake zargi da kisan wata matar aure masi shekaru 22 a gidanta da ke unguwar Tsamiyar Duhuwa da ke yankin Farawa a Jihar Kano. A ranar 6 ga watan Afrilu ne aka tsinci gawar matar mai suna Rumaisa Haruna, ne a gidanta bayan an yi mata kisan gilla. Rundunar...
Tabbas a halin yanzu, wasu kasashe ba su ba da’a muhimmanci ba, kana suna ta daukar matakan kashin kai yadda suka ga dama, lamarin da ya sa al’amuran kasa da kasa suka shiga rudani. Dangane da wannan batu, dole ne Sin da kasashen Afirka masu da’a su karfafa hadin kai, su yi adawa da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe Naira miliyan dari da hamsin da ɗaya da dubu dari takwas da sittin da uku (N151,863,895.97) domin sake gina wani masallaci da wani matashi ya cinna wa wuta a yayin da jama’a ke tsaka da sallar Asuba a cikin jam’i a Tiga Gadan da ke Karamar Hukumar Gezawa,...
Babbar Kotun Musulunci a Jihar Kano ta yanke wa Shafiu Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda cinna wuta a wani masallaci a kauyen Gadan, Karamar Hukumar Gezawa, yayin da jama’a ke tsaka da jam’in sallar asuba a ranar 15 ga Mayu, 2024. Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 23 tare da raunana wasu. An...
Shugaban hukumar kare hakkin bil’adama na MDD ta bukaci kasashen duniya su takurawa HKI ta kawo karshen kissan kiyashin da take yi a gaza bayan hare-haren da ta kai a kan wata makaranta a unguwar Fahmi Aljarjawi a cikin birnin Gaza wanda ya kashe falasdinawa akalla 36. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta...
Duk tare da yakin da suke fafatawa a Gaza, dimbin yahudawan sahyoniyya masu bauta sun kutsa cikin masallacin Al-aksa da ke birnin Qudus inda suka gudanar da bukukuwan addinu a jiya Litinin. Shafin yanar Gizo na labarai ‘Arab News’ ya bayyana cewa, bakin na addini, farin ciki ne da kwace gabacin birnin Qudus daga hannun...
Ga shi abin ci ya yi tsadar da samun a ci sau uku yana da wajala, balle kuma a nemi mai gina jiki. Kwananan masu sayar da ƙwai suka koka saboda rashin ciki, masu kifi dai haka abin yake balle kuma masu nama. Duk da hakan bai hana yara murmushi ba wataƙila saboda ba su...
’Yan sanda sun tsare wata matar aure kan zargin ta da kashe kishiyarta a Ƙaramar Hukumar Daura da ke Jihar Katsina. Mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Katsina, DSP Abubakar Aliyu, ya bayyana cewa matar ta yi wa uwargidarta kisan gilla ne bayan wata hatsaniya da aka samu a tsakaninsu, wanda ya ƙazance...
Kotu ta yanke wa wani magidanci mai shekara 56 hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan laifin yin fyaɗe ga agolarsa ’yar shekara 14. Babbar Kotun Jihar Ekiti ta yanke wa mutumin hukuncin ne byan an gurfanar da shi kan zargin aikata laifin a watan Oktoban shekarar 2024, watanni bakwai da suka gabata. A yayin zaman kotun da...
Mutanen garin Rano ake Jihar Kano sun kashe DPO na Babban Ofishin ’Yan Sandan garin tare da banka wa ofishin wuta Fitattun jama’ar gari sun kai wa Hedikwatar ’Yan Sanda da ke Rabin hari ne a sakamakon mutuwar matashin a hannun ’yan sandan. Wasu sanarwar da kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Kano, S.P. Abdullahi...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Najeriya tana cikin ƙasashen da suka fi yawan yara a duniya, a cewar Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF). Sai dai a cewar Hukumar ta UNICEF, kusan rabin wadannan yara suna fuskantar kalubale, kama daga cin zarafi zuwa rashin samun kulawa da dai sauran...
Shugaban kasar Iran wanda ya karbi bakuncin Fira ministan Pakistan da marecen jiya Litinin, ya bayyana cewa; Kasar Pakistan, makwabciyar jamhuriyar musulunci da muhimmanci, ta dubban shekaru. Shugaban kasar ta Iran Mas’ud Fizishkiyan wanda yake Magana a lokacin taron manena labaru na hadin gwiwa da Fira ministan na Pakistan, ya kuma ce; Da akwai haduwar...
Da safiyar yau Talata ne dai sojojin HKI su ka kai wa gabashin zirin Gaza da kuma Khan-Yunus hare-hare, bayan sa’oi daga kisan kiyashin da su ka yi wanda ya ci rayukan mutane 80. Saandiyyar sabon harin na safiyar yau, wani karamin yaro ya yi shahada, a yankin al-karama dake Arewacin Gaza. A daren jiya...
Rundunar ‘yan sandan Birnin Tarayya ta buƙaci al’ummar da ke kewayen hanyar Mararaba zuwa Nyanya su kwantar da hankalinsu bayan jin ƙarar wani abu da ya fashe a yammacin ranar Litinin. Lamarin ya faru ne a wata tashar bas da ke kusa da barikin sojoji na Mogadishu a kan hanyar Mararaba zuwa Nyanya. A wata...
Rundunar ‘yansanda ta fara gudanar da bincike kan fashewar wani abu a mashigar babban birnin tarayya Abuja a kan hanyar Mararaba zuwa Nyanya a ranar Litinin. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ya ce rundunar ‘yansandan ta samu rahoton kiran gaggawa a ranar 26 ga...