2025-09-18@02:44:21 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1520
«xYan Najeriya Mazauna kasashen waje»:

Isra’ila tace Ta Yi Kokarin Kashe Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Yakin Kwanaki 12 Da Kasar Iran
Ministan yakin HKI Israel Kazt ya bayyana cewa sun yi kokarin kashe jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae a yakin kwanaki 12 amma bayanan da suke da shi ya kasa kaiwa ga manufarsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan shi ne karon farko wanda HKI take tabbatar...
Kazalika, an amince da amincewar ne a taron majalisar zartarwa na jihar karo na 12, wanda Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, ya jagoranta a gidan gwamnati da ke Katsina. Da yake karin haske ga manema labarai bayan taron, kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin gida, Dakta Nasiru Mu’azu Danmusa ya ce, an sanar da matakin...
’Yan ta’adda sun kashe aƙalla mutum 63 a wani mummunan hari da suka kai a garin Darul Jamal, kusa da kan iyakar Najeriya da Kamaru, a yankin Bama na Jihar Borno. Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya tabbatar da cewa daga cikin waɗanda suka rasa rayuka akwai sojoji 5 tare da fararen hula 58. Tsagin...
Ƙungiyoyin Musulmi maza da mata da ƙananan yara daga sassa daban-daban na Jihar Oyo sun gudanar da bukukuwan zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW), na bana (shekara ta 1447 bayan hijira). Aminiya ta ruwaito cewa an fara gudanar da bukukuwan ne a ranar Asabar daga harabar babban Masallacin Unguwar Sabo, mazaunin...
A jiya Jumma’a 5 ga wannan wata, babban taron MDD karo na 79 ya jefa kuri’a tare da zartas da kudurin hadin gwiwar dake tsakanin MDD da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO da kasar Sin da dukkan kasashe membobin kungiyar SCO kimanin 40 suka gabatar tare. Kudurin ya amince da muhimmiyar rawar da...

Xi Ya Mika Sakon Taya Murna Ga Zaman Kwamitin Sada Zumunta Da Zaman Lafiya Da Ci Gaba Tsakanin Sin Da Rasha
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murna ga zaman taro na 15 na kwamitin sada zumunta da bunkasa zaman lafiya da ci gaba tsakanin Sin da Rasha, da aka gudanar yau Asabar a birnin Vladivostok na Rasha. Xi ya jaddada cewa, tun kafuwarsa a cikin shekaru 28 da suka gabata, kwamitin sada...
Rahotanni sun tabbatar da cewa ’yan bindiga sun kashe mutane bakwai, yayin wani hari da suka kai ƙauyen Magajin Wando da ke Ƙaramar Hukumar Ɗandume, a Jihar Katsina. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Juma’a, lokacin da maharan suka afka wa ƙauyen. Mauludi: Ƙungiyoyin addini sun nemi gwamnati ta sassauta...
Rahotanni sun tabbatar da cewa ’yan bindiga bakwai sun mutu a wani hari da suka kai ƙauyen Magajin Wando da ke Ƙaramar Hukumar Ɗandume, a Jihar Katsina. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Juma’a, lokacin da maharan suka afka wa ƙauyen. Mauludi: Ƙungiyoyin addini sun nemi gwamnati ta sassauta dokar...
Mambobin kwamitin zartarwar na ADC da suka hada da Bolaji Abdullahi (Sakataren yada labarai na kasa), Babachir Lawal (Mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin arewa maso gabas), Usani Uguru Usani (Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa), Farfesa Oserheimen Osunbor (Babban lauyan jam’iyyar na kasa), Bar Chinedu Idigbo (Sakataren shirye-shiryen jam’iyyar na kasa), Sen. Musa Elayo (Mataimakin shugaban...

