Leadership News Hausa:
2025-10-13@15:46:31 GMT

Yanzu-Yanzu: Kwara United Ta Sallami Kocinta, Tunde Sanni

Published: 6th, October 2025 GMT

Yanzu-Yanzu: Kwara United Ta Sallami Kocinta, Tunde Sanni

Tags: KwaraNPFL ShareTweetSendShare Rabilu Sanusi Bena

Related Wasanni Kwallon Hockey: Nijeriya Na Fatan Samun Nasara A Masar 5 hours ago Wasanni Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or 2 days ago Wasanni Nijeriya Ta Samu Kwarin Gwiwar Zuwa Kofin Duniya 2 days ago.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Kwara

এছাড়াও পড়ুন:

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

Shugabannin masana’antu sun kuma yi kira ga gwamnati da ta daidaita tattalin arziki, inganta saukin gudanar da harkokin kasuwanci, da aiwatar da shirye-shiryen tallafi ga masana’antu na cikin gida.

 

Bugu da kari, masana sun nuna cewa rikicin kudin waje da rashin daidaito a kimar musayar kudi su ne manyan matsaloli ga kamfanoni masu zaman kansu daga kasashen waje, inda kalubalen samun damar mayar da ribar kamfani zuwa kasashen waje da samun kudin waje ke rage amincewar masu zuba jari sosai kuma yana karfafa su su bar kasar.

 

Binciken da LEADERSHIP Sunday ta gudanar ya nuna cewa yanayin tattalin arzikin Nijeriya ya sha wahala tun daga shekarar 2020, inda wasu kamfanoni suka rufe ayyukansu, ko suka yi kaura, ko kuma suka rage yawan ayyukansu a kasar.

 

Ana danganta wannan yanayi da wahalhalun tattalin arziki, canje-canjen kimar kudi, da tsadar gudanar da ayyuka, wanda hakan ya haifar da asarar ayyukan yi da kuma rashin daidaiton tattalin arziki mai yawa.

 

Wasu daga cikin manyan kamfanonin da suka bar Nijeriya sun hada da Standard Biscuits Nigeria Limited, NASCO Fiber Product Limited, Union Trading Company Nigeria Plc, da Deli Foods Nigeria Limited.

 

Ficewar wadannan kamfanonin daga kasuwar Nijeriya ya samo asali ne daga tasirin rashin daidaiton tattalin arziki da sauran kalubalen gudanarwa.

 

Yawancin kamfanonin sun bayyana cewa matsalolin tattalin arziki masu tsanani, canje-canjen kimar kudi marasa tabbas, da hauhawar farashin gudanar da ayyuka su ne manyan dalilan da suka sa suka yanke wannan shawara.

 

“Nijeriya dole ne ta samar da tsarin da zai ja hankalin wadanda za su zuba jari a masana’antu, hakar ma’adanai, wadanda za su sarrafa albarkatun kasa da kayan albarkatun da ake da su, tare da tabbatar da ci gaban tattalin arziki mai hadin kai,” in ji shi.

 

Haka kuma, shugaban Kungiyar Masu Kananan Harkokin Kasuwanci na Nijeriya (ASBON), Dakta Femi Egbesola, ya bayyana cewa ficewar kamfanoni masu zaman kansu na kasashen waje ya shafi yawancin Kananan da Matsakaitan Harkokin Kasuwanci (SMEs) da kamfanoni na cikin gida da ke aiki a kasar, tare da karawa da cewa gwamnati dole ne ta dauki matakan gaggawa don hana ficewar kamfanonin ketare.

 

A yayin da yake magana da daya daga cikin wakilanmu, Daraktan Gudanarwa na Cowry Asset Management Company, Johnson Chukwu, ya bayyana cewa haduwar rikicin kudin waje da rashin daidaito a kimar musayar kudi ya yi tasiri mara kyau ga ra’ayin masu zuba jari na kasashen waje wajen ci gaba da shiga harkokin zuba jari na kamfanoni masu zaman kansu a kasar.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Rahotonni Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki October 11, 2025 Manyan Labarai Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce October 4, 2025 Rahotonni Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya October 4, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano
  • Yanzu-Yanzu: ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki Na Tsawon Mako Biyu
  • Yaƙi Da Boko Haram: An Kashe Sojoji 2,700 A Shekara 12 – Janar Irabor
  • Daga Karshe Tawagar Super Eagles Ta Sauka A Uyo Bayan Saukar Gaggawa A Angola
  • Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
  • Sojoji Da ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Shida Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Taraba
  • Babban Kwamanda Ya Jagoranci Ceton Mutanen Da Aka Sace A Kwara
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci’ Yan Nijeriya Su Rika Sayen Kayan Da Aka Sarrafa A Gida