Aminiya:
2025-10-13@15:46:38 GMT

Makiyaya sun kashe manomi a gonarsa a Borno

Published: 7th, October 2025 GMT

Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kai farmaki a wata gonar wake, inda suka kashe wani mai gonar yana tsaka da aiki a Ƙaramar Hukumar Monguno da ke Jihar Borno.

Shaidu sun ce makiyaya kimanin 10 ne  suka kai harin bayan sun kutsa da shanunsu suka yi kiwo a wasu gonaki da misalin ƙarfe 12:20 na  ranar Asarar a Dajin Ngolom.

Ɗaya daga cikin manoman da makiyayan suka kutsa gonarsu, Abatcha Abatcha da ke yankin Gana Ali Ward, manoman sun buƙaci makiyayan su bar gonakin, amma sai lamarin ya rikice zuwa tashin hankali.

“Makiyaya sun kai mana hari da sanduna. Ɗaya daga cikin manoman da Allah Ya yi wa rasuwa, Bakulu Bafindi mai shekaru 30 daga unguwar Sabon Lamba a Maiduguri, ya samu munanan raunuka sakamakon arangamar, inda aka garzaya da shi Babban Asibitin Monguno, daga bisani wani jami’in lafiya ya tabbatar da rasuwarsa.”

’Yan bindiga sun kashe wani mutum sun sace hakimi a Kwara Zargin takardun bogi: Jami’ar Nsukka ba ta taɓa ba ni takardar digiri ba — Minista

Tuni dai aka ajiye gawarsa a ɗakin ajiyar gawarwaki na asibitin kafin daga bisani a miƙa ta ga ’yan uwansa domin yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Borno, Nahum Daso ya bayyana cewar, tuni jami’an tsaro da ’yan banga na yankin suka ƙaddamar da farautar maharan, yayin da ake ci gaba da zaman ɗar-ɗar a tsakanin manoman.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Makiyaya

এছাড়াও পড়ুন:

Jami’ar MDD: Taron Kolin Matan Duniya Ya Zo Daidai Lokacin Da Ya Dace

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Mutane A Fadin Duniya Sun Soki Ayyukan Neman ‘Yancin Kan Taiwan October 12, 2025 Daga Birnin Sin Sharhi: Lai Qingde Ba Zai Iya Jirkita Gaskiya Ba October 12, 2025 Daga Birnin Sin Wang Yi: Sin Na Maraba Da Dukkanin Matakai Na Dawo Da Zaman Lafiya A Gaza October 11, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 9, sun kwato kudin fansa a Borno
  • Jami’ar MDD: Taron Kolin Matan Duniya Ya Zo Daidai Lokacin Da Ya Dace
  • ’Yan ta’adda sun kashe sojoji 4 a wani sabon hari a Borno
  • Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 5 a Borno
  • Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 9, Sun Ƙwato Naira Miliyan 5 A Borno
  • Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi
  • ’Yan bindiga sun kashe sojoji 3 a Kebbi 
  • ’Yan bindiga sun kashe Civilian JTF 8 a Zamfara
  • Guguwar Ritaya Na Barazana Ga Ayyukan Hukumar Kwastam Yayin Da Jami’ai 825 Za Su Yi Ritaya
  • Sojoji sun mutu yayin da Boko Haram ta kai hari sansanin soji a Borno