Maulidi: Gwamnan Zamfara Ya Taya Al’ummar Musulmi Murna, Ya Buƙaci A Dage Da Addu’o’in Samun Zaman Lafiya
“Kowace ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal rana ce ta murnar zagayowar ranar haihuwar Manzonmu mai albarka (SAW). “Wannan lokaci ne mai kyau da ya kamata dukkan Musulmi su yi koyi da rayuwar Manzon Allah (SAW). “Musulunci ba addini kawai ba ne, hanya ce ta rayuwa, rayuwar Annabi (SAW), ta shiryar da...
Wanda aka kama sunansa iro Garba mai shekaru 25 daga Zangwaye Fulani a ƙaramar hukumar Ajingi a Jihar Kano. Ya amsa cewa shi da wasu mutane huɗu sun yi garkuwa da mutane a Kano, Jigawa da Bauchi. An kuma samu rigunan sojoji guda uku a hannunsa. Kwamishinan ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin kama...
Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce a yau Juma’a, shugaba Amurka Donal Trump zai rattaba hannu kan wata doka da za ta sauya sunan ma’aikatar tsaron kasar zuwa ma’aikatar yaki. Canjin suna na dindindin na buƙatar Izinin majalisa, to amma umarnin zartarwa da shugaban zai sa wa hannu, zai ba da damar amfani...
Yakin ya farkar da Sin da duniya baki daya, wanda ya zama tushen kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a shekarar 1949, daga bisani kuma ya dora kasar bisa tafarkin zamani. Ga duniya, mulkin mallaka ya fara wargajewa. Kasashe da dama sannu a hankali suka fahimci cewa, in sun jajirce, za su samu ‘yancin kai. Tasirin...
Karamar karamar hukumar Jibiya ita ce ta fara shirya taro domin yin sulhu da ‘yan bindigar, sai dai kuma ba a ga wakilin gwamnatin Jihar Katsina a wannan sulhu ba, amma dai an ga shugaban karamar hukumar da sauran jami’an tsaro da ake zargin daga Abuja suke halartar irin wannan taro. An yi wannan sulhu...

‘Yan Nijeriya Suna Shan Wahala A Lokacin Da Gwamnatin Tinubu Ta Fi Damuwa Da Aljihunta – Sule Lamido
“Tun lokacin Buhari har zuwa yanzu lokacin Tinubu, ‘yan Nijeriya na cikin wahala. Talauci tana nan a ko’ina, matasa ba su da aikin yi, kuma tattalin arziki yana lalacewa. Su na cewa suna yaki don Nijeriya, amma a zahirin gaskiya, suna yaki ne kawai don kansu da aljihunsu. “Na kasance cikin gwagwarmaya tun daga...
Da yake ganawa da ‘yan jarida a ranar Litinin, tsohon shugaban kungiyar masu tsara gidaje a Nijeriya, Aliyu Wammako, ya ce, rashin biyan ‘yan kwangila kudadensu na shafan tattalin arziki sosai. Ya bukaci gwamnatin tarayya da ka da ta tsaya bata wani lokaci ta kama biyan ‘yan kwangila kudadensu da hakan zGwamnatin tarayyar Nijeriya ta...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta gayyaci tsohon Gwamnan jihar, Nasir El-Rufa’i da sauran jagororin jam’iyyar ADC kan zargin yunkurin tayar da zaune tsaye. A cewar takardar wacce Aminiya ta gani, an gayyace su ne domin su yi wa rundunar bayani kan zargin su da hadin baki da tunzura jama’a wajen tayar da tarzoma da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yayin da ake gudanar da bukukuwan Mauludi a sassa daban-daban a garuruwan Najeriya, wasu yankunan na gudanar da nasu bukukuwar na daban. Ko yaya ake gudanar da bikin Sallar Gani? NAJERIYA A YAU: Hare-hare Kan Tarurrukan Siyasa Da Alakarsu da 2027 DAGA LARABA: Yadda Matan Da Ke Auren...
