Hizbullah: Iran Ba Ta Taba Tsoma Baki A Cikin Kudurorinmu Ba
Published: 7th, October 2025 GMT
A wata tattaunawa ta musamman da ya yi da tashar Al Mayadeen, daya daga cikin m manyan kusoshin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyed Abdullah Safieddine, ya yi magana kan lamurra da suka shafi harkokin gudanawa na cikin gida na kungiyar, da kuma shugabancinta a karkashin Sheikh Naim Qassem, da kuma dangantakarsu da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Safieddine ya jaddada cewa Iran ba ta taba tsoma baki a cikin harkokin aiki ko na soja na kungiyar Hizbullah ba, yana mai cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci bai taba tsoma baki cikin duk wani matakin soji ba, yana daukar Sayyed Hassan Nasrallah a matsayin mai yanke shawara ta karshe a kan dukkanin batutuwa na kungiyar.
Ya kara da cewa a lokacin yakin Yulin 2006, a lokacin da makiya suka kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Labanon, Jagoran ya kasance a birnin Mashhad, inda ya kira kwamitin tsaron kasa da manyan jami’an kasar ya shaida musu cewa an fara yakin, ya umarce su da cewa: ‘Ku je ku tambayi Sayyed Hassan da Hizbullah abin da suke bukata na dauki domin ci gaba da yin tsayin daka domin samun nasara.
Ya ce babu wani umarni da Iran take baiwa Hizbullah, illa dai kawai ta kan bayar da nata taimakon da Hizbullah take bukata ne kawai ba ta tare da tsoma baki kan kudurorin kungiyar ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sakamakon Jin Ra’ayin Isra’ilawa: Kashi 66% Na Goyon Bayan Kawo Karshen Yakin Gaza October 7, 2025 Vatican: Yakin Isra’ila a Gaza yaki ne a kan mutane raunana marasa kariya October 7, 2025 Sisi: Samun zaman lafiya na gaskiya a Gabas ta Tsakiya ya dogara da kafa ‘yantacciyar kasar Falasdinu October 7, 2025 Netanyahu Ya Dage Kan Samun Nasara A Yakin Gaza Amma Abinda Yake Kasa Akasin Haka October 6, 2025 Iran Ta Ti Watsi Da E3 Da Yadda Suke Tunkarar Shirin Nukliyar Kasar October 6, 2025 Aragchi Ya Bayyan Kokarin Ma’aikatarsa Na Bukatun Iran A Shirinta Na Makamashin Nukliya October 6, 2025 Lebanon: Shahidai Biyu Sanadiyyar Hare-Haren HKI A Lardin Nabatia A Kudancin Kasar October 6, 2025 HKI Ta Tabbatar Da Cewa An Kashe Sojojinta Fiye Da Dubu Daya A Yakin Gaza October 6, 2025 Kwamandan Dakarun IRGC Ya Ce: Suna Lura Da Duk Wani Motsin Abokan Gaba October 6, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Fitar Da Sanarwa Kan Batun Shirin Tsagaita Bude Wuta A Gaza October 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yabawa Pakistan Saboda Goyon Bayanta
Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr Ali Larijan wanda ya ke ziyarar aiki na kwanaki uku a kasar Pakistan ya yabawa kasar saboda goyon bayan da ta bawa kasarsa a lokacin yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka dorawa kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Dr Ali Larijana yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Talata. Sannan yace ya isar da sakon gaisuwa na Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khami’ae ga mutanen kasar Pakistan. Banda haka ya gana da Firai ministan kasar Shehbaz Sharif da shugaban kasa Asif Ali Zardari da kuma kakakin majalisar dokokin kasar kasar Sardar Avaz Saadik.
A ganawar Larijani da Sharif sun tattauna kan dangantaka mai tsawo da ke tsakanin Iran da Pakisatan, da kuma bukatar a kara zurfafata.
Sharif a nasa bangaren ya bayyana cewa nan ba da dadewa waministan harkokin wajen kasar Mohammad Ishak Dar zai ziyarci Tehran inda ake saran zai rattaba hannu kan yarjeniyoyi na bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu, daga ciki har da batun kammala aikin shimfida bututun gas daga kasar Iran zuwa Pakistan. Da kuma harkokin sadarwa.
A cikin wannan shekarar ne dai kasashen biyu suka rattaba hannu kan yarjeniyar bunkasa kasuwanci ta dalar Amurka billion 10 a tsakaninsu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Al-Houthi ya yi ta’aziyyar shahadar babban kwamanda na Hizbullah November 26, 2025 UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin Lebanon November 26, 2025 Matsalolin Tsaro A Yankunan Bakin Ruwa A Kasar Siriya Ya Kai Ga Zanga-Zangar Lumana November 26, 2025 Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu November 26, 2025 EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi November 25, 2025 Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Tashar Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru Mafaka Ta Wucin Gadi November 25, 2025 China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci