2025-09-18@02:45:36 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1520
«xYan Najeriya Mazauna kasashen waje»:

Iran Ta Yi Kakkausar Suka Kan Babban Darektan Hukumar IAEA Saboda Yadda Yake Mika Wuya Ga Bakar Siyasa
Babban darektan hukumar IAEA ya zama tamkar wata yar tsana ce a hannun kasashen Yamma don dakile shirin nukiliyar Iran An fara taron kwata-kwata na hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa a birnin Vienna, wanda ya samu halartar wakilan kasashe 35 mambobi hukumar Bisa la’akari da rahoton da babban daraktan ya fitar...
Gwamnatin Sudan ta zargi ‘yan tawayen kasar na dakarun kai daukin gaggawa da kai hari kan ayarin motocin agaji kai a yankin Darfur Gwamnatin Sudan ta sanar da cewa: “Dakarun kai daukin gaggawa sun kai hari kan ayarin motocin agajin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Darfur ta Arewa ta hanyar jiragen sama...
A wa’adinsa na farko a 2017, Trump ya kafa irin wannan haramci da ya shafi ƙasashe bakwai ns Musulmai, wanda ya jawo gagarumar suka daga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam. Masana harkokin tsaro da na diflomasiyya na ganin cewa wannan sabon mataki na iya ƙara tsamin dangantaka tsakanin Amurka da ƙasashen da...
A bara ne dai dam ɗin Alo ta cika da ruwa har wani ɓangare ya buɗe, lamarin da ya haddasa mummunar ambaliya a Maiduguri, inda aka rasa rayuka da dukiyoyi da dama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya zanta ta wayar tarho da firay ministan HKI Benyamin Natanyahu kan kasar Iran da kuma yakin Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa majiyar ofishin Natanyahu ta bayyana cewa tattaunawar tana zuwa ne a dai-dai lokacinda rikici da yaki yake ci gaba a gaza, da...
Wani kamfanin kera kayakin aikin likita mai zaman kansa a nan Tehran ya gabatar da wata na’ura mai aikin tiyata wanda kuma aka dora masa kayan aiki na zamani. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa an gabatara da wannan na’urar a kasuwar baje kolin kayakin aikin likita karo na 26TH wanda...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ’Yan Najeriya suna ci gaba da nuna damuwa da yadda rahotannin kwace-kwacen waya suke karuwa a sassan daban-daban na kasa. Daya daga cikin rahotanni na baya-bayan nan shi ne inda a birnin Kaduna aka bayar da rahoton cewa wani matashi ya daba wa wani babban soja wuka...
Mataimakin firaministan Sin He Lifeng, ya gana da babbar ministar kudin Birtaniya Rachel Reeves jiya Lahadi a birnin Landan, inda suka zurfafa musaya game da batutuwan da suka shafi tattalin arziki da hadin gwiwa a fannin hada-hadar kudade, da sauran batutuwan dake janyo hankulan kasashensu. He, wanda kuma shi ne ya jagoranci tawagar kasar Sin...
Majiyar sojan Rasha ta sanar da cewa; Tun daga watan Febrairu na 2024, zuwa yanzu ta tarwatsa tankokin yaki samfurin ” Abrams” kirar Amurka da ta bai wa kasar Ukiraniya har guda 26. Ya zuwa yanzu adadin wadannan tankokin da su ka rage a tare da sojojin Ukiraniya ba su wuce 5, ba domin adadinsu...

Ministan Harkokin Kiwon Lafiya Na Iran Ya Bukaci A Yawaita Sayar Da Kayakin Likita Zuwa Kasashen Waje
Minitan kiwon lafiya na kasar Iran ya bukaci kamfanonin da suke kera kayalin kiwon lafiya da kuma aikin likita so kara yawan kayakin da ake sayarwa zuwa kasashen waje. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Mohammad Reza Zafarkhan yana wannan kiran a jawabin da ya gabatar a taron bude kasuwar baje koli...
