BBNaija S10: Ban san yadda zan kashe N150m da na lashe ba — Imisi Eniola
Published: 6th, October 2025 GMT
Gwarzuwar gasr Big Brother Naija (BBNaija) ta wannan shekara, Imisi Eniola Ayanwalwe, ta ce ba ta san yadda za ta kashe Naira miliyan 150 da ta lashe a gasar ba.
Imisi Eniola Ayanwale ce ta zama gwarzuwar BBNaija da aka kammala a daren Lahadi ne bayan kwanaki 70 ana fafatawa mai cike da ce-ce-ku-ce da nishaɗi.
An sanar da sakamakon tare da karrama ta da kyaututtuka ne a babban bikin ƙarshe da Ebuka Obi-Uchendu ya gabatar, inda Imisi ta doke abokiyar takararta Dede a karshe.
Ta tafi da tsabar kuɗi Naira miliyan 80 a matsayin wani ɓangare na kayatattun Naira miliyan 150 da ta lashe a matsayin gwarzuwar BBNaija karo na 10.
A bana, masu shirya gasar sun canja tsarin yadda ake fitar da zakara, inda suka ce za a zabi gwarzon ne daga cikin mutum 10 na ƙarshe da suka rage a gidan, maimakon mutum biyun ƙarshe kamar yadda aka saba. Amma daga bisani gasar ta dawo yadda aka saba, aka bar Imisi da Dede a zagayen ƙarshe kafin a sanar da sakamakon.
’Yan bindiga sun kashe wani mutum sun sace hakimi a Kwara Zargin takardun bogi: Jami’ar Nsukka ba ta taɓa ba ni takardar digiri ba — MinistaBayan sanar da ita a matsayin zakara, Imisi ta bayyana farin ciki da godiya, tana mai cewa har yanzu bata tsara yadda za ta yi da kuɗin ba.
Ta ce, “A gaskiya ban shirya yadda zan yi da kuɗin ba tukuna. Zan fara neman shawarar kuɗi tukunna, domin ban taɓa rike irin waɗannan maƙudan kuɗaɗe ba.”
A zamanta na ƙarshe da Big Brother kafin kammala gasar, Imisi ta bayyana cewa ta koyi darussa da dama yayin zamanta a gidan, ciki har da juriya da sanin kanta.
Imisi ta shahara saboda halayenta na raha, annashuwa da tsage gaskiya da kuma yadda take warware saɓani cikin natsuwa, abin da ya jawo mata masoya da dama a shafukan sada zumunta.
Kafin sanar da sakamakon, masu kallo sun zaƙu suna jiran wanda zai zama zakara a bana, wanda yanzu Imisi ta shiga jerin fitattun zakarun baya kamar su Phyna, Mercy Eke, Laycon, Whitemoney, da Ilebaye.
An rufe gasar ta BBNaija kaka ta S10 da shagulgula, inda Imisi ta bar dandali cikin farin ciki da kyaututtuka da kuma tarihi da ba za a manta da shi ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gwarzuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Wata mata ta kashe ’yar shekara 7 a Ribas
Ana fargabar cewa wata mata mai suna Success ta kashe wata yarinya mai shekaru bakwai, Alicia Olajumoke, a unguwar Rumueme da ke birnin Fatakwal na Jihar Ribas.
Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa matar da ake zargin tana da kusanci da dangin mahaifiyar yarinyar, wacce ita kaɗai ce a wurin iyayenta.
El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADC An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin NijeriyaBayanai sun ce ita ma matar ta caka wa kanta wuƙa a wuya bayan kashe yarinyar, kuma bayan an garzaya da duk su biyun asibiti, likitoci suka tabbatar da cewa sun riga mu gidan gaskiya.
Lamarin wanda ya faru a ranar Talata ya ɗimauta mazauna yankin, la’akari da zargin cewa matar ta kashe yarinyar ce a gidanta bayan ta je har makarantarsu ta ɗauko ta ba tare da izinin mahaifiyarta ba.
Jami’ar hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, inda ta ce an kai gawar yarinyar ɗakin ajiye gawa domin bai wa likitoci damar kammala bincikensu na kimiyya gabanin soma nasu binciken.
“Mun ziyarci wurin da abin ya faru, mun ɗauki hotuna, kuma an garzaya da su asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsu.”