Kwamandan Dakarun IRGC Ya Ce: Suna Lura Da Duk Wani Motsin Abokan Gaba
Published: 6th, October 2025 GMT
Kwamandan Kare Juyin Juya Halin Musulunci ya jaddada cewa: Duk wani motsi na abokan gaba daga teku ko tsibirai zai gamu da martani mai tsanani
A yayin da yake duba shirye-shiryen yaki a tsibiran Tekun Pasha, babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC), Manjo Janar Mohammad Pakpour, ya jaddada cewa: Duk wani mataki da makiya za su dauka a teku ko a tsibiran, za su fuskanci kwakkwaran martani daga rundunar sojojin Ruwan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta IRGC.
Babban kwamandan rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta IRGC, Manjo Janar Mohammad Pakpour, ya duba shirye-shiryen da ake yi na yaki da rundunonin yaki a tsibirin Tekun Fasha.
Manjo Janar Pakpour ya jaddada cewa: “Sun shirya tsaf don tunkarar makiya a tsibirai, bakin teku, da kuma teku.”
Da yake tantance shirye-shiryen da ake yi a tsibiran Tekun Pasha, Babban Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta IRGC ya ce: “Rundunar Sojin Ruwa na IRGC na da kyakkyawar tarbiya da kyakkyawan shiri a teku, da tsibiran, da kuma bakin teku.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Fitar Da Sanarwa Kan Batun Shirin Tsagaita Bude Wuta A Gaza October 6, 2025 Kungiyar Jihadul-Islami Ta Falasdinu Ta Jaddada Aniyarta Ta Gwagwarmayar Neman ‘Yancin Falasdinawa October 6, 2025 Kungiyar Human Righs Watch Ta Yi Tsokaci Kan Shirin Trump Na Batun Tsagaita Bude Wuta A Gaza October 6, 2025 Hukumar Samar Da Abinci Ta MDD Ta Yi Gargadin Rage Tallafin Jin Kai A Kasar Somaliya October 6, 2025 Janar Pakpour: Duk wani shishigi a kan Iran zai fuskanci martani mai tsanani October 6, 2025 Iran na goyan bayan duk wani shiri da zai samar da ‘yancin Falasdinawa October 6, 2025 Babban mai shiga tsakanin na Hamas ya isa Masar domin tattaunawa da Isra’ila October 6, 2025 Rahoto: A cikin shekaru biyu Isra’ila ta jefa tan 200,000 na bama-bamai a Gaza October 6, 2025 Gidauniyar Mandela ta yi tir da Isra’ila kan dakile ayyukan jin kai zuwa Gaza October 6, 2025 Afirka Ta Kudu Ta Aike Da Tawagar Bincken Musabbabin Mutuwar Jakadanta A Birnin Paris October 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kare juyin juya halin Musulunci
এছাড়াও পড়ুন:
Abin da ya sa nake haxa harkar fim da harkar karatu-Nabila
Daga Musa kutama , kalaba
Hasana Aminu matashiyar jaruma ce a Masana’antar Kannywood, wacce ta fito a finafina da dama ciki har da fim xin A Duniya da wasu fitattun finafunan Hausa. A zantawarta da Aminiya, Hasana Aminu wadda aka fi sani da suna Nabila ta ce, a halin yanzu tana tauna taura biyu ne a baka
Ga yadda girar su ta kasan ce:
Sunan Jarumar?
Sunana Hasana Aminu, amma an fi sani na da suna Nabila a Masana’antar Kannywood da ke Kano
Ta yaya kike gwama karatu da kuma kasuwanci da harkar fim?
Eh, to farko ko da na shigo Masana’antar Kannywood sai na ga ai ashe ma ina da damar da zan iya yin karatu yayin da kuma nake sana’ata ta harkar fim. Domin kafin in fara fim na riga na samu kwalina na NCE. To sai na fahimci tunda dai ban da harkar fim kuma ina yin kasuwancin da zai iya taimaka min in xauki nauyin qaro karatu, ai gara in je in karo karatun. Wannan ne dalilin da ya sa na koma karatu, inda yanzu nake karatun Kimiyyar Aikin Xakin Gwaje-gwaje a matakin Babbar Difloma wato HND kuma sakamakon haka wasu ma daga cikin ‘yan masana’antar sun yi koyi da ni, sun koma makaranta su ma suna ci gaba da karatunsu.