Minitan kiwon lafiya na kasar Iran ya bukaci kamfanonin da suke kera kayalin kiwon lafiya da kuma aikin likita so kara yawan kayakin da ake sayarwa zuwa kasashen waje. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Mohammad Reza Zafarkhan yana wannan kiran a jawabin da ya gabatar a taron bude kasuwar baje koli...
Wani rahoto na gungun kwararru da aka fitar a Lahadin nan, ya nuna yadda kasar Sin ke ta kokarin samar da kyakkyawan yanayin zaman lafiya, da kawance, da hadin gwiwa a yankunan tekun kudancin kasar. Rahoton na kwararrun cibiyar Xinhua, mai alaka da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin wato Xinhua, na da lakabin “Mayar...
A masana’antar Nollywood dake Kudancin Nijeriya, manyan masu kudinsu, sarakuna, hukumomi da gwamnatoci na iyakar kokarinsu wajen ganin masana’antar ta cigaba, ta hanyoyi daban daban da suka hada da kayan aiki, wajen daukar fim, fadada ilimi, tallace tallace da sauran tallafi da masana’antar ke bukata, a wasu lokutan ma akan daukesu har kasashen Turai wajen...
Jirgin ruwan na “Madeleine” shi ne na 36 a cikin jerin jiragen ruwan ‘yanci da suke son karya takunkumin da aka kakabawa yankin Gaza tun 2007. A cikin wannan jirgin ruwan da akwai ‘yan gwgawarmaya masu rajin kare hakkin bil’adama su 12 da su ka fito daga kasashe daban-daban, yana kuma dauke da kayan agaji...
Jami’in gabatar da kara, Anil Kumar, ya tabbatar da hukuncin kotun, kamar yadda jaridar The Times of India ta ruwaito a ranar Litinin. Rahoton ya bayyana cewa, “A ranar 30 ga Mayu, 2020, ta shigar da karar, tana mai cewa ta samu sako a ranar 12 ga Mayu, 2020, daga wata lambar kasa da kasa...
Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ta bayyana cewa; Matakin da Amurka ta dauka na kakaba takunkumin shiga Amurka akan wasu ‘yan kasa da kuma wasu kasashen musulmi yana nuni da yadda Amurkan take adawa da musulmi. Haka nan kuma ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta ce; Daukin matakin hana wasu mutane yin tafiya...
A wasu lokuta, matsalolin suna fitowa kai tsaye sakamakon rashin fahimta daga mataki na kasa, wadada a wasu lokutan ba su da wata alaka da sakatariyar jam’iyyun da ke mataki na sama. Ko a cikin jam’iyyar APC da ke mulki, akwai jayayya a cikin rassan jihohinta da ba su warware ba kuma suna barazanar ga...
Shugaban kasar Amurka ya ci gaba da fadin kalamai na zagi ga tsohon mai taimaka masa a harkokin gwamnati bayan sun babe. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Trump yana cewa hamshaken attajirin ya haukace. Labarin ya nakalto Fadar white house na karyata zancen cewa mutanen biyu zasu dinke barakan da ta...
Abu Ubaida kakakn dakarun Ezzuddeen Al-Qassam reshen soje na kungiyar Hamasa ya bayyana cewa dakarunsa zasu ci gaba da Yakar sojojin yahudawa har zuwa korarsu daga yankin zirin Gaza. Abu Ubaida ya kara nda cewa, dakarun Hamas suna a madaka ga sojojin HKI babu jada baya babu janyewa daga matsayinsu. Kafin haka dai a jiya...
A yau Jumma’a, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, a duk irin kalubalen da za a iya samu daga waje, masana’antun kasar Sin za su ci gaba da zama ababen nema a duniya, kuma kasuwannin kasar za su kasance a ko yaushe masu jan hankali wajen zuba jarin waje....