Sai dai soja ɗaya ya samu rauni kaɗan amma yana cikin koshin lafiya. Haka kuma sun lalata tayoyi guda huɗu na mota, sannan manyan motoci biyu sub kama da wuta a yayin arangamar. Laftanal Kanal Uba ya ƙara da cewa sojojin na ci gaba da gudanar da ayyuka a yankin domin hana ‘yan ta’adda damar...
Shugaba Bola Tinubu zai tashi daga Abuja yau Alhamis, 4 ga watan Satumba, domin fara hutu na aiki a Turai a matsayin wani ɓangare na hutunsa na shekarar 2025. Mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya ce hutun zai ɗauki kwanaki 10. Gargaɗi: Ƙauyuka 43 A Jihohi 14 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa Harin Sojojin...
Ya kuma nuna damuwa kan rikicin magoya bayan wasu ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta, yana mai cewa hakan na iya tayar da hankali a jihar. Game da tsaro kuwa, Gwamna Sule ya bayyana cewa gwamnati na ɗaukar matakai don shawo kan matsalolin da ke tasowa a wasu sassan jihar. Ya ce sun ƙarfafa haɗin...
Babban sakataren jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da Kim Jong Un, babban sakataren jam’iyyar ma’aikata ta kasar Koriya ta Arewa, kuma shugaban harkokin gudanarwa na kasar Koriya ta Arewa, a yau Alhamis a birnin Beijing. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
Shugaba Bola Tinubu zai tashi daga Abuja yau Alhamis, 4 ga watan Satumba, domin fara hutu na aiki a Turai a matsayin wani ɓangare na hutunsa na shekarar 2025. Mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya ce hutun zai ɗauki kwanaki 10. Gargaɗi: Ƙauyuka 43 A Jihohi 14 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa Harin Sojojin...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas ta yi gargadin cewa sabon salon da ’yan mata suka fito da shi na karbar kudin samarinsu da nufin za su je wajensu amma su ki zuwa laifi ne da za a iya hukunta su da shi. A cikin wani bidiyo da Kakakin rundunar a jihar, Grace Iringe-Koko, ta wallafa...
Siyasar Jihar Gombe ta ƙara ɗaukar zafi yayin da fitaccen ɗan siyasar nan, Umar Faruk FK, ya fice daga jam’iyyar PDP tare da dimbin magoya bayansa, tare da komawa APC. FK, ya bayyana cewa PDP ta gaza bayar da shugabanci nagari a jihar, shi ya sa ya yanke shawarar barin ta. 2027: ’Yan adawa na...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Karuwar hare-hare kan ’yan siyasa a kwanan nan ta sa wasu ’yan Najeriya sun fara fargabar abin da ka iya faruwa idan aka fara yakin neman zaben 2027. A kwanan nan ne dai wasu wadanda ake zargin ’yan bangar siyasa ne suka kai hare-hare a kan tarurruka ko...

Firaministan Senegal: Yadda Sinawa Ke Girmama Tarihi Da Kiyaye Labarun Abubuwan Da Suka Faru Da Su Na Da Matukar Burgewa
Firaministan kasar Senegal Ousmane Sonko ya bayyana a wata hira da ya yi da wakilin rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) a kwanan baya cewa, yadda jama’ar kasar Sin suke mutunta tarihi da kiyaye bayar da labarun abubuwan da suka faru da su ya yi matukar burge shi. Sonko ya ce, duk...
Kazalika, wannan biki na tunawa da nasarar fatattakar zalunci yana tunatar da mu mahimmancin waiwaye a kan tarihi. Fina-finai da aka yi game da hakan kamar “Dead to Rights”, da bikin nune-nunen a sassan yankin Macao, da faretin soja a birnin Beijing, hidindimu ne na sake duba tarihi, da sadaukarwar al’ummomin da suka gabata domin...