Yi wa mai karatu bayanin yadda kika gwama karatun fim da kuma kasuwancu?
Gaskiya daga Asabar zuwa Lahadi ne nake zuwa karatun, daga Litininn zuwa Juma’a duk ina da lokaci da nake tafiya harkokin fim xin.
Don yanzu duk a inda aka kira ni a harkar fim ina da lokacin da zan je in dawo tsakanin Litinin zuwa Juma’a. Amma Asabar da Lahadi kowa ya san ranar makaranta ce duk wanda ke masana’antar ko ya aiko ya san lokacin makaranta ne.
Ko hakan bai sanya kin takura kanki ba?
Gaskiya ban tava jin na takura kaina ba, wani abin ma da ya fi haka duk zan iya haxawa da shi saboda ina da lokaci isasshe.
Ga wanda duk ya karanta wannan hira ta yaya zai iya gane cewa Hasana Aminu ce ta Kannywood da ake kallo a fim xin kannywood?
Eh, duk wanda ya san ni ko ya kalli finafinan da na yi kamar su Dare Xaya da Rigar Aro zai san ni ce
Ki fito a fim xin Xan Jarida kuma a matsayin ‘yar jarida kika fito, ko a iya cewa ke ma hala kina da shauqin zama ‘yar jarida ?
A gaskiya na fito dai a qanwar xan jaridar, inda na kasance abokiyar shawararsa a kan duk abin da yake yi ya riqa taqaitawa a irin aikinsa da kuma duk abin da yake yi ya lura da aikinsa.
Ko hakan ta sa ke ma kina sha’awar aikin jarida?
(Dariya) gaskiya ba na da sha’awar hakan.
Waje xaya ana samun wasu ‘yan matsaloli a Kannywood ta yadda ake samun ta da qura tsakaninsu da hukumomi, sai ga shi wasu kuma yanzu ne ma suke shirin shigowa masana’antar. Me za ki ce?
To gaskiya matsala kam akwai ta masu qoqarin shigowa kada su daka ta wasu waxanda suke ciki. Domin kowa da irin tarbiyarsa. Sannan kuma su yi binciken mutanen da suke son su shigo ta hannunsu
Batun manyan matoci na alfarma da riqe manyan wayoyi da mutane ke yawan ta da qura suna baza zarge-zarge ga ‘yan fim musamman mata. Me za ki ce?
Eh to idan duba wani lokaci za ka ga wani abu shi ke ta da wani. Domin in ka yi la’akari da hawa babbar mota, ai akwai maza akwai mata a Masana’antar Kannywood kuma matan ne kawai aka fi zargin gani suna hawa motocin. To su mazan me ya sa ba su hawan manyan motocin ko su ba su samun kuxi ne kamar mazan. Don haka wannan ba abu ne da zan so zurfafawa ba domin idan ka shigo harkar Kannywood za ka ga abubuwa da daman gaske. Kuma a rayuwa idan mutum bai da damar yin abu kuma ya sa wa kansa dole sai ya yi shi ko ta wane hali, to za a iya shiga wani hali da ba a zata ba.
Sabon salon xora finafinai a YouTube da haskawa a sinimar hakan ko a ganinki ya kawo wani ci gaba?
Eh, to wannan ka ga shi yanayin harkar ce abu ne wanda su masu shirya fim suke dubawa, ka ga mutum a da zai iya ya sayar da fim xinsa na series wato mai dogon zango, amma a yanzu yana da dama biyu ta xorawa a YouTube da sayarwa don samun riba.
Ana samun karvuwar finafinan Hausa a sauran qasashe maqwabtan Nijeriya. Me za ki ce a kan haka musamman a qasashen Nijar da Kamaru Ghana da Chadi ?
Gaskiya hakan na faruwa ne saboda yadda ake inganta ayyukan fim a Kannywood ta hanyar qwarewa da kuma samar da ingantattun kayan aiki. Wato lokaci ne kowa ya sa kuxinsa zai ga kuxinsa yadda ka zuba kuxi, ka yi fim hakan za ka ga ya yi gaba zuwa wasu wuraren da ma ba ka yi tsammani ba.