“Gidauniyarmu ta farko da aka kafa a shekarar 1952, ta tallafa wa masu fasaha daban-daban na Afirka, ta hanyar ba su damar shiga kasuwannin duniya. Gidauniyar Egbuagu, wadda aka kaddamar a yau; za ta mayar da hankali ne wajen kula da ayyukan shari’a, domin taimaka wa ‘yan Nijeriyan da ake tsare da su ba bisa...

Adadin ‘Yan Jaridar Falasdinu Da Suka Yi Shahada Sun Karu Zuwa 226 Tun Bayan Fara Kisan Kare Dangi A Gaza
Adadin ‘yan jarida wadanda suka yi shahada a Gaza ya karu zuwa 226 tun bayan fara kisan kare dangi kan yankin Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya tabbatar a yau Juma’a cewa: Adadin ‘yan jaridun da suka yi shahada ya karu zuwa 226, bayan sanar da shahadar dan jarida Ahmed Qaljah. Ofishin ya...
Wani rahoton tsaro da hukumar Kididdiga (NBS) ta fitar a watan Disamban 2024, ta ce, yawan kudin fansa da jama’an Nijeriya suka biya ya zarce naira tiriliyan 2.23 ga masu garkuwa da mutane daga Mayun 2023 zuwa Afrilun 2024. A cewar rahoton na CESPS, kusan kashi 65 cikin 100 na magidanta da suka fuskanci matsalar...
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Gwamnatin jihar Zamfara tana taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar wannan rana ta Babbar Sallar. “Babbar Sallah tana bai wa Musulmi damar girmama sadaukarwar da Annabi Ibrahim (AS) ya yi na ɗansa domin biyayya ga umarnin Allah. “Tana tunatar da mu muhimmancin imani, rashin son kai, da sadaukarwar da...
Kafafen watsa labarun kasar ta Zambia da kuma jam’iyyarsa ta “PFT” sun sanar da cewa; Tsohon shugaban kasar ya fadi ne a lokacin da yake motsa jiki a gidansa dake birnin Lusaka. Bayan da aka kai shi asibitin soja na “Maina Soko” likitoci sun tabbatar da cewa ya rasu. Gwamnatin kasar ta Zambia ta tabbatar...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yau mutane na kallon bukukuwan Sallah da ido daban—yayin da wasu ke ganin ta zama lokaci na shakatawa nishadi kawai, wasu kuwa na cewa an bar al’adun da ke nuna kimar wannan babban lokaci na Musuluncin. Wadanda suka manyanta na ganin akwai abubuwa da dama da a...
A cewarsa, jami’an tsaron sun samu kiran gaggawa da ke cewa, wasu gungun ‘yan fashi da makami sun rufe babbar hanyar, sun fara yin fashi ga matafiya a ranar 4 ga watan Yunin 2025. Nan take aka tura tawaga a ƙarƙashin jagorancin babban jami’in ɗansanda (DPO) da ke kula da caji ofis ɗin Toro,...
Shugaban kasar Iran Masuod Pezeshkiyan ya zanta ta wayar tarko tare da shugaban kasar Masar abdulfatta Assisi, inda suka taya juna murnar tahowar sallar Babba. Shugaban ya bayyana cewa kasar Iran tana da tsari ta makobta farko, don haka ne take, kara kyautata dangantaka da kasashe makobta da kuma musamman kasar ta Masar. Kamfanin dillancin...
Farfesa Jibril Amin Likita kuma tsohon malamin Jami’a, ya rasu a jiya Laraba yana dan shekara 85 a duniya. Jaridar Daily Trusta ta Najeriya ta nakalto majiyar iyalar mamacin na tabbatar da haka. Ta kuma bayyana cewa kwamishin gidaje a jihar Adama Hon Abdullahi Prambe ya tabbatar da labarin. Sannan ya kara da cewa an...
Lamarin ya ƙara tsananta ne bayan fitowar wani littafi mai taken Original Sin da ya zargi wani na kusa da Biden da ɓoye yadda jikinsa ya gaza yayin yaƙin neman zaɓen 2024, wanda daga ƙarshe ya janye. Wannan ya ƙara sanya tambayoyi kan ko an san da cutar sankarar da ya kamu da ita tun...
Abubakar ya tabbatar da cewa rundunar na da cikakken niyyar kare sararin samaniyar Nijeriya da rayuka da dukiyoyi a faɗin ƙasar nan. Ya kuma gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda irin goyon bayan da yake bai wa sojoji, musamman ta fannin kayan aiki da walwalar ma’aikata. A makon da ya gabata, rundunar ta kashe...
Aliyu, ya bayyana cewa Jibrin manomi ne daga ƙauyen Gargai da ke ƙaramar hukumar Bebeji a Kano. Ya kuma ce yana fama da cutar gyambon ciki da hawan jini. Likitoci sun bayyana cewa rasuwarsa ta faru ne sakamakon bugun zuciya da gazawar zuciya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Ma’aikatan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), sun yi barazanar shiga yajin aiki, wanda hakan zai iya jefa Abuja, Kogi, Nasarawa da Jihar Neja cikin duhu. Ma’aikatan, ƙarƙashin ƙungiyoyin NUEE da SSAEAC, sun ce kamfanin ya gaza cika alƙawuran da ya ɗauka bayan sun dakatar da wani yajin aiki a watan Nuwamban 2024. A...
Mazauna unguwar da asibitin kula da ido ta kasa yake wato Mahuta da ke jihar Kaduna sun amince da Gwamna Uba Sani ya zarce karo na biyu, biyo bayan warware takaddamar filaye da aka dade ana yi wanda ya yi sanadiyar rushe gidaje da dama a gwamnatin da ta gabata. Wannan na zuwa ne...
Wasu daga cikin mazauna yankin Mokwa da ambaliyar ruwa ta lalata wa gidaje a Jihar Neja, yanzu na zaune a sansanin ’yan gudun hijira. Ambaliyar, wadda ta kashe sama da mutum 100, ta jawo asarar dukiya da lalacewar gidaje da dama a yankin. Direbobi sun toshe babbar hanyar Kogi sakamakon harbe abokan aikinsu Ambaliyar Mokwa:...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wata al’ada da ta zama gama gari a tsakanin matasa, ita ce yankewa da fige kaji a unguwanni, musamman a lokutan bukukuwan Sallah. A da, ana da wurare na musamman da ake yin irin wannan abu. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa NAJERIYA A YAU:...
Jami’an Yansanda masu kula da ayyukan ta’addanci da kuma hana aukuwarsu a nan Iran sun sami nasarar kama wasu yan kungiyar ISIS 13 a duk fadin kasar daga ciki har da shugabansu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Brigadier General Saeed Montazer al-Mahdi kakakin rundunar FARAJA mai kula da fada da yan...
“Za mu warkar da raunukan rarrabuwar kawuna da yaki da kuma kafa makomar zaman lafiya da wadata,” in ji shi. “Komai runtsi, zaman lafiya ya fi yaki.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta jaddada haramcin gudanar da hawan Durbar na shagulgulan Babbar Sallah. Wannan sanarwar na cikin wata takarda da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Kano. Sanarwar ta bayyana cewa an sanya wannan doka ne bisa...
Kamar yadda majiyar ta bayyana, bayanan sirri da hukumar DSS ta samu sun nuna cewa, ‘yan ta’addan da suka fito daga dajin Bilbis da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara da wasu sassan jihar Kaduna, Gide ne ya gayyace su da su kai farmaki a kauyukan Kuchi. Majiyar ta ci gaba da cewa,...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Inganta sinadarin Uranium shi ne mabuɗin batun nukiliya, don haka Iran ba zata taba yin watsi da shi ba A jawabin da ya gabatar a safiyar yau Laraba, a daidai lokacin da ake cika shekaru 36 da wafatin jagoran juyin juya halin Musulunci Imam Khumaini (Allah ya...