Domin ya ce wannnan matsala ce da ta shafi ƙasa, kuma ‘yan Nijeriya suna da ‘yancin sanin halin da ƙasar ke ciki. A cewarsa wannan babban zargi ne, don haka bai kamata a manta da shi ta hanyar yin jawabi ba tare da wasu gamsassun hujjoji ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
Wasu matasa da ake zargin ’yan daba ne sun tarwatsa wani taro da dattawan Katsina suka shirya a kan zaman lafiya a jihar jim kadan da fara shi ranar Talata. Hakan na zuwa ne ’yan kwanaki kadan bayan an kai irin makamantan irin wadannan hare-haren a kan tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i da tsohon...
Tun kafin zaɓen 2023 PDP ke fama da rikici, matsalar da ake ganin ta taimaka wajen hana jam’iyyar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
Alal hakika, akidar mulkin danniya akida ce wadda take tarnaki ga ci gaba da wayewa ta bil Adam, kuma yaduwar wannan akida barazana ce ga daukacin bil Adam. Don haka yaki da wannan akida ta bazu kamar wutar daji tsakanin sama da kasashe 80 daga nahiyoyin Asia, Turai, Afirka da Oceania. An kuwa tafka asarar...
Babban sakataren MDD António Guterres, wanda ya halarci taron kolin kungiyar hadin gwiwar Shanghai wato SCO da aka gudanar a birnin Tianjin dake kasar Sin, ya bayyana cewa, Sin ta taka rawar gani sosai wajen cimma nasarar yakin duniya na biyu. Kuma gudummawar da Sin ta bayar ita ce mabudin nasarar da kawancen kasashen duniya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta cafke wani ɗan bindiga da ake zargin ɗan ƙungiyar Lukurawa ne tare da shanu goma da ya sato, a wani samame da aka kai kasuwar shanu ta Bachaka. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Nafi’u Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar...

Shugaban Zimbabwe Ya Sauka Beijing Domin Halartar Bikin Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Mamayar Dakarun Japan
A yau Litinin shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya iso birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin domin halartar bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin mamayar dakarun Japan, da yakin kin tafarkin murdiyya na duniya. Shugaba Mnangagwa ya sha ziyartar kasar Sin, inda a shekarar da ta gabata ma ya zo birnin Beijing...
Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, wanda ya shigo kasar Sin don halartar taron koli na kungiyar hadin-kai ta Shanghai wato SCO na bana, ya zanta da dan jaridan babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a birnin Tianjin, inda ya ce, Xi Jinping shugaban kasa ne mai sanin ya...
A cewar sa, yankin Arewa-maso-yamma ya samu kaso mafi girma na ayyuka da ya kai naira tiriliyan 5.97, Kudu-maso-kudu ya samu naira tiriliyan 2.41, Arewa-ta-tsakiya naira tiriliyan 1.13, Kudu-maso-gabas naira biliyan 407, Arewa-maso-gabas naira biliyan 400, yayin da Kudu-maso-yamma (ban da Legas) ya samu naira biliyan 604. Idris ya ce dukkan waɗannan yankuna suna...
Ƙungiyar Arewa ta ’Yan Jarida (ABMPF) ta roƙi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da rushe Kasuwar Alaba Rago da Gwamnatin Jihar Legas ta fara, tana mai cewa matakin ya jawo asarar biliyoyin naira tare da barin dubban ’yan kasuwa cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi. Shugaban Ƙungiyar, Alhaji Abdullahi Yelwa, ya ce rusau ɗin ya haddasa wa...

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jaddada Muhimmancin Aiwatar Da Yarjejeniyar Da Iran Ta Cimma Da China
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada muhimmancin aiwatar da yarjejeniyar bisa manyan tsare-tsare tsakanin Iran da China A daidai lokacin da shugaban kasar Iran ya kai ziyarar aiki zuwa kasar China, asusun kula da shafukan sada zumunta na ofishin kula da tsare-tsare da wallafa ayyukan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei...
A cewar majiyar, kwale-kwalen zai iya daukar fasinjoji 16 ne kacal, amma a zagaye na Uku cunkoson matafiyar ya yi yawa inda wasu mata biyu suka tilasta wa kansu afkawa cikin jirgin inda suka zama fasinjoji zuwa 18, ana kyautata zaton cewa, wannan ne ya yi sanadin kifewar kwale-kwalen. Daga kanmu, magana ta...
Hadakar ta wuce batun tattalin arziki kadai, domin a bangaren tsaro ma, Rasha ta yi amfani da lalacewar alaka tsakanin kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar da kasashen yamma, inda ta samu kutsawa cikinsu. Ganin yadda yankin ke fama da matsalolin tsaro, sai Rasha ta aika musu da sojojin haya na Wagner domin...
Da ma can an yi ta ba da shawara cewa ya kamata Arsenal ta dauki danwasa mai buga gefen hagu kamar Gabriel Martinelli, amma ba ta ce komai ba har sai yanzu. Bayan da cinikin Eze ya fada, yanzu kuma kungiyar ta Arsenal ta sake mayar da hankalinta wajen sayan dan wasan baya daga kungiyar...
Matsala ta farko na yi mata take da: 1. Sai Bango Ya Tsage….: Gaskiyar diyan Bawo, da yake cewa, ‘Sai bango Ya tsage, kadangare ke samun wurin shiga. Lallai babu yadda za a yi gwamnati da sauran manyan al’umma suna kallon harshen Hausa a matsayin wani harshe wanda nazartarsa koma baya ne ga al’umma kuma...
Ɗan wasan ɗan shekaru 22 ya zura ƙwallaye 10 ne kawai a wasanni 52 da ya buga a United bara, kuma zuwan Sesko ya ka5ra rage masa damar zama a cikin ƙungiyar. Sha’awar Napoli kan Højlund ta ƙaru ne bayan Romelu Lukaku ya samu rauni a cinyarsa wanda zai sa ya daɗe a jinya. ...
‘Kun kuduri aniyar kiyaye manyan ka’idojin bin doka domin tabbatar da cewa kowa, har da masu mulki, suna karkashin doka kuma ana iya daukar mataki a kansu. Idan muka yi haka, to mun magance tushen matsalar mulki a wannan kasa,’ in ji shi. Sarkin Musulmi ya jaddada cewa adalci shi ne tubalin zaman lafiyar al’umma,...
Sai dai, Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta yi watsi da wannan shawara, tana mai cewa hakan zai jefa miliyoyin ma’aikata da iyalansu cikin duhu, wahala, talauci, da kiyayya ga gwamnati. Upah ya yi gargadi cewa wadannan tasirin ba za su tsaya a gidaje kawai ba, domin al’ummar masu kasuwanci ma za su sha da...
Tsohon Gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya ce ’yan Najeriya sun riga sun yanke shawara kan zaɓen shekarar 2027 da ke tafe. Yayin da yake jawabi a Abuja ranar Alhamis a taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar NNPP, Kwankwaso ya ce: “A yau, yawancin ’yan Najeriya na kokarin yadda za su samu abinci....
Bisa wani rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa, hakan ya nuna cewa, wannan shi ne karo na farko da Asusun Anita na Nijeriya ya samu karuwa tun daga watan Disambar shekarar 2021. Kazalika, rahoton ya sanar da cewa, a watan Agusta Asusun ya ci gaba da karuwa wanda daga watan aka samu kimanin...
Jami’an tsaro sun halaka aƙalla ’yan ta’adda 50 a yayin wata musayar wuta a yankin Ƙaramar Hukumar Mariga da ke Jihar Neja. Hadin gwiwar sojoji da sauran tsaro sun aika ’yan ta’addan lahira ne a yayin wani ƙazamar arangama a yankin Kumbashi da ke Ƙaramar Hukumar. Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Neja, muka wakilin Ƙaramar...