Sanarwar tafiyar tasa ta biyo bayan ganawar da Inzaghi ya yi da jami’an Inter a ranar Talata, sanarwar da Inter Milan ta fitar ta ce Kulob din da Simone Inzaghi sun yanke shawarar rabuwa, “Wannan shi ne shawarar da aka dauka bisa yarjejeniyar juna”, shugaban Inter Giuseppe Marotta ya kara da cewa “Ina so in...

Guardian: Isra’ila Tana Kai Wa Makarantun Dake Dauke Da ‘Yan Gudun Hijira a gaza Hari, Tana Sane Da Hakan
Jaridar Guardian ta ta kasar Birtaniya ta bada labarin cewa, Hare-haren da sojojin HKI su ka kai kan wata makaranta, inda yan gudun hijira Falasdinawa suke samun mafaka da gangan suka yi shi, suna sane, kuma a halin yanzu suna Shirin kai wa wasu makarantun guda 4 hare-hare nan gaba. Jaridar ta kara da cewa:...
Daya daga cikin manyan-manyan jami’an gwamnatin tsohon shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya bayyana cewa: “Babu tantama gwamnatin HK Isra’ila ta tafka laifukan yaki a kan Falasdinawa a zirin Gaza da ta killace. Matthew Miller wanda ya yi aiki a matsayin kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka tun daga 2023 har zuwa karshen gwamnatin Joe Biden,...
Ofishin shugaban kasar Turkiya, ya bayyana fatan cewa tattaunawar da ake yi a tsakanin Rasha da Ukiraniya a birnin Istanbul, za ta kai ga tsayar da tsagaita budewa juna wuta wanda kuma zai ga, kawo karshen yakin baki daya. Ofishin shugaban kasar Turkiya ya bayyana haka a yau Talata, ta kuma kara da cewa,; Tattaunawar...
A cikin sanarwar da dukkan bangarorin da suka halarci taron suka sanya wa hannu, an amince da cewa, kungiyar za ta ba da wata guda domin tattauna bukatun JUSUN. Wani bangare na yarjejeniyar ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta saki kudaden da suka wajaba ga bangaren ma’aikatan shari’a a cikin wannan watan. Sanarwar ta...
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, yace nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu cikin shekaru biyu kadai shaida ce ta shugabanci mai hangen nesa da jaruntaka. Ya bayyana haka ne a yayin taron farko na National Dialogue on Citizen Engagement and National Security da aka gudanar a Abuja, mai...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Soki Rahoton Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Ta Duniya Kan Kasarsa
Ministan harkokin wajen Iran ya soki rahoton hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya yayin ganawa da Grossi a birnin Alkahira Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya soki sabon rahoton da hukumar ta IAEA ta fitar kan shirin makamashin nukiliyar kasar Iran yayin ganawarsa da babban darektan hukumar ta makamashin nukiliya ta duniya...
’Yan bindiga sun sako wani magidanci da suka yi garkuwa da shi da amaryarsa na tsawon wata bakwai, bayan sun bindige matar tasa tare da karɓar kuɗin fansa Naira miliyan 30 daga iyalansa. A watan Oktobar 2024 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutumin suna Yakubu Dada tare da amaryarsa, a yayin da ma’auratan...
Ya ƙara da cewa FRSC ta fara bincike kan dalilan da ke jawo hatsarin, kuma za ta gabatar da sakamakon binciken ga hedikwatarta da kuma Gwamnatin Jihar Kano domin ɗaukar matakan da suka dace don hana irin faruwar irin wannan iftila’i a gaba. Hukumar ta kuma sake jaddada ƙudirinta na wayar da kan al’umma